Iran Ta kai Hare Hare Isra'ila, Hayaki na Tashi a Sansanin Sojin Amurka
- Rahotanni sun nuna cewa kasar Iran ta kaddamar da jerin hare-hare da makamai masu linzami zuwa Isra'ila bayan harin da aka kai mata
- Hakan na zuwa ne jim kadan bayan shugaba Donald Trump ya sanar da cewa ya hada kai da Isra'ila wajen kai hari kasar Iran da safiyar Asabar
- Bayan harin Iran zuwa Isra'ila, wasu bayanai sun tabbatar da an ji kara a wani sansanin sojin Amurka a Bahrain, hayaki ya tashi daga baya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Gwamnatin Iran kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki zuwa Isra’ila bayan harin da Amurka ta kai mata daga kasar.
An fara yaki tsakanin kasashen ne bayan an gaza cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran game da mallakar makaman nukiliya da sauransu.

Kara karanta wannan
Iran ta sha alwashi mai zafi bayan Israila da Amurka sun kai mata hari, ta fadi shirinta

Source: Getty Images
Iran ta kai hare-hare Isra'ila
Al-Jazeera ta rahoto cewa rundunar IRGC ta Iran ta tabbatar da cewa ta harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki zuwa Isra’ila bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai.
Sanarwar Iran ta ce:
“A martani ga harin da makiya suka kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, an fara kaddamar da zagayen farko na manyan hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki.”
An farmaki sansanin sojin Amurka
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa an ga hayaki daga yankin Juffair na kasar Bahrain, inda hedkwatar rundunar ruwan Amurka take.
Biyo bayan labarin, kasar Bahrain ta tabbatar da cewa hedkwatar rundunar ruwan Amurka ta fuskanci harin makami mai linzami a yau Asabar.
Haka kuma, an ruwaito cewa an ji karar fashe-fashe mai karfi a babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa, Abu Dhabi, bayan harba makamai da Iran ta yi.

Source: Getty Images
Kiran Iran ga 'yan kasarta
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Iran ta ce Trump ya karya duk dokokin kasa da kasa, inda ya kai hari yayin da kaashen biyu ke tattaunawa.
A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta umarci gwamnoni a duk fadin kasar da su tuna da umarnin da aka ba su a baya, tare da bayar da rahotanni cikin gaggawa kan halin da ake ciki a jihohi.
Sanarwar ta ce:
“A tattara dukkan kayan aiki domin magance bukatun gaggawa na jama’a.”
Wani babban jami’in Iran ya shaida cewa sun gargadi Isra’ila da ta “shirya ga abin da ke tafe, domin martaninmu zai kasance a fili ba tare da tsoro ba.
“Kai hari kan dukkan kadarorin Amurka da Isra’ila da muradunsu a Gabas ta Tsakiya ya zama halas.
"Babu zaman lafiya bayan wannan hari, kuma komai na iya faruwa, har da abubuwan da ba a taba tunanin su a baya ba,”
Inji jami’in
Shugaba Donald Trump ya kai hari Iran
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fitar da sanarwa bayan harin da ya ce sun kai biranen kasar Iran.
Trump ya bayyana cewa su suka kai harin kuma za su cigaba domin kawar da gwamnatin Musulunci da ta shafe shekaru tana mulki.
Ya yi kira ga mutanen Iran da su fito su karbe mulki daga hannun Ayatolla Ali Khamenei, inda ya ce ba lallai su sake samun irin damar ba.
Asali: Legit.ng

