Yadda Saudiyya Ta Kakkabo Wasu Makamai da Iran Ta Harba a Yaki da Amurka

Yadda Saudiyya Ta Kakkabo Wasu Makamai da Iran Ta Harba a Yaki da Amurka

  • Saudiyya ta sanar da cewa ta tare makaman roka na Iran da aka harba domin kai hari filin jirgin Riyadh da sansanin Prince Sultan
  • Majiyar tsaro ta ce kariyar sama ta yi nasarar kakkabe makaman ba tare da lalata dukiya ko jikkata mutane ba
  • Rahotanni sun ce an kai hari kan filayen jiragen Dubai, Abu Dhabi, Kuwait da Manama, inda aka tabbatar da mutuwar mutum guda

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Riyadh, Saudiyya - Saudiyya ta bayyana cewa ta dakile makaman roka na Iran da aka nufa da su.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kai harin ne kan filin jiragen saman Riyadh da sansanin sojoji na Prince Sultan.

Saudiyya ta kakkabo makamin roka da Iran ta harba
Yariman Saudiyya, Mohammed Bin Salman. Hoto: @KSAmofaEN
Source: Twitter

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Aljazeera cewa kariyar sama ta samu nasarar kakkabe makaman a ranar Lahadi 1 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Yawan sojojin Amurka da suka mutu bayan harin Iran, wasu da dama sun jikkata

Yadda rigima ta barke tsakanin Iran, Isra'ila

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rigima tsakanin Iran da Isra'ila wanda ya jawo fargaba a yankin Gabas ta Tsakiya da sauran kasashe.

Hakan ya faru bayan Isra'ila ta samu goyon bayan Amurka suka kai wani mummunan hari Iran da safiyar jiya Asabar 28 ga watan Fabrairun 2026.

Daga bisani, Iran ta yi martani inda ta harba makaman roki ofisoshin Amurka da ke wasu ƙasashe a Gabas ta Tsakiya.

Hare-haren sun shafi wasu birane a ƙasashen Larabawa ciki har da Hadaddiyar Daular Larabawa da Abu Dhabi da Riyadh da Kuwait.

Harin da ya kashe Ayatullah Ali Khamenei

Har ila yau, hukumomi a kasar Iran sun tabbatar da mutuwar jagoran Addini a kasar, Ayatullah Ali Khamenei bayan harin Isra'ila.

Lamarin ya tayar da hankulan al'ummar Iran da sauran Musulmi inda dubban Iraniyawa suka cika birnin Tehran domin nuna jimami kan rashin da aka yi.

Kara karanta wannan

Da gaske harin Iran ya hallaka Benjamin Netanyahu? an samu gaskiyar lamarin

An kakkabo makamin rokan Iran a Saudiyya

Majiyar ta ce wannan nasara ba ta haifar da tangarda ga zirga-zirgar jiragen sama ba, kuma babu asarar rayuka ko dukiya da aka samu.

Saudiyya ta kakkabo makamin rokan Iran
Marigayi Ayatullah Ali Khamenei. Hoto: @khamenei_ir.
Source: Twitter

Shaidan gani da ido kusa da filin jirgin ya bayyana cewa ya ga kuma ya ji yadda makamin ya tarwatse a sararin sama.

An kuma rawaito cewa an kai irin wadannan hare-hare kan filayen jiragen Dubai, Abu Dhabi, Kuwait da Manama, cewar Times of Israel.

Mahukunta sun tabbatar da cewa an samu mutuwar mutum guda a Abu Dhabi sakamakon abin da suka kira “lamari” a harin.

Saudi Arabiya na dauke da sansanonin sojojin Amurka da jami’anta, duk da cewa manyan cibiyoyi suna Bahrain da Qatar.

Yariman Saudiyya ya yi waya da Trump

A wani labarin, an ji cewa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya tattauna da Shugaba Donald Trump kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Khamenei da manyan shugabannin tsaron Iran 4 da suka rasu, ya rasa wasu iyalansa

Trump ya la’anci harin makamai masu linzami kan Saudiyya, ya kuma jaddada goyon bayan Amurka ga masarautar.

Yariman ya kuma tattauna da Shugaban Syria, Ahmed Al-Sharaa, wanda ya nuna goyon bayan ƙasarsa ga Saudiyya kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com