Iran/Isra’ila: Abin da Trump da Yariman Saudiyya Suka Tattauna a Wayar Tarho

Iran/Isra’ila: Abin da Trump da Yariman Saudiyya Suka Tattauna a Wayar Tarho

  • Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya tattauna da Shugaba Donald Trump kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya
  • Trump ya la’anci harin makamai masu linzami kan Saudiyya, ya kuma jaddada goyon bayan Amurka ga masarautar
  • Yariman ya kuma tattauna da Shugaban Syria, Ahmed Al-Sharaa, wanda ya nuna goyon bayan ƙasarsa ga Saudiyya kan lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Riyadh, Saudiyya – Yarima mai jiran gadon Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya yi magana ta waya da Shugaban Amurka, Donald Trump.

Yariman ya samu kiran waya daga Donald Trump, a ranar Asabar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki.

Trump ya kira Yariman Saudiyya a wayar tarho
Shugaba Donald Trump da Dan Sarkin Saudiyya, Mohammed bin Salman. Hoto:Getty Images.
Source: Getty Images

Arab News ta tabbatar da cewa Yarima da kuma Trump sun yi magana kan harin Iran a Saudiyya da kuma fargabar karuwar rikici a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Amurka da Isra'ila sun kashe jagoran addinin Musulunci na Iran? Gaskiya ta bayyana

Yadda rikici ya barke tsakanin Iran da Isra'ila

Wannan tattaunawa na zuwa ne bayan barkwar rikici tsakanin Iran da Isra'ila a safiyar ranar Asabar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026.

Hukumomin kasar Isra'ila sun tabbatar da kai Iran wanda ya jawo asarar rayuwa da dukiyoyi inda wasu rahotanni ke cewa harin ya shafi makarantar yara mata.

Daga bisani, Iran ta mayar da martani tare da neman daukar fansa kan wasu ofisoshin Amurka da Isra'ila da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Hakan ne ma ya sa kasashen Larabawa suka shiga wani yanayi dalilin hare-haren Iran a wasu biranen kasashensu da dama.

Trump ya yi Allah-wadai da harin Iran a Saudiyya
Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Donald Trump.
Source: Getty Images

Tattaunawar Trump da Yariman Saudiyya

A yayin tattaunawar, Trump ya bayyana Allah-wadai da harin makamai masu linzami da aka kai kan masarautar Saudiyya, wanda rundunar tsaron sararin samaniyar ƙasar ta samu nasarar dakilewa.

Ya kuma jaddada cikakken goyon bayan Amurka ga Saudiyya, tare da bayyana goyon baya ga duk matakan da masarautar ke ɗauka domin tinkarar irin waɗannan hare-haren.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki a rigimar Iran da Isra'ila, Najeriya ta ba da shawara

An tabbatar da cewa hare-haren sun fito daga Iran, waɗanda ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin da a yanzu ya sake rikicewa, cewar Qatar News Agency.

Yariman Saudiyya ya yi magana da shugaban Syria

A wata tattaunawa ta daban, Yarima Mohammed bin Salman ya kuma yi magana ta wayar tarho da Shugaban Syria, Ahmed Al-Sharaa, inda suka tattauna kan ci gaba da rikicin soji a yankin.

Rahotanni sun ce Al-Sharaa ya tabbatar da goyon bayan ƙasarsa da haɗin kai da Saudiyya, yana mai jaddada kin amincewar Syria da duk wani cin zarafin ikon mallakar Saudiyya ko barazana ga tsaro da zaman lafiyarta.

Iran/Isra'ila: An ji abubuwan fashewa a Saudiyya

Kun ji cewa wasu rahotanni sun ce an ji karar fashe-fashe a biranen Riyadh, Dubai da Abu Dhabi bayan Iran ta harba makamai masu linzami.

Mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa sun tabbatar da cafke makamai masu linzami, inda rahotanni suka ce mutum guda ya mutu a Abu Dhabi.

Tashin hankalin ya biyo bayan hare-haren hadin gwiwa da Israel da Amurka suka kai kan Iran, lamarin da ya kara dagula tsaro a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.