Trump Ya Lallaba Ya Shiga Burkina Faso, Ya ba Shugaba Traore Miliyoyin Daloli
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake tunkarar wasu kasashen Afrika da tallafin kudi yayin da Rasha da China ke cigaba da kara karfi a nahiyar
- Rahotanni sun tabbatar da cewa Amurka ta kulla yarjejeniyar Dala miliyan 147 a Burkina Faso karkashin jagorancin Shugaba Ibrahim Traore
- Wasu kasashen Afrika sun nuna shakku wajen rattaba hannu kan yarjejeniya da Amurka, inda kasar Zimbabwe ta ki amincewa da ita gaba daya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Burkina Faso - Amurka ta sake komawa yankin Sahel ta fuskar dabarun siyasa ta hanyar yarjejeniyar lafiya ta Dala miliyan 147 a Burkina Faso
Yarjejeniya ta mayar da hankali kan ƙarfafa tsarin kiwon lafiya, sa ido kan cututtuka, da inganta samun kulawar lafiya a matakai daban-daban.

Source: Getty Images
Rahoton Africa Business Insider ya nuna cewa yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara fafatawa wajen samun tasiri a yankin Sahel, inda sauye-sauyen kawance da tsare-tsaren tsaro suka sauya yanayin siyasar yankin.
Tallafin gwamnatin Amurka ga Burkina Faso
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka za ta bayar da Dala miliyan 147 cikin shekaru biyar domin taimaka wa Burkina Faso wajen yaƙi da wasu cututtuka.
Rahoton Reuters ya ce cututtukan sun hada da HIV, zazzabin cizon sauro, da sauran cututtuka masu yaɗuwa, tare da inganta sa ido kan barkewar cututtuka da yadda ake magance su.
Abin da kasar Burkina Faso za ta yi
Burkina Faso kuma za ta zuba Dala miliyan 107 a tsarin kiwon lafiyarta, tare da ƙarin Dala miliyan 12 domin ƙarfafa lafiyar al’umma da faɗaɗa ƙarfin dakunan gwaje-gwaje.
Ta hanyar zurfafa hulɗa da Burkina Faso, Washington na nuna alamar dawo da tsarin diflomasiyya da ƙoƙarin sake tabbatar da kasancewarta a Sahel da manyan ƙasashe ke ƙoƙarin ƙara tasiri a ciki.
A daidai lokacin da gwamnatocin soji a yankin Sahel suka kori sojojin Faransa tare da ƙarfafa alaƙa da Rasha, Amurka na ƙoƙarin sake bayyana tasirinta ta hanyar diflomasiyya.
Kasashe sun nuna shakku kan Amurka
Duk da cewa Washington ta kulla wasu sababbin yarjejeniyoyin tallafin lafiya a faɗin Afirka, ba dukkan gwamnatoci ne suka rungumi tsarin ba tare da shakka ba.
Zimbabwe ta zama misali, inda ta janye gaba ɗaya, bayan ta dakatar da tattaunawa kan wata yarjejeniyar tallafin lafiya da Amurka ke goyon baya, wadda aka ce darajarta ta kai ɗaruruwan miliyoyin daloli.
Kasar ta nuna damuwa kan batun ‘yancin kai, musamman kan tanade-tanaden da suka shafi sarrafa bayanai da tsarin sa ido da ke cikin yarjejeniyar.

Source: Getty Images
Haka zalika, Zambia ta jinkirta rattaba hannu kan wata babbar yarjejeniyar lafiya da Amurka, inda jami’ai suka ce wasu sassan daftarin ba su dace da muradun ƙasar ba.
Donald Trump na son sulhu da Iran
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya yi magana game da Iran a wani dogon tattaunawa da ya yi a majalisar Amurka.
A bayanan da ya yi wa 'yan majalisar, Trump ya bayyana cewa ya fi son shawo kan Iran ta hanyar tattaunawa maimakon gwabza yaki.
Duk da haka, ya ce ba zai taba barin Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, inda ya ce ya gargadi Tehran kan haka tun a shekarar 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


