Khamenei da Manyan Shugabannin Tsaron Iran 4 da Suka Rasu, Ya Rasa Wasu Iyalansa
- Rahotanni daga kafafen yada labarai na Iran sun tabbatar da mutuwar jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei
- Har ila yau, an tabbatar da cewa ministan tsaron kasar da mai ba Khamenei shawara kan tsaro duk sun rasu
- An tabbatar da cewa yar Khamenei, mijinta da jikarsa su ma sun rasa ransu a hare-haren Amurka da Isra’ila
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Kasar Iran ta tabbatar da mutuwar Ayatullah Ali Khamenei a harin da Isra'ila da Amurka suka kai a ranar Asabar.
Wannan lamari ya tayar da kura a ƙasashen duniya inda Iran ta lashi takobin daukar fansar jinin Khamenei.

Source: UGC
Rahoton Aljazeera ya ce bayan mutuwar Khamenei akwai wasu manyan jami'an tsaron kasar da aka hallaka.
Wasu iyalan Khamenei sun rasa rayukansu
Kafafen yada labarai na Iran sun ruwaito a ranar Lahadi cewa ’yar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ta rasu.
Har ila yau, akwai mijinta da jikarsa wadanda su ma suka mutu a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai.
Rahoton ya bayyana cewa an kashe su ne a cikin hare-haren soji da aka kai, a daidai lokacin da rikicin siyasa da na soja ke kara tsananta tsakanin Iran da kasashen biyu.
Rahotanni sun ce bayan tuntubar majiyoyi masu tushe daga cikin gidan Jagoran, an tabbatar da rasuwar ’yar, mijinta da jikarsa.
A cewar rahoton:
“Bayan tuntubar majiyoyi masu tushe daga cikin gidan Jagoran Juyin Juya Hali, cikin bakin ciki an tabbatar da shahadar ’yar, mijinta da jikarsa.”
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da musayar hare-hare da barazana tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila, lamarin da ya janyo damuwa a duniya.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu karin bayani kan cikakkun bayanan yadda harin ya faru ko kuma wurin da aka kai shi.

Source: Getty Images
Khamenei da manyan jami'an Iran da suka rasu
Rahoton The Times of India ya tabbatar da cewa Iran ta Yi rashin manyan jami'anta da suka yi gwagwarmaya a kasar.
Majiyar ta ce daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai ministan tsaron kasar da kuma babban kwamandan IRGC.
Bayan haka, Legit Hausa ta duba manyan shugabannin tsaro a Iran da suka mutu akwai:
1. Jagoran addini a Iran - Ayatullah Ali Khamenei
2. Ministan tsaron Iran - Aziz Nasirzadeh
3. Mai ba Khamenei shawara kan tsaro - Ali Shamkhani
4. Shugaban ma'aikatan sojojin Iran - Janar Abdolrahim Mousavi
5. Babban kwamandan IRGC - Mohammad Pakpour
Ana jimamin mutuwar Ali Khamenei a Iran
An ji cewa dubban mutane sun taru a Tehran suna makokin kisan Ayatollah Ali Khamenei bayan harin hadin gwiwar Amurka da Isra’ila.
IRGC ta sha alwashin daukar mummunan ramuwar gayya kan Isra’ila da sansanonin Amurka a yankin Gulf bayan rasa jagoran addini a Iran.
Shugaba Donald Trump ya gargadi Iran cewa duk wata ramuwar gayya za ta jawo hari mafi tsanani da ba a taba gani ba inda ya ja masu kunne.
Asali: Legit.ng

