Trump Ya Fadi Kwanakin da zai Shafe Yana Gwabza Yaki da Iran

Trump Ya Fadi Kwanakin da zai Shafe Yana Gwabza Yaki da Iran

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa Iran kasa ce mai karfi, yana ganin za su shafe makonni suna gwabzawa da ita
  • Trump ya bayyana haka ne yayin da ya tabbatar da mutuwar sojojin Amurka a wani hari da Iran ta kai, inda ya ce ba makawa za su dauki fansa
  • Bugu da kari, Trump ya ce duk da abubuwan da ke faruwa, ya bude kofar cigaba da tattaunawa da Iran, amma bai da tabbas ko hakan zai yiwu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Rahotanni sun nuna cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yakin da ake yi da Iran a halin yanzu na iya ɗaukar mako huɗu.

A yanzu haka dai an shiga rana ta uku, inda Iran ke kai hare-hare sansanonin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya bayan harin da Isra'ila ta kai mata da taimakon Trump.

Kara karanta wannan

Yawan sojojin Amurka da suka mutu bayan harin Iran, wasu da dama sun jikkata

Shugaba Donald Trump na magana
Shugaban Amurka na yawabi a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira ta wayar tarho da jaridar Daily Mail ta Birtaniya, inda ya ce tun da farko ya san cewa rikicin zai ɗauki lokaci.

Za a shafe mako 4 ana yaki da Iran

Shugaba Donald Trump ya jaddada cewa yaki da Iran na iya ci gaba na tsawon mako huɗu masu zuwa saboda wasu dalilai

Ya ce:

“Tunda farko an ɗauke shi a matsayin shirin mako huɗu. Mun yi tunanin zai ɗauki mako huɗu ko makamancin haka. Ƙasa ce babba, zai ɗauki mako huɗu — ko ƙasa da haka,”

Trump ya ce bai yi mamakin yadda abubuwa suka gudana ba zuwa yanzu:

“A’a, ina ganin komai yana tafiya kamar yadda aka tsara,”
Wajen da aka kai hari Iran
Wani waje da Isra'ila da Amurka suka kai hari Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Maganar sojojin Amurka da aka kashe

Wasu rahotanni sun nuna cewa Shugaban Amurka ya tabbatar da mutuwar wasu sojojin kasar sa uku a wani farmaki da Iran ta kai musu.

Kara karanta wannan

Macron ya fadi shirin da Faransa ke yi bayan Amurka da Isra'ila sun kai wa Iran hari

Ya amince cewa su ne 'yan Amurka na farko da suka mutu a yakin, inda ya ce hare-haren baya kamar kama shugaba Nicolás Maduro na Venezuela a Janairun 2026 sun gudana ba tare da mutuwar wani ɗan Amurka ba.

Reuters ta rahoto Trump ya ce:

“Amurka za ta ɗauki fansa saboda mutuwarsu, kuma za ta yi mummunan martani ga ‘yan ta’addan da suka fara wannan yaki,”

Akwai yiwuwar tattaunawar Amurka da Iran?

Shugaban ya kuma bayyana cewa har yanzu ya buɗe ƙofa ga tattaunawa da Iran, amma bai tabbatar da ko hakan zai faru nan ba da jimawa ba.

Trump ya yi wannan jawabi ne daga gidansa na hutu na Mar-a-Lago, inda yake tun bayan bayar da umarnin kai hare-hare kan Iran.

Birtaniya ta tallafawa Amurka kan Iran

A wani labarin, kun ji cewa Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ba Amurka damar amfani da sansanin sojojinsu a yakin da ta ke da Iran.

Keir Starmer ya bayyana cewa sun dauki matakin ne domin tabbatar da kare mutanen Birtaniya da ke zaune a Gabas ta Tsakiya.

Duk da haka, Firaministan ya bayyana cewa ba a hada kai da wasu wajen kai hari Iran ba a farmakin da ya jawo kashen wasu shugabannin Tehran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng