Trump Ya Ce Su Suka kai Hari Iran, Ya Fadi Babban Burinsa a kan Khamenei
- Shugaban Amurka ya fito ya yi magana game da harin da aka kai kasar Iran da safiyar yau Asabar, inda ya ce Amurka ta hada kai da Isra'ila
- Trump ya bayyana cewa za su gama da gwamnatin kasar, inda ya bukaci mutanen Iran su fito su karbi kasar idan ya gama samun nasara
- Ya kara da cewa yana so sojojin Iran su ajiye makamai su mika wuya ga Amurka, abin da kasar ta sha cewa ba zai taba yi wu ba a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Amurka da Isra’ila sun kai hare-haren soja kan wasu wurare a Iran da sanyin safiyar Asabar, bayan da Shugaba Donald Trump ya shafe makonni yana barazanar matsa wa gwamnatin Iran lamba.
Tun kafin hakan ma, ya taba yi mata barazana kan yadda ya ce ta murkushe masu zanga-zanga a watan Janairun 2026, amma bai kai hari ba a lokacin.

Source: Getty Images
Maganar Donald Trump kan kai hari Iran
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na X, Shugaba Donald Trump ya yi gargadi ga Iran, inda ya sanar da cewa tare da Isra'ila suka kai harin.
Ya ce:
“Amurka na gudanar da wani babban aiki mai zurfi da ke gudana domin hana wannan muguwar gwamnatin kama-karya barazana ga Amurka da muhimman muradunta na tsaro.”
Kafin hare-haren, sojojin Amurka sun tura fiye da jiragen ruwa da jiragen sama 12 zuwa Gabas ta Tsakiya, yayin da gwamnatin Trump ke matsa lamba ga Iran tare da gudanar da tattaunawar nukiliya a fakaice da jami’an Iran.
Kiran Trump ga sojojin kasar Iran
Bayan sanar da “manyan” hare-haren soja na Amurka kan Iran, Trump ya yi gargadi ga rundunar soji ta Iran, wadda ke karkashin jagoran kasar, Ayatollah Ali Khamenei.
Ya yi kira ga sauran sojoji da ‘yan sandan kasar, yana mai cewa su ajiye makamansu su samu cikakkiyar kariya, ko kuma su fuskanci mutuwa tabbatacciya.

Source: Getty Images
Trump ya bukaci kifar da Khamenei
Trump ya bukaci fararen hular Iran su nemi mafaka saboda yiwuwar tsananin hare-haren bama-bamai, amma a lokaci guda ya karfafa musu gwiwa su kifar da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci wadda ke mulkin kasar tun shekarar 1979.
CBS News ta rahoto ya ce:
“Lokacin ‘yancinku ya kusa,”
“Idan mu ka kammala, ku karbe mulkin kasarku. Zai kasance a hannunku. Watakila wannan ce dama daya tilo da za ku samu.”
Shugaban ya ce ayyukan sojan Amurka a Iran na iya haifar da asarar rayukan Amurkawa saboda haka ya bukaci su nemi mafaka a wurare daban-daban.
Ga bayanin da Trump ya yi a kasa:
Isra'ila ta kai hari a kasar Iran
A wani labarin, kun ji cewa ma'aikatar tsaron Isra'ila ta sanar da kai hari wasu biranen Iran da safiyar ranar Asabar, 28 ga Janairun 2026.
Bayan harin, gwamnatin Isra'ila ta sanar da ayyana dokar ta baci a fadin kasar domin fargabar abin da zai biyo baya daga bangaren Iran.
Wasu daga cikin shugabannin Iran sun bayyana cewa lamarin zai jawo barkewar yakin da tsagaita wuta ba zai kasance a hannun Amurka ko Isra'ila ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

