Jagoran Musulunci na Iran: Mutane 5 da Za Su Iya Maye Gurbin Ayotallah Khamenei
Iran - Gwamnatin Iran yanzu tana fuskantar ƙalubalen gano wanda zai gaji Ayatollah Ali Khamenei bayan Amurka da Isra'ila sun kashe shi.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Tsohon shugaban, wanda ya yi mulki na kusan shekaru 40, bai ayyana magaji a hukumance ba har aka kashe shi. Yanzu dai majalisar manyan malamai 88 ce ke da alhakin zaɓar sabon jagora.

Source: UGC
Neman magajin Ayotallah Khamenei
Wannan babban aiki ne da majalisar ta taɓa yi sau ɗaya kawai tun kafa jamhuriyar Musulunci a 1979, lokacin da aka zaɓi Khamenei bayan mutuwar Ayatollah Ruhollah Khomeini shekaru 30 da suka wuce, in ji rahoton CNN.
Hukumomin ƙasar za su so su yi hanzari domin nuna cewa akwai zaman lafiya, inda ake sa ran mambobin majalisar za su gana nan ba da jimawa ba domin tattaunawa kan ƴan takara kafin sanar da sabon shugaba.
To sai dai, ba a sani ba ko za su iya kasadar yin taron ganin yadda Shugaba Donald Trump ya sha alwashin cewa hare-haren Amurka da Isra'ila kan gwamnatin za su ci gaba a kwanaki masu zuwa.
Sabon jagoran Iran dole ne ya kasance namiji, malami mai hikimar siyasa, kwarjini, da kuma biyayya ga tsarin jamhuriyar Musulunci yanzu.
Mutum 5 da za su iya maye gurbin Khamenei
Ga jerin mutum 5 da za a iya maye gurbin Khamenei:
1. Mojtaba Khamenei (Shekaru 56)

Source: Getty Images
Mojtaba shi ne ɗa na biyu ga marigayi Khamenei, kuma an san shi da samun gagarumin tasiri tare da ƙwaƙƙwarar alaƙa da dakarun kare juyin juya hali (IRGC) da kuma dakarun Basij.
Sai dai, mika mulki daga uba zuwa ɗa abu ne da ake ƙyama a tsarin malaman Shi'a, musamman a Iran ɗar da ta kifar da mulkin sarauta.
Wani cikas shi ne cewa Mojtaba ba babban malami ba ne kuma ba shi da wani matsayi na hukuma a gwamnati, sannan Amurka ta sanya masa takunkumi a 2019.
2. Alireza Arafi (Shekaru 67)

Source: Twitter
Arafi malami ne da aka sani wanda ya riƙe muƙamai a hukumomin gwamnati kuma amintaccen Khamenei ne, in ji rahoton CNBC News.

Kara karanta wannan
Jingir ya yi fito na fito da shirin kafa 'yan sandan jihohi, malamin ya yi zargin munafurci
A halin yanzu shi ne mataimakin shugaban majalisar kwararru kuma mamba ne a majalisar koli ta Guardian Council.
Masana sun bayyana cewa Khamenei ya nuna amincewa da iyawarsa ta hanyar ba shi manyan muƙamai, kodayake ba a san shi da samun alaƙa ta kusa da hukumomin tsaro ba.
3. Mohammad Mehdi Mirbagheri (Shekaru 60)
Mirbagheri malami ne mai tsauraran ra'ayi kuma mamba a majalisar kwararru wanda ke wakiltar ɓangaren da ya fi kishin mazan jiya.
Kwanan nan aka ruwaito shi yana kare yawan asarar rayuka a yaƙin Gaza, inda ya ce mutuwar ko da rabin mutanen duniya ce "ta cancanta" idan za a samu kusanci da Allah.
Yana adawa da kasashen Yamma sosai kuma ya yi imanin cewa dole ne a yi yaƙi tsakanin muminai da kafirai, cewar rahoton Iran Wire.
4. Hassan Khomeini (Shekaru 50)

Source: Twitter
Khomeini jikan wanda ya kafa jamhuriyar Musulunci ne, Ayatollah Ruhollah Khomeini, wanda hakan ya ba shi daraja ta addini da juyin juya hali.
Yana lura da makabartar Khomeini amma bai taɓa riƙe muƙamin gwamnati ba kuma ba shi da tasiri ga jami'an tsaro.
An san shi da rashin tsauraran ra'ayi idan aka kwatanta da takwarorinsa, har ma an hana shi takarar majalisar kwararru a 2016.
4. Hashem Hosseini Bushehri (Shekarun 60)

Source: Twitter
Bushehri babban malami ne dake da alaƙa da hukumomin da ke lura da mika mulki, musamman majalisar kwararru inda yake matsayin mataimakin shugaba na farko.
An ce yana da kusanci da Khamenei amma ba a cika sanin sa ba a cikin gida, sannan ba shi da wata alaƙa ta kusa da dakarun IRGC.
An kashe Ayotallah Khamenei a Iran
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Iran ta tabbatar da kisan jagoran Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei sakamakon harin hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila.
An kashe jagoran ne a ofishinsa dake rukunin Beit Rahbari yayin da yake gudanar da ayyukansa na yau da kullum a ranar Asabar.
Iran za ta gudanar da zaman makokin kwanaki 40 yayin da Isra'ila ta kaddamar da sababbin hare-hare kan makaman linzamin kasar.
Asali: Legit.ng

