Rigimar Iran da Isra’ila: Bam Ya Tarwatse a Saudiyya, an Shiga Dimuwa Mai Tsanani

Rigimar Iran da Isra’ila: Bam Ya Tarwatse a Saudiyya, an Shiga Dimuwa Mai Tsanani

  • Rahotanni sun ce an ji karar fashe-fashe a biranen Riyadh, Dubai da Abu Dhabi bayan Iran ta harba makamai masu linzami
  • Mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa sun tabbatar da cafke makamai masu linzami, inda rahotanni suka ce mutum guda ya mutu a Abu Dhabi
  • Tashin hankalin ya biyo bayan hare-haren hadin gwiwa da Israel da Amurka suka kai kan Iran, lamarin da ya kara dagula tsaro a yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Riyadh, Saudiyya - Tashin hankali a Gabas ta Tsakiya ya kara kamari bayan an ji karar fashe-fashe a biranen Riyadh, Dubai da Abu Dhabi.

Hakan ya biyo bayan rahoton harba makamai masu linzami daga Iran yayin da ake ci gaba da takun-saka tsakaninta da Isra'ila.

Bam ya fashe a Saudiyya bayan harin Iran
Dan Sarkin Saudiyya, Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud. Hoto: @insharifain.
Source: Twitter

Lamarin ya faru ne bayan Isra’ila tare da Amurka sun kaddamar da wasu hare-haren hadin gwiwa da suka kai kan wasu wurare a Iran, abin da ya kara haifar da fargabar barkewar rikici mai fadi a yankin, cewar Hindustan Times.

Kara karanta wannan

Halin da Khamenei da shugaban Iran ke ciki bayan hare haren Amurka da Isra'ila

Biranen da aka ji fashe-fashe a yau

Rahotanni sun ce an ji karar manyan amo a sassa daban-daban na Abu Dhabi, ciki har da yankin Corniche.

Shaidu sun bayyana cewa an ji fashe-fashe da dama a jere, har ma tagogi suna karkarwa sakamakon dakile makaman da aka harba.

Mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa sun tabbatar da cewa sun samu nasarar cafke wasu makamai masu linzami da suka nufi yankinsu, sun ce mutum guda ya rasa ransa a Abu Dhabi.

Haka kuma, an ruwaito karar wata babbar fashewa a Dubai, sai dai jami’ai ba su bayyana ko tana da alaka kai tsaye da cafke makamai ko wani aikin tsaro ba.

A Riyadh, babban birnin Saudiyya, mazauna garin sun ce sun ji karar fashe-fashe a lokaci guda, bayan Iran ta bayyana aniyarta ta mayar da martani kan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai.

Hayaki ya turnuke a Saudiyya bayan fashewar bam
Yadda hayaki ya fara tashi a Iran bayan harin Isra'ila. Hoto: Getty Images.
Source: Getty Images

Matakan da aka dauka bayan fashewar

Duk da cewa hukumomin Saudiyya ba su bayyana cikakkun bayanai kan barnar ko asarar rayuka ba, rahotanni sun nuna cewa an tsaurara matakan tsaro a fadin kasar, cewar The Times of Israel.

Kara karanta wannan

An rufe sararin samaniyar kasashe 8 da yaki ya barke tsakanin Iran da Amurka

Masu sharhi sun ce wannan sabon mataki na nuna cewa rikicin Isra’ila da Iran na iya wuce yankin da ake fafatawa a halin yanzu, lamarin da ke barazana ga tsaron kasashen Gulf da kuma zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa.

Shugabannin kasashe daban-daban na ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki, sakamakon fargabar cewa rikicin na iya bazuwa a fadin Gabas ta Tsakiya baki daya.

Martanin Saudiyya kan fashewar bam a Riyadh

Ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar da sanarwa a shafin X inda take Allah-wadai da harin Iran a Riyadh.

Kasar ta caccaki Iran tare da bayyana matsayarta cewa ba za ta taba kasa a guiwa ba wurin ci gaba da goyon bayan kasashen Larabawa yan uwanta ba.

Isra'ila ta kai hari a Iran

Kun ji cewa Isra’ila ta kaddamar da abin da ta kira “harin riga-kafi” kan Iran, a cewar Ministan Tsaro na kasar, Israel Katz, yayin da ta ayyana dokar ta-baci.

Gwamnatin ta ayyana dokar ta-baci ne saboda tsammanin martanin Iran ta hanyar amfani da jiragen yaki marasa matuki da kuma makamai masu linzami.

An ji karar fashe-fashe da dama a birnin Tehran na kasar Iran, babban birnin kasar, yayin da aka kuma rawaito fashe-fashe a wasu wurare daban-daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.