Yaki da Iran: Jiragen Yakin Amurka Sun Ruguzo daga Sama a Kuwait
- Hukumomi sun tabbatar da rikitowar da dama daga cikin jiragen yakin kasar Amurka a Kuwait yayin da ake cigaba da yaki da Iran
- Gwamnatin Kuwait ta bayyana cewa an mika wasu daga cikin matukan asibiti domin lura da lafiyarsu bayan fadowar jirgin yakin
- A daya bangaren, an bukaci 'yan kasar Amurka da su yi taka-tsan-tsan wajen fita zuwa wurare a Bahrain yayin da Iran ke luguden wuta
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kuwait - Ana cigaba da kai hare-hare yayin da Amurka/Isra'ila da Iran ke cigaba da gwabza yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Yayin da Iran ke cigaba da kai hare-hare, Kasar Kuwait ta sanar da cewa wasu jiragen yakin Amurka sun fado kasa suna daga sararin samaniya.

Source: Getty Images
Rahoton AP ya nuna cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da aka shiga rana ta uku a yakin da ya jawo mutuwar mutane sama da 100.
Jiragen Amurka sun fado a Kuwait
Ma’aikatar tsaron Kuwait ta ce wasu jiragen yakin Amurka sun faɗi a ƙasar a ranar Litinin, inda matukan jiragen suka sha da kyar.
Ma’aikatar ba ta bayyana abin da ya haddasa faɗuwar jiragen ba, sai dai lamarin ya faru ne a lokacin da Iran ke ci gaba da kai hare-hare masu tsanani kan ƙasar.
Biyo bayan lamarin, gwamnatin Kuwait ta sanar da cewa an kai matukan jiragen asibiti domin duba lafiyarsu da ba su kulawa.
Kakakin ma’aikatar tsaron Kuwait ya ce:
“Wasu jiragen yakin Amurka sun faɗi da safiyar yau. Muna tabbatar da cewa dukkan ma’aikatan jiragen sun tsira.”
Ya ƙara da cewa ana binciken musabbabin lamarin yayin da hukumomi suka kaddamar da aikin ceto nan take a wajen da abin ya faru.
Duk da rikitowar jirgin, har zuwa yanzu, rundunar sojin Amurka ta Central Command ba ta yi martani kai tsaye ba kan lamarin.
An gargadi 'yan Amurka a Bahrain
Ofishin jakadancin Amurka a Bahrain ya ce hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami daga Iran sun ci gaba a ranar Litinin, 2 ga Maris, 2026.
A wani saƙo da ya wallafa a dandalin X, ofishin jakadancin ya bukaci ‘yan Amurka da ke ƙasar da su guji otal-otal da ke babban birnin Manama, yana mai cewa:
“Za a iya kaiwa wuraren hari.”

Source: Getty Images
Bahrain na ɗaya daga cikin ƙasashen Tekun Fasha da Iran ta kai wa hari bayan farmakin da Amurka da Isra’ila suka kai, wanda ya haddasa rikicin Gabas ta Tsakiya.
Trump ya ce zai fafata da Iran
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa za su iya shafe mako hudu suna gwabza yaki da Iran.
Ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da shi, inda ya ce zuwa yanzu abubuwa suna tafiya daidai duk da kashe sojojin Amurka a Kuwait.
Trump ya ce sun bude kofar tattaunawa da Iran domin kawo zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, duk da ya ce ba lallai hakan ya yiwu ba.
Asali: Legit.ng

