Iran Ta Harba Makamai Masu Linzami, Sun Sauka kan Manyan Sansanonin Amurka 4
- Kasar Iran ta kaddamar da hare-haren makami mai linzami kan sansanonin sojojin Amurka dake kasashen Qatar, Kuwait, Bahrain da UAE
- Akalla mayaka biyu ne suka rasa rayukansu a kasar Iraki sakamakon hare-haren sama da aka kai kan sansanin dakarun Hashid Shaabi
- Hukumomin Bahrain da Qatar sun kunna kararrawar gargadi yayin da suke kokarin kakkabo makaman linzamin da kasar Iran ta harba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iran - Kasar Iran ta kaddamar da gagarumin harin makami mai linzami kan sansanonin sojojin Amurka da ke a wasu manyan kasashen Gulf guda hudu.
Makaman Iran sun sauka a sansanonin sojojin Amurka a kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Qatar, Bahrain, da kuma Kuwait.

Source: Getty Images
Iran ta farmaki sansanonin Amurka
Wannan mataki ya janyo fargaba da tashin hankali a fadin shiyyar Gabas Ta Tsakiya, kamar yadda rahoton Aljazeera ya nuna.

Kara karanta wannan
Amurka da Isra'ila sun kashe jagoran addinin Musulunci na Iran? Gaskiya ta bayyana
Kafafen yada labaran Iran sun ruwaito cewa an kai hare-haren ne a lokaci guda kan muhimman wuraren da sojojin Amurka ke amfani da su yau.
Wuraren da makaman Iran suka sauka sun hada da:
- Qatar: Sansanin saman Al Udeid.
- Kuwait: Sansanin saman Al Salem.
- UAE: Sansanin saman Al Dhafra.
- Bahrain: Hedkwatar runduna ta biyar ta Amurka.
Kafofin yada labarai sun ruwaito karar fashe-fashe masu karfi a birnin Abu Dhabi. Haka kuma, hukumomin Bahrain sun tabbatar da cewa an harba makami mai linzami kan rundunar sojojin Amurka ta biyar, inda aka kunna kararrawar gargadi a fadin kasar.
Yanayin tsaro a Qatar da Iraki
Duk da cewa an ji fashe-fashe biyu a birnin Doha, ma'aikatar tsaron Qatar ta bayyana cewa dakarunta sun yi nasarar kakkabo dukkan makaman da aka harba zuwa kasarta yanzu.
A gefe guda kuma, a kasar Iraki, an kashe mayakan Hashid Shaabi guda biyu sannan wasu uku sun jikkata bayan wasu hare-haren sama da aka kai a yankin Jurf al-Sakhar da ke kudancin Bagadaza.
Wadannan mayaka na PMF, wadanda bangare ne na jami'an tsaron Iraki, suna da alaka ta kut-da-kut da kasar Iran yanzu, in ji rahoton Reuters.

Source: Getty Images
Dalilin kai hare-haren Iran
Wannan harin na Iran ya zo ne a matsayin martani ga hare-haren hadin gwiwar sojojin Amurka da Isra'ila da suka kai kan wasu muhimman wurare a Tehran.
Rahoton BBC ya nuna cewa Tehran ta yi rantsuwar daukar fansa, tana mai zargin Washington da kai mata hari kai-tsaye.
Masana harkokin soja sun yi gargaɗin cewa wannan takaddama na iya jefa kasashen yankin Gulf cikin babban yaki wanda zai iya dagula lissafin tsaron duniya baki daya.
Halin da dan Najeriya yake ciki a Kuwait
A zantawar Legit Hausa da wani matashi Sadiq Madabo, wanda yanzu haka yake zaune a Kuwait, ya shaida cewa babu wata sanarwar gargadi da suka samu cewa za a kai hare-hare.
"Babu wata sanarwa da muka samu cewa wannan yaki zai barke tsakanin kasashe guda biyu, amma dama mun san ana zaman doya da manja tsakanin Isara'ila da Iran da kuma Amurka da ke tare da Isra'ila.

Kara karanta wannan
Rigimar Iran da Isra'ila: Bam ya tarwatse a Saudiyya, an shiga dimuwa mai tsanani
"Ba mu san da cewa yakin zai sake barkewa ba. Musamman ma mu da muke nan (Kuwait) ba mu san yakin zai zo ya shafi kasashen da muke ciki ba, amma mun san Amurka na da sansanoni a nan (Kuwait) da sauran kasashen Larabawa da ke kewaye da Iran."
- Sadiq Madabo.
Sadiq Madabo ya ce wannan yakin ya zo da sabon salo, domin kuwa shirin da Iran ta yi wannan karon ya fi wanda ta yi a shekarar baya, don haka ba kanwar lasa ba ce.
"A yanzu na ga hakikanin karfin Iran, domin kan ka ce me, sun kai hare-hare a kasashe bakwai na Larabawa. Amma ina rokon Allah ya takaita, don idan ya wuce haka, to wasu kasashe za su iya shiga."
- Sadiq Madabo.
Trump ya magantu kan kai hari Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, Amurka da Isra’ila sun kai hare-haren soja kan wasu wurare a Iran da sanyin safiyar Asabar, bayan jerin barazanar Shugaba Donald Trump.
Tun kafin hakan ma, ya taba yi mata barazana kan yadda ya ce ta murkushe masu zanga-zanga a watan Janairun 2026, amma bai kai hari ba a lokacin.
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafukansa na soshiyal midiya, Shugaba Donald Trump ya yi gargadi ga Iran, inda ya sanar da cewa tare da Isra'ila suka kai harin.
Asali: Legit.ng
