Iran Ta Maida Martani Kai Tsaye ga Amurka kan Yunkurin Kifar da Gwamnatin Musulunci

Iran Ta Maida Martani Kai Tsaye ga Amurka kan Yunkurin Kifar da Gwamnatin Musulunci

  • Iran ta maida martani kan kalaman shugaban Amurka, Donald Trump cewa yana da burin kifar da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta kasar
  • Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana wannan yunkuri a matsayin aikin da ba zai yiwu ba saboda goyon bayan 'yan Iran
  • Ya kuma tabbatar da cewa manyan jami'an gwamnati ciki har da shugaban kasa, Masoud Pezeshkian suna nan a raye bayan harin Amurka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Yayin da musayar wuta ta kara zafi, gwamnatin Iran ta bayyana yunkurin Amurka da Isra'ila na kifar da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci a matsayin abin da ba zai yiwu ba.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ne ya bayyana haka yayin da yake martani ga ikirarin shugaban Amurka, Donald Trump cewa burinsu su canza gwamnati a Iran.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki a rigimar Iran da Isra'ila, Najeriya ta ba da shawara

Abbas Araghchi.
Ministan harkokin waje na kasar Iran, Abbas Araghchi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta maida martani ga Amurka

Abbas Araghchi ya shaidawa NBC News, a wata hira yau Asabar, cewa kifar da gwamnatin Iran a halin yanzu, aiki ne gagarumi kuma wanda ba zai yiwu ba kwata-kwata.

Araghchi ya ce farmakin hadin gwiwar soji da aka kaddamar da safiyar ranar ba zai iya haifar da sauyin gwamnati ba, ganin cewa miliyoyin ’yan Iran na goyon bayan Jamhuriyar Musulunci.

Ya yi ikirarin cewa a ranar 11 ga Fabrairu, kusan ’yan Iran miliyan 30 sun fito kan tituna domin bikin cika shekaru 47 da juyin juya halin Musulunci, inda suka nuna goyon bayansu ga shugabannin da ke kan mulki.

“Eh, duk da haka mun cewa akwai kuma mutanen da ke korafi, amma a lokaci guda akwai gagarumin goyon baya ga gwamnati da tsarin da muke kai a yanzu,” in ji shi.

Amurka ta kashe shugabannin Iran?

Da aka tambaye shi ko zai iya tabbatar da cewa jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, yana raye, Araghchi ya amsa cewa, “a iya abin da na sani, yana raye.”

Kara karanta wannan

Halin da Khamenei da shugaban Iran ke ciki bayan hare haren Amurka da Isra'ila

Ya kara da cewa shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, shugaban bangaren shari’a, kakakin majalisa, shugaban majalisar tsaron kasa da “dukkan manyan jami’ai” suna raye.

“Mai yiwuwa mun rasa kwamandoji daya ko biyu, amma hakan ba babbar matsala ba ce,” in ji Araghchi.
Iran.
Shugaban kasar Iran da jagoran addini, Imam Ayatullahi Khamenei Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Ya kuma yi ikirarin cewa “komai yana tafiya lafiya,” yana mai cewa Amurkawa da Isra’ilawa “sun kasa cimma manufofinsu.”

Ya kara da cewa Iran na da “tsarin siyasa mai karfi da tsari,” kuma duk wani yunkuri da aka taba yi a baya na kifar da gwamnatin Musulunci ya ci tura, cewar rahoton JNS.

An rufe sararin samaniyar kasashe 8

A wani labarin, kun ji cewa akalla kasashe takwas ne suka rufe sararin samaniyarsu sakamakon hare-haren da ake yi tsakanin Amurka da kasar Iran.

Jerin hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran, da kuma martanin da Tehran ta mayar, ya haddasa barkewar tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.

Akalla kasashe takwas ne suka sanar da rufe sararin samaniyar su a ranar Asabar, ciki har da Iran, Isra'ila, Iraki, Jordan, Qatar, Bahrain, Kuwait, da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE),

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262