Iran ce Ta Kakkabo Su? Amurka Ta Yi Magana kan Jiragen Yakinta 3 da Suka Fado a Kuwait

Iran ce Ta Kakkabo Su? Amurka Ta Yi Magana kan Jiragen Yakinta 3 da Suka Fado a Kuwait

  • Kasar Amurka ta tabbatar da fadowar jiragen yakinta guda uku a Kuwait, inda ta danganta lamarin da kuakuren abokan aiki
  • Rahotanni sun nuna cewa jiragen Amurka uku sun rikito kasa a daidai lokacin da yaki ke kara zafi tsakaninta da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Rundunar sojin Amurka ta bayyana cewa duka matukan jiragen su shida sun tsira da rayuwarsu, ta kuma godewa kasar Kuwait

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United States - Kasar Amurka ta tabbatar da cewa jiragenta guda uku sun gamu da tangarda, an kakkabo su bisa kuskure a Kuwait.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Kuwait ta tabbatar da aukuwar lamarin, a daidai lokacin da Iran ke ci gaba da kai farmaki duk wani sansanin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.

Jirgin sojin Amurka.
Jirgin yaki marasa matuki mallakin rundunar sojin Amurka Hoto: @CENTICOM
Source: Twitter

Rundunar sojin Amurka, United States Central Command (CENTCOM), ta tabbatar da hatsarin jiragen guda uku a wani sako da ta wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Yakin Iran da Amurka ya rutsa da tsohon kyaftin din Najeriya, an ji halin da yake ciki

Yadda aka harbo jiragen Amurka 3

Ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon abin da ta kira “hari daga abokan aiki bisa kuskure."

“Da karfe 11:03 na dare agogon ET, ranar 1 ga Maris, jiragen yaki na Amurka kirar F-15E Strike Eagle guda uku da ke tallafawa Operation Epic Fury suka rikito kasa a Kuwait.
"Jiragen sun yi hatsari ne sakamakon abin da ake zargin hari ne daga bangaren abokan aiki bisa kuskure,” in ji sanarwar.

Matukan jiragen Amurka sun tsira

Sai dai ta tabbatar da cewa matukan jiragen suna cikin koshin lafiya, kamar yadda Premium Times ta tattaro a rahoton da ta wallafa.

A sanarwar da ta fitar a shafinta, rundunar CENTCOM ta kara bayani cewa an harbi jiragen bisa kuskure ne yayin artabu, wanda ya hada da hare-hare daga jiragen Iran. makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki.

Ta tabbatar da cewa jami'anta da wasu abokan aiki ne suka harbo jiragen yakin na Amurka bisa kuskure daga sararin samaniyar Kuwait.

Kara karanta wannan

Yakin Iran da Amurka: Bama bamai sun tarwatse a Dubai da wasu kasashe 2

Rundunar sojin Amurka ta ce dukkan ma’aikatan jirgin guda shida sun yi nasarar ficewa ta hanyar kujerar gaggawa, an kubutar da su cikin nasara kuma suna cikin yanayi mai kyau.

Dakarun sojin Amurka.
Dakarun rundunar sojojin Amurka a bakin aiki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kuwait ta tabbatar da aukuwar lamarin

Kuwait ta amince da faruwar lamarin, inda Amurka ta nuna godiyarta ga kokarin rundunar tsaron Kuwait da goyon bayansu a wannan aiki.

An ce ana ci gaba da bincike kan musabbabin lamarin, kuma za a fitar da karin bayani idan an samu sababbin bayanai.

Iran ta sake kai hari Dubai da kasashe 2

A wani labarin, kun ji cewa an ji karar fashe-fashe a biranen Dubai da wasu kasashe biyu a Gabas ta Tsakiya yayin da aka shiga ta na uku ta hare-haren Iran da Amurka.

Daga cikin wuraren da aka ji tashin fashe-fashe da jiniyar gargaɗi akwai kasar Kuwait da safiyar Litinin din nan, inda ganau suka shaida cewa an ga hayaki yana tashi kusa da ofishin jakadancin Amurka.

Hukumar tsaron farin kaya ta Kuwait ta bayyana cewa dakarun kariyarsu sun kakkabo mafi yawancin jirage mara matuƙa na Iran a kusa da unguwannin Rumaithiya da Salwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262