Gaskiya Ta Fito: Trump Ya Fadi Wasu Dalilai 2 da Suka Sa Ya Kai Hare Hare Iran

Gaskiya Ta Fito: Trump Ya Fadi Wasu Dalilai 2 da Suka Sa Ya Kai Hare Hare Iran

  • Shugaban kasa Donald Trump ya yi dogon bayani game da hare-haren da Amurka ci gaba da kai kasar Iran, a Gabas ta Tsakiya
  • Yayin da yakin ya shiga rana ta uku, Amurka ta rasa sojoji hudu, kuma Trump ya lashi takobin murkushe gwamnatin Iran baki daya
  • Da yake bayyana dalilai biyu na fara kai hari Tehran, ya ce ya dauki matakin ne lokacin da ya fahimci barazanar Iran ta kai makura

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana manyan dalilan da suka sanya ya ba da umarnin kai hare-hare a kasar Isra'ila da kashe Ayotallah Khamenei.

A karshen makon nan ne, Isra'ila da Amurka suka kai jerin hare-hare a Iran, lamarin da ya yi ajalin manyan sojojin kasar, ciki har da jagoran addini, Khamenei.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da musayar wuta, Iran ta samu gagarumin goyon baya a yaki da Amurka da Isra'ila

Trump ya ce ya kai hare-hare Iran ne don hana su kera makaman nukiliya da masu linzami.
Makami mai linzami da Iran ta yi gwajinsa (hagu) da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a filin jirgin Florida. Hoto: Mohsen Shandiz/Corbis, Mandel NGAN / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Dalilin Trump na kai hare-hare Iran

A ranar Litinin, Trump ya ce ya ba da umarnin kai hari kan kasar Iran ne domin dakile shirye-shiryenta na kera makaman nukiliya da makaman linzami masu dogon zango, in ji rahoton Reuters.

Trump ya lashi takobin cewa Amurka za ta ci gaba da wannan yaki muddin bukatar hakan ta taso. A wani taro da aka gudanar a Fadar White House, shugaban ya kuma ce Iran ta zama babbar barazana, shi ya sa ya yanke shawarar kai harin.

Zuwa yanzu, hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar Ayatollah Khamenei, da kuma nutsar da jiragen yakin Iran da dama, tare da farmakar wurare sama da 1,000.

Trump ya bayyana cewa wannan ita ce "dama mafi kyau ta karshe da Amurka take da ita domin kawar da barazanar da wannan gwamnati ke yi wa duniya".

Ko da yake ya dade yana fafutukar janye sojojin Amurka daga kasashen waje, Trump ya ce wannan hari na na Iran yana tafiya cikin nasara fiye da yadda aka tsara, cewar rahoton Iran International.

Kara karanta wannan

Trump ya fadi adadin shugabannin Iran da aka kashe, ya bayyana mamakin da kasar ta ba shi

'Manufofin yakin Amurka da Iran' - Trump

Trump ya bayyana cewa an kiyasta yakin zai dauki tsawon makonni hudu zuwa biyar, amma Amurka tana da karfin da za ta ci gaba da fafatawa na tsawon lokacin da ya wuce hakan.

Ya ce babban dalilin fadan shi ne hana Iran kera makaman nukiliya, (duk da cewa Tehran ta sha musanta hakan), da kuma ruguza shirinta na makamai masu linzami da ke cin dogon zango.

Trump ya yi ikirarin cewa Iran na shirin kera makaman da za su iya sauka cikin Amurka, kodayake rahotannin sirri na Amurka sun nuna cewa wannan ikirarin na shugaban ya wuce gona da iri.

Jaridar The Straits Times ta rahoto Trump ya kuma bayyana cewa dakarun Amurka sun nutsar da jiragen ruwan Iran guda 10, inda ya ce "suna can kasan teku a halin yanzu".

Ya kara da cewa burin yakin ya hada da murkushe dakarun ruwan Iran da kuma hana kasar cigaba da bai wa kungiyoyin mayaka dake yankin goyon baya.

Kara karanta wannan

Bayan kashe 'dan kasarta, China ta maida martani kan yakin Iran da Amurka, Isra'ila

Trump ya lashi takobin ci gaba da kai hare-hare Iran har sai ya cimma manufarsa.
Hayaki ya turnuke saman Tehran bayan an rahoto tashin wani abin fashewa a safiyar 28 ga Fabrairu, 2026. Hoto: Mahsa / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Tunawa da sojojin Amurka da suka mutu

A karshen jawabin nasa, Trump ya yi ishara da asarar rayukan sojojin Amurka hudu da aka yi ya zuwa yanzu a wannan fafatawa da ta shiga rana ta uku.

Ya lashi takobin cewa:

"Domin tunawa da su, za mu ci gaba da wannan yaki tare da kwarin gwiwa da jajircewa domin murkushe barazanar da wannan gwamnati take yi wa al'ummar Amurka".

Wannan jawabi na Trump shi ne mafi fadi da ya taba yi tun bayan fara yakin a ranar Asabar, inda ya nuna cewa Amurka ba za ta sassauta ba har sai ta cimma burinta.

Matsalar da Trump yake fuskanta a Amurka

A wani labari, mun ruwaito cewa, bincike ya nuna cewa kashi 27 kacal na Amurkawa ne suka goyi bayan harin da Donald Trump ya kai wa kasar Iran.

Akalla sojojin Amurka uku ne aka kashe yayin da wasu biyar suka jikkata, lamarin da ya sa farin jin Trump ya ragu da kashi 39, kamar yadda binciken ya nuna.

Binciken ya kuma nuna cewa Amurkawa da dama sun bayyana aniyarsu ta janye wa daga goyon bayan Trump idan har wasu abubuwa biyu suka faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com