Iran: Raɗe Raɗin Kashe Khamenei na Ƙara Ƙarfi daga Majiyoyin Amurka da Isra'ila

Iran: Raɗe Raɗin Kashe Khamenei na Ƙara Ƙarfi daga Majiyoyin Amurka da Isra'ila

  • Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an kashe jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei a ranar Asabar, a hare-haren sama
  • Shi ma Shugaba Donald Trump ya shaidawa manema labarai cewa rahotannin da ake yadawa kan kisan Khamenei gaskiya ne
  • Sai dai, ministan harkokin wajen Iran ya karyata rahotannin, inda ya ce Khamenei da Shugaba Masoud Pezeshkian suna nan raye

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran - Wani babban jami'in kasar Isra'ila ya shaida wa manema labarai cewa, jagoran addinin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya riga mu gidan gaskiya.

Wannan jami'i, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya ce Khamenei ya mutu ne sakamakon wasu hare-haren sama da hadin gwiwar sojin Amurka da Isra'ila suka kai Iran.

Jita jita kan kisan jagoran addinin Musulunci na Iran, Ayotallah Ali Khamenei ta kara karbi.
Jagoran addinin Musulunci na Iran, Ayotallah Ali Khamenei. Hoto: @khamenei_ir
Source: Twitter

"Ba ya tare da mu," Netanyahu kan Khamaenei

Kara karanta wannan

Iran ta maida martani kai tsaye ga Amurka kan yunkurin kifar da gwamnatin Musulunci

Ko da yake hukumomin Iran ba su tabbatar da mutuwar Khamenei ba tukuna, majiyoyin Isra'ila sun shaida wa kamfanin labaran Reuters cewa suna da hoton gawar tasa.

Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa akwai alamun da ke nuna cewa Khamenei "ba ya tare da mu" a halin yanzu, wanda ke nufin, "ya rigamu gidan gaskiya."

Sai dai, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran ya musanta hakan, yana mai cewa jagoran yana nan "cikin koshin lafiya."

Amma rashin ganin Ayotallah Khamenei a bainar jama'a tun lokacin da hare-haren suka fara ya jawo karuwar rade-radin, na cewar ya mutu.

Trump ya gasgata rahoton kisan Khamenei

Amurka da Isra'ila sun kaddamar da manyan hare-hare a Iran a ranar Asabar, inda kafofin watsa labaran Iran suka ce mutanen da suka mutu sun haura 200.

A cikin wani sakon bidiyo, an ji Shugaba Donald Trump yana cewa:

"Manufarmu ita ce kare al'ummar Amurka ta hanyar kakkabe duk wata barazana daga gwamnatin Iran, wadda ke tattare da wasu mutanen banza."

Donald Trump, ya shaida wa kamfanin labaran NBC cewa, "muna da yakin cewa labaran gaskiya ne," yayin da yake martani kan rahotannin da ke cewa an kashe jagoran Iran, Ali Khamenei a harin sama.

Kara karanta wannan

Amurka da Isra'ila sun kashe jagoran addinin Musulunci na Iran? Gaskiya ta bayyana

Amma Esmaeil Baghaei, ministan wajen Iran ya karyata wadannan rahotanni, inda ya tabbatar da cewa Khamenei da shugaban Iran, Masoud Pezeshkian suna nan a raye.

Sai dai, har kawo wannan lokaci, Legit Hausa ba ta iya tantance hakikanin halin da Khamenei yake ciki ba, ko yana raye, ko ya mutu.

Ministan harkokin wajen Iran ya karyata jita jitar cewa an kashe Ayatollah Khamenei.
Jagoran addinin Musulunci na Iran, Ayotallah Ali Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tasirin Khamenei ga Iran da Gabas Ta Tsakiya

Khamenei, mai shekaru 86, ya zama jagoran Iran mafi daraja tun a shekarar 1989 bayan rasuwar Ayatollah Ruhollah Khomeini, in ji rahoton CNN.

A karkashin mulkinsa, Iran ta zama babbar abokiyar adawar Amurka a yankin, inda ya fadada tasirin sojan kasar a fadin Gabas ta Tsakiya ta hanyar goyon bayan kungiyoyi irin su Hamas da Hezbollah.

Idan har ta tabbata, to kisan Khamenei zai babban kalubale ga Iran, wadda take fama da yakin basasa da matsalolin tattalin arziki tun bayan yakin kwanaki 12 da aka yi a watan Yunin 2025.

Iran ta farmaki sansanonin Amurka

A wani labari, mun ruwaito cewa, Iran ta kai hare-haren makami mai linzami kan sansanonin sojojin Amurka dake kasashen Qatar, Kuwait, Bahrain da UAE.

Kara karanta wannan

Halin da Khamenei da shugaban Iran ke ciki bayan hare haren Amurka da Isra'ila

Akalla mayaka biyu ne suka rasa rayukansu a kasar Iraki sakamakon hare-haren sama da aka kai kan sansanin dakarun Hashid Shaabi.

Hukumomin Bahrain da Qatar sun kunna kararrawar gargadi yayin da suke kokarin kakkabo makaman linzamin da kasar Iran ta harba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com