Makaman Iran Sun Dura Babbar Matatar Mai a Saudiyya, Gobara Ta Tashi

Makaman Iran Sun Dura Babbar Matatar Mai a Saudiyya, Gobara Ta Tashi

  • Rahoto ya nuna cewa ma’aikatar tsaron kasar Saudiyya ta ce sojoji sun harbo jirage marasa matuƙa da suka nufi matatar mai a ranar Litinin
  • Ta bayyana cewa ta yi nasarar harbo jiragen daga sama, amma duk da haka an ce karafun jiragen sun haddasa gobara a matatar man
  • Matatar Ras Tanura da ke kusa da Dammam na iya tace fiye da gangar mai rabi miliyan a rana daya, tana cikin mafi girma a Gabas ta Tsakiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - An kai hari kan matatar mai ta Ras Tanura mallakar kamfanin Saudi Aramco a Saudiyya a ranar Litinin, bayan karafuna da suka faɗo sakamakon harbo wani jirgin maras matuƙi na Iran.

Harin ya faru ne yayin da rikicin da ke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ke ci gaba duk da kisan jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Kara karanta wannan

Yakin Iran da Amurka: Bama bamai sun tarwatse a Dubai da wasu kasashe 2

Matatar man kasar Saudiyya
Matatar man Ras Tanura da ke Saudiyya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Times of India ya nuna cewa kakakin sojin Saudiyya ne ya sanar da hakan yayin da Iran ke cigaba da harba makamai.

Gobara ta tashi a matatar Saudiyya

Jaridar Indian Express ta ruwaito labarin, tana ambaton wani dan jarida na cewa gobarar da ta tashi karama ce, kuma an shawo kanta.

Bidiyoyin da aka wallafa daga wurin sun nuna hayaƙi mai kauri kuma baki yana tashi bayan harin, lamarin da ya jawo lamarin ya dauki hankali sosai.

An rufe matatar man Saudiyya

Kamfanin Saudi Aramco ya rufe matatar Ras Tanura da ke kusa da Dammam na ɗan lokaci bayan jirage marasa matuƙa na Iran sun nufi wurin.

Talabijin na gwamnatin Saudiyya ya ce an dauki matakin ne a matsayin kariya, yana mai cewa babu wanda ya mutu sakamakon gobarar.

Matatar man Saudiyya a 2022
Matatar Saudi da ta kama da wuta a yaki da Yemen a 2022. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wasu rahotanni sun bayyana cewa matatar na daga cikin manyan matatu a Gabas ta Tsakiya saboda tana iya tace fiye da gangar mai rabin miliyan a rana.

Kara karanta wannan

Yaki da Iran: Jiragen yakin Amurka sun ruguzo daga sama a Kuwait

Bayani kan harin Iran a Saudi

Wani masani kan harkokin tsaro ya ce kai hari kan matatar na nuna ƙarin tsanantar rikici a Gabas ta Tsakiya, domin an nufi muhimmin ginshiƙin tattalin arzikin Saudiyya.

Masani Torbjorn Soltvedt daga kamfanin bincike na Verisk Maplecroft ya yi magana da AP a wata hira, inda ya ce:

“Harin kan matatar Ras Tanura ta Saudiyya babban lamari ne, domin yanzu kayayyakin makamashi na yankin Tekun Fasha sun shiga cikin yanayi maras tabbas.”

Ya ƙara da cewa:

“Wani lokaci na rashin tabbas na iya biyo baya yayin da Iran ke ƙoƙarin haifar da babbar illa ta tattalin arziki ta hanyar nufar tankokin mai, kayayyakin makamashi na yankin, hanyoyin kasuwanci da abokan huldar Amurka.”

Ga yadda MS Ingawa ya wallafa bidiyon matatar a shafin X:

Jiragen Amurka sun fado kasa

A wani labarin, kun ji cewa hukumomi a kasar Kuwait sun sanar da fadowar wasu jiragen yakin Amurka da safiyar Litinin, 2 ga Maris 2026.

Kara karanta wannan

Yadda Saudiyya ta kakkabo wasu makamai da Iran ta harba a yaki da Amurka

Rahotanni sun nuna cewa jiragen sun kama da wuta bayan fadowa kasa, an hango wani matuki ya sha da kyar kuma yana asibiti ana duba lafiyarsa.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da gwabza yaki tsakanin Amurka tare da hadin gwiwar Isra'ila da kuma kasar Iran a Gabas ta Tsakiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng