Hatsabiban Makamai da Iran Ta Mallaka yayin da Take Yaki da Amurka da Isra'ila
Iran - Bayan kisan gillar da Amurka da Isra'ila suka yi wa Ayatollah Ali Khamenei, kasar Iran ta nuna cewa wannan karon yaƙi ne na rayuwa ko mutuwa, kuma ba makawa, sai ta dauki fansar kisan jagoranta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
To sai dai, babbar tambayar da ke gaban masana tsaro ita ce: Ta yaya Iran za ta yi amfani da rumbun makamanta domin gasa wa Amurka da ƙawayenta aya a hannu?

Source: Getty Images
Taswirar makamai masu linzami na Iran
Iran tana da rumbun makamai masu linzami mafi girma a shiyyar Gabas ta Tsakiya, kamar yadda rahoton Aljazeera ya nuna.
Ganin cewa tsofaffin jiragen yaƙinta na samfurin F-4 da F-14 ba za su iya karawa da jiragen yakin zamani na Amurka ba, Iran ta mayar da hankali kan makamai masu linzami a matsayin kashin bayan kariyarta.
Mafi tsayin zangon makamanta na iya kaiwa kilomita 2,000 zuwa 2,500, wanda ke nufin za su iya dukan Isra'ila da dukkan sansanonin Amurka a yankin Gulf, amma ba za su iya kaiwa cikin Amurka ba.
Ga nau'ukan makamai masu linzami da Iran ta mallaka, tare da nisan zangon da suke kai wa:
1. Makamai masu gajeren zango: Kilomita 150-800

Source: Getty Images
Ana amfani da waɗannan makaman, kamar su Fateh-110, Zolfaghar, da kuma tsofaffin Shahab-1/2, domin kai hare-hare cikin sauri kan sansanonin soji na maƙwabta.
Amfaninsu shi ne ana iya harba su da yawa a lokaci guda, wanda ke rage wa abokan gaba lokacin shiryawa da kuma gajiyar da na'urorin kariya.
Wannan ita ce dabarar da Iran ta yi amfani da ita a harin Ain al-Assad a shekarar 2020 bayan Amurka ta kashe Qassem Soleimani, wani babban jami'in sojanta, in ji rahoton BCC.
Wannan harin ya tabbatar da cewa Iran na iya janyo asara mai girma ga Amurka ba tare da ta tashi jirgin yaƙi ko ɗaya ba.
2. Makamai masu matsakaicin zango: Kilomita 1,500-2,000

Source: Getty Images
Waɗannan su ne makaman da ke sauya lissafin yaƙin, kamar su Shahab-3, Emad, Ghadr-1, da kuma sababbin samfuri kamar Kheibar Shekan.
Samfurin Sejjil ya shahara saboda yana amfani da daskararren man fetur, wanda ke ba shi damar kasancewa a shirye don harba shi cikin ƴan mintuna kaɗan.
Waɗannan makamai sun sanya ƙasashen Qatar, Bahrain, Kuwait, Saudi Arabia, da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) cikin haɗari kai-tsaye.
Duk wani sansanin Amurka da ke cikin waɗannan ƙasashe yana ƙarƙashin barazanar waɗannan makamai, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto amfani da irin makaman a wannan yaki.
Jirage mara matuƙi da makaman "Cruise"

Source: Getty Images
Ba ya ga makamai masu linzami, Iran tana amfani da makaman Cruise kamar Soumar, Ya-Ali, da Paveh waɗanda ke da basirar guje wa na'ururar gano makamai ta kasashe.
Samfurin Soumar na da karfin tafiyar nisan kilomita 2,500, wanda ke nufin yana da nisa sosai, kuma zai iya kaucewa na'urorin kariya.
A bangaren jiragen mara matuƙi kuma, ko da yake ba su da sauri, amma ana amfani da su cikin ayarin makamai domin gajiyar da tsarin kariya na abokan gaba.
Masana na ganin wannan dabarar za ta zama babban jigon yaƙin idan ya daɗe, domin tana sa filayen jirgi da tashoshin makamashi kasancewa cikin fargaba na sa'o'i da dama.
Biranen makamai na karƙashin kasa
Wani babban ƙarfin Iran shi ne "biranen makama masu linzami" da aka gina a cikin manyan ramuka a ƙarƙashin duwatsu, kamar yadda rahoton Yahoo.com ya nuna.
Wannan na nufin koda an kai wa Iran hari na farko mai tsanani, za ta iya ci gaba da harba makamai na tsawon makonni.
Ga sojojin Amurka, wannan yana nufin dole ne su shirya wa yaƙi mai tsayi maimakon nasara mai sauƙi. Watakila wannan ne dalilin da ya sa Shugaba Donald Trump ya ce yakin zai iya daukarsu makonni hudu, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.
Hormuz: Takura wa tattalin arzikin duniya

Source: Getty Images
Dabarar Iran ba ta tsaya a kan amfani da makamai masu linzami kawai ba. Mashigar Hormuz, wadda ɗaya bisa biyar na man fetur da iskar gas na duniya ke bi ta cikinta, ita ce babbar makamin Iran.
Iran na iya barazana ga jiragen kasuwanci ta hanyar amfani da jiragen yaki na ruwa, nakiyoyin teku, da kananan jiragen yaƙi masu sauri don kakkabe duk wani jirgin ruwan abokan gaba.
Ko da ba a rufe mashigar Hormuz gaba ɗaya ba, barazanar harba makamai na sa farashin inshorar jirage da na danyen mai tashi.
Tuni dai kamfanin sufuri na Maersk ya dakatar da zirga-zirga ta mashigar cewar rahoton RFI, yayin da dakarun IRGC suka ce sun riga sun harbi manyan jiragen dakon mai guda uku na Amurka da Birtaniya.
Wannan ya sa farashin danyen mai na Brent ya tashi da 10% zuwa $80, kuma masana na hasashen zai iya kaiwa $100 nan ba da jimawa ba.
Dabarun Iran na yanzu sun fi na baya
A ƙarshe, wannan sabon yaki ya nuna cewa dabarun Iran na wannan karon sun fi na baya tsanani, musamman ma ganin yadda za su yi yakin don fanshe kisan jagoransu.
Wani dan Najeriya mazaunin Kuwait, Sadiq Madabo, ya shaida wa Legit Hausa cewa, su da suke a Gabas ta Tsakiya, sun gaskata karin karfin Iran.
Sadiq Madabo ya ce wannan yakin ya zo da sabon salo, domin kuwa shirin da Iran ta yi wannan karon ya fi wanda ta yi a shekarar baya, don haka ba kanwar lasa ba ce.
"A yanzu na ga hakikanin karfin Iran, domin kan ka ce me, sun kai hare-hare a kasashe bakwai na Larabawa. Amma ina rokon Allah ya takaita, don idan ya wuce haka, to wasu kasashe za su iya shiga."
- Sadiq Madabo.
Iran ta dauki matakai bayan kisan Khamenei
Kun dai ji cewa, bayan tabbatar da mutuwar Ayatollah Ali Khamenei, sakamakon hare-haren Amurka da Isra'ila, Iran ta dauki wasu tsauraran matakai.
Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran sun sanar da dokar yin zaman makoki na kwanaki 40 da kuma hutun kwanaki bakwai, inda aka rufe dukkan ofisoshin gwamnati.
Dangane da tanadin kundin tsarin mulkin Iran, an kafa wata majalisar shugabanci domin jan ragamar ƙasar a wannan lokaci da ake shirin sauya shugaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




