Jirgin Sama Dauke da Makudan Kudi Ya Gamu da Hatsari, Mutane Sun Daka Wawa

Jirgin Sama Dauke da Makudan Kudi Ya Gamu da Hatsari, Mutane Sun Daka Wawa

  • Wani jirgin sama na dakon kaya mallakin rundunar sojojin Bolivia ya yi hatsari a kusa da babban birnin kasar, La Paz
  • Rahotanni sun nuna jirgin ya dauko takardun kudi masu yawa lokacin da ya rikito kan titi, an tabbatar da mutuwar mutane 20
  • Gwamnatin Bolivia ta gargadi mazauna yankin da aka ce sun daka wawa kan kudin da jirgin ya dauko, ta ce amfani da su babban laifi ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bolivia - Akalla mutane 20 ne suka riga mu gidan gaskiya sa'ilin da wani jirgin jigilar kayayyaki na sojin ƙasar Bolivia, wanda ke ɗauke da takardun kuɗi, ya yi hatsari.

Jirgin saman, wanda ke dauke da makudan kudi, ya gamu da hatsari ne yayin da yake ƙoƙarin sauka kusa da babban birnin ƙasar, La Paz.

Kara karanta wannan

Bayan kai hari masallaci, 'yan bindiga sun sace mata masu ciki a Sokoto

Jirgin sama.
Jirgin sama yayim da yake tsakiyar tafiya a sararin samaniya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jirgin sama dauke da kudi ya yi hatsari

Rundunar 'yan sanda ta sanar da hakan a ranar Juma'a, yayin da cincirindon jama'a suka yi ƙoƙarin kwashe kuɗaɗen da suka watsu, kamar yadda tashar Channels ta kawo.

Jirgin, samfurin C-130 Hercules wanda kamfanin Lockheed Martin ya kera, ya kauce hanyarsa ne a filin jirgin sama na El Alto, inda ya faɗa kan wani babban titi, ya murƙushe motoci da dama.

Jama'a sun daka wa kudi wawa a Bolivia

An ga baraguzan jirgin a kan titin da ya faɗa, sannan an hango mutane na rugawa domin kwashe tsabar kuɗin da suka watsu, lamarin da ya sa 'yan sanda harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa su

Jaridar The Times of India ta dauko rahoton cewa daga bisani, an hango jami'ai suna cinna wa kuɗaɗen wuta a wurin da hatsarin ya afku.

Har yanzu ba a tantance musabbabin hatsarin ba, amma shaidu sun shaida cewa yanayin sararin samaniya ya kasance mai matuƙar haɗari.

Kara karanta wannan

Wani ya shigo masallaci da makami tsirara, masallata 5000 sun fice ana azumi

"Akwai ƙanƙara mai ƙarfi tana fadowa kuma ana yin walƙiya” lokacin da jirgin ya faɗo, in ji Cristina Choque, wata mai sayar da kaya 'yar shekara 60 wacce fallen jirgin ya faɗa wa motarta.

An tabbatar da mutuwar mutane 20

Ma'aikatar Tsaron ƙasar ta ce za ta ƙaddamar da bincike kan hatsarin. Kwamandan 'yan sanda mai kula da sashin binciken kisan kai a El Alto, Colonel Rene Tambo, ya shaida wa manema labarai cewa an yi asarar rayuka "kusan 20, ko ma fiye da haka."

Ma'aikatar Lafiya ta Bolivia ta bayar da rahoton cewa akalla mutane 28 ne suka ji rauni, wadanda yanzu haka suke karbar magani.

Jirgin Bolivia.
Wurin da jirgin jigilar kaya ya fado dauke da kudi a kasar Bolivia Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cikin wata sanarwa, ma'aikatar tsaron ta bayyana cewa:

“Kuɗaɗen da jirgin ke ɗauke da su ba su da lambar shaida ta hukuma saboda haka ba za a iya amfani da su ba a doka. Tarawa, mallaka, ko amfani da su babban laifi ne.”

Karamin jirgin sama ya fado titi a Georgia

A wani rahoton, kun ji cewa wani matuki da dalibinsa sun tsira daga mutuwa bayan karamin jirginsu ya yi hatsari a kan babbar hanya a jihar Georgia.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan Boko Haram sun farmaki karamar hukumar gwamna ana cikin Ramadan

Rahotanni daban-daban sun nuna cewa jirgin ya fuskanci matsalar inji ne jim kaɗan bayan ya tashi daga filin tashi da sauka na Lee Gilmer Memorial.

Matukin jirgin Thomas Rogers ya yi ban kwana da iyalinsa ta hanyar aika sakon murya bayan ya fahimci cewa injin jirgin ya daina aiki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262