Halin da Ake Ciki a Iran bayan Rasuwar Jagoran Addini, Ayatullah Ali Khamenei
- Dubban mutane sun taru a Tehran suna makokin kisan Ayatollah Ali Khamenei bayan harin hadin gwiwar Amurka da Isra’ila
- IRGC ta sha alwashin daukar mummunan ramuwar gayya kan Isra’ila da sansanonin Amurka a yankin Gulf
- Shugaba Donald Trump ya gargadi Iran cewa duk wata ramuwar gayya za ta jawo hari mafi tsanani da ba a taba gani ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran – Dubban masu makoki sun taru a tsakiyar birnin Tehran bayan rahoton kisan Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a harin hadin gwiwar Amurka da Isra’ila.
Masu makokin sun hallara a dandalin Enghelab (Juyin Juya Hali) a ranar Lahadi, sanye da bakaken kaya, wasu suna kuka tare da daga tutocin Iran da hotunan marigayin.

Source: Facebook
Khamenei, wanda ya jagoranci Iran tun 1989, an kashe shi ne a farkon mummunan harin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar, cewar rahoton Aljazeera.
An sanar da dokar zaman makoki a Iran
Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran sun sanar da dokar yin zaman makoki na kwanaki 40 a faɗin ƙasar domin girmama Khamenei.
Wannan mataki ya haɗa da bayar da hutun kwanaki bakwai a jere, inda aka rufe dukkan ofisoshin gwamnati, makarantu, da wuraren kasuwanci, cewar rahoton The Business Standard.
Gidan talabijin na ƙasar ya nuna sanarwar tare da bayyana mutuwarsa a matsayin "shahada," inda aka yi kira ga jama'a da su kiyaye wannan lokaci.
An kaddamar da harin ne domin kifar da gwamnatin Iran, kamar yadda kafafen yada labaran gwamnati suka tabbatar wanda ya jawo fargaba a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da mutuwar malamin mai shekaru 86, yana mai kiran sa “daya daga cikin mafiya sharri a tarihi.”

Source: Getty Images
Khamenei: Iran ta lashi takobin daukar mataki
Rundunar kare juyin juya halin Iran (IRGC) ta sha alwashin hukunci mai tsanani da yanke hukunci ga wadanda ta kira “makasan” Khamenei, tare da alkawarin kaddamar da “hari mafi muni a tarihi” kan Isra’ila da sansanonin Amurka da ke kasashen Gulf.
A gefe guda, Trump ya gargadi cewa duk wata ramuwar gayya daga Iran za ta jawo mata hari da karfi “wanda ba a taba gani ba.”
Rahotanni sun ce an sake jin karar fashewar abubuwa a Doha, Dubai da Manama, yayin da siren gargadi suka rika kara a tsakiyar Isra’ila, inda sojojin Isra’ila suka ce suna mayar da martani ga harba makamai masu linzami daga Iran.

Source: Facebook

Source: Facebook

Source: Facebook
Khamenei: Iran ta sha alwashin daukar fansa
Mun ba ku labarin cewa Iran ta gabbatar da mutuwar jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, a hare-haren Amurka da Isra’ila da aka kai masu.
Gwamnatin Iran ta ayyana kwanaki 40 na zaman makoki da hutun jama’a bakwai domin jimamin wannan babban rashi da ya same su.
Rundunar tsaron ƙasar ta IRGC ta yi alkawarin ɗaukar fansa kan waɗanda ta kira “makasan” jagoran addini a Iran wanda ya jawo suka daga wasu kasashen duniya.
Asali: Legit.ng

