Bayan Barazanar Yaki, Trump Ya Ja da Baya game da Gwabzawa da Kasar Iran
- Yayin da Amurka ke ƙara shirye-shirye da tura sojoji Gabas ta Tsakiya a shirin yaki da Iran, Donald Trump ya yi maganar da ke nuna alamun ja da baya
- Shugaba Trump ya yi magana ne yayin wani jawabi da ya yi a majalisar dokokin Amurka, inda ya ce ba zai taba barin Iran ta mallaki makamin nukiliya ba
- Gwamnatin Amurka ta shafe lokaci tana barazanar kai hari Iran, inda kasar ta ce ba za ta yi wasa ba wajen mayar da martani kan sansanonin Washington
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Amurka na cigaba da aika sako ga Iran yayin da Tehran ke mayar da martani yayin da kasashen ke barazanar fuskantar juna a fagen daga.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana game da shirin yaki da ya ce zai fafata da Iran kan zargin mallakar makamai da kasar ta karyata.

Source: Getty Images
Rahoton Al-Jazeera ya bayyana cewa Trump ya yi maganar ne yayin da Amurka da Iran ke shirin zama a kasar Oman a makon da muke ciki.
Iran: Donald Trump ya nuna ja da baya
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya shaida wa Majalisar dokoki cewa ya fi son a warware sabanin da ke tsakanin Amurka da Tehran ta hanyar diflomasiyya.
Ya fadi haka ne yayin da yake gabatar da hujjarsa kan yiwuwar kai hare-hare kan Iran, wadda ya ce tana ƙoƙarin ƙera makamai masu linzami da za su iya kai hari kan Amurka.
A jawabin da ya gabatar a taron haɗin gwiwa na majalisar dattawa da majalisar wakilai a jawabinsa na shekara-shekara, Trump ya yi magana da kakkausar murya kan Iran.
“Mun shafe shi (Nukiliyar Iran) gaba ɗaya kuma suna son su farfado da shi. Kuma a wannan lokaci ma suna ci gaba da neman cika burinsu,”
In ji Trump, yayin da ya fara magana kan yiwuwar ɗaukar matakin soja kan Iran kusan mintuna 90 bayan fara dogon jawabin nasa.

Source: Getty Images
Rahoton Axios ya nuna cewa ya kara da cewa:
“Muna tattauna wa da su. Suna son su cimma yarjejeniya, amma har yanzu ba mu ji: ‘Ba za mu taɓa mallakar makamin nukiliya ba.’”
Trump ya ce “zaɓinsa” shi ne “a warware wannan matsala ta hanyar diflomasiyya, amma abu ɗaya tabbatacce ne:
"Ba zan taɓa bari babbar ƙasar da ke ɗaukar nauyin ta’addanci a duniya, wadda su ne ba tare da shakka ba, ta mallaki makamin nukiliya.
“Ba za a bar hakan ya faru ba,”
Trump ya ce ya gargadi kasar Iran
Trump ya ce bayan hare-haren da Amurka ta kai wuraren nukiliyar Iran a watan Yunin 2025, ya gargadi kasar kan mallakar makamai:
Ya ce:
“An gargaɗe su da kada su sake yunƙurin farfaɗo da shirinsu na makamai, musamman makaman nukiliya – amma duk da haka suna ci gaba.”
Sheikh Gumi ya caccaki kasar Amurka
A wani labarin, kun ji cewa babban malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki Amurka kan maganar Shari'a a Najeriya.
Wasu 'yan majalisar Amurka sun mika rahoto ga shugaba Donald Trump game da zargin kisan Kiristoci, inda suka nemi a soke Shari'a a kasar nan.
A martanin da ya yi, malamin ya bayyana cewa Shari'a hakkin 'yan Najeriya ne kuma ba abu ne da za a iya hakura da shi saboda Amurka ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


