Rana ta 3: Hezbollah Ta Shigar wa Iran Fada, An Kashe Mutane 31 a Harin Sama

Rana ta 3: Hezbollah Ta Shigar wa Iran Fada, An Kashe Mutane 31 a Harin Sama

  • Akalla mutane 31 ne aka rahoto sun mutu a birnin Beirut bayan harin ramuwar gayya da kungiyar Hezbollah ta kai wa kasar Isra'ila
  • Hezbollah ta nuna cewa ta kai hari Isra'ila ne domin ɗaukar fansar kisan jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei da kuma kare Lebanon
  • Sai dai, bayan harin Isra'ila a Beirut, Ministan tsaro ya yi barazanar cewa suna da burin kashe shugaban Hezbollah Naim Qassem

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Lebanon - Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai farmaki a Beirut, babban birnin ƙasar Lebanon, inda suka kashe akalla mutane 31.

Wannan ya biyo bayan harin makami mai linzami da jirage mara matuƙi da ƙungiyar Hezbollah ta ƙaddamar kan wani sansanin soji a birnin Haifa da ke Arewacin Isra'ila.

Isra'ila ta kashe mutane 31 a harin da ta kai Beirut
Hayaki na tashi a Beirut bayan harin da Isra'ila ta kai garin a ranar 2 ga Maris, 2026. Hoto: IBRAHIM AMRO / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Harin Hezbollah ya harzuka Isra'ila

Hezbollah ta bayyana cewa ta kai harin ne domin ɗaukar fansar kisan jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei da kuma kare al'ummar Lebanon daga hare-haren Isra'ila, in ji rahoton Aljazeera.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Iran ta kai hari ofishin Netanyahu, Firaministan Isra'ila

Hukumar dillancin labaran Lebanon ta tabbatar da cewa mutane 31 ne suka riga mu gidan gaskiya, yayin da wasu 149 suka jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai yau.

Hezbollah ta jaddada cewa tana da haƙƙin kare kanta daga zaluncin da aka kwashe watanni 15 ana yi mata.

Sai dai, Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya gargaɗi babban sakataren ƙungiyar, Naim Qassem, cewa yanzu ya zama mutumin da ake nema domin a kashe shi.

Katz ya ƙara da cewa duk wanda ya bi tafarkin Khamenei zai tsinci kansa a jahannama, kamar yadda rahoton BBC ya nuna.

Isra'ila ta fadada yaƙin zuwa Kudancin Lebanon

Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana cewa za ta ci gaba da kai "munanan hare-hare" kan sansanonin Hezbollah a fadin Lebanon.

Bayan Beirut, an ruwaito hare-hare a ƙauyuka da dama na kudancin Lebanon da kuma kwarin Bekaa da ke gabashin ƙasar.

Isra'ila ta bayyana cewa ta kai harin ne da nufin kakkabe wasu manyan mambobin Hezbollah a Beirut da kuma wani babban jigo a kudancin ƙasar, kodayake ba ta bayyana sunayensu ba.

Kara karanta wannan

Yan Shi'a sun yi zanga zanga a Kano da jihohin Arewa kan kashe Khamenei a Iran

Isra'ila ta ce ta kai hare-hare Lebanon da nufin kakkabe dakarun Hezbollah.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu tsaye a wani waje da makamin Iran ya sauka a 19 ga Yunin 2025. Hoto: MARC ISRAEL SELLEM/POOL/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Isra'ila ta gargadi mazauna Lebanon

Domin kauce wa asarar rayukan fararen hula, Isra'ila ta umarci mazauna ƙauyuka sama da 50 a kudancin Lebanon, ciki har da garin Bint Jbeil, da su bar gidajensu cikin gaggawa.

Ko da yake Hezbollah ta yi laushi bayan yaƙin 2024, amma har yanzu tana ƙoƙarin nuna cewa tana da ikon kawo cikas ga tsaron Isra'ila, da kuma taimakawa Iran.

Iran ta farmaki ofishin Netanyahu

A wani labari, mun ruwaito cewa, dakarun IRGC sun yi iƙirarin ƙaddamar da hari kan Isra'ila ta hanyar amfani da makami mai linzami samfurin Kheibar.

A cewar IRGC, makaman Kheibar da ta harba sun sauka kan ofishin Firayiminista Benjamin Netanyahu da kuma hedkwatar rundunar sojin saman Isra'ila.

Wannan hari, wanda dakarun Musulunci na Iran suka kira "rukuni na 10" na hare-hare, ya afku ne a matsayin martani ga kashe Ayatollah Ali Khamenei.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com