Kwamitin Amurka Ya Gama Bincike, Shugaba Trump Zai Dauki Matakai Masu Tsauri kan Najeriya

Kwamitin Amurka Ya Gama Bincike, Shugaba Trump Zai Dauki Matakai Masu Tsauri kan Najeriya

  • Kwamitin Majalisar dokokin Amurka ya kammala bincike kan zargin kisan kiristoci a Najeriya, ya mika rahoto ga Shugaba Donald Trump
  • A rahoton bincike, an ba gwamnatin Amurka shawarar kakaba takunkumin tattalin arziki kan Najeriya domin tilasta mata daukar mataki
  • Haka zalika, rahoton ya bukaci Amurka ta dakatar da tallafin da take bai wa Najeriya har sai mahukunta sun kare rayukan kiristoci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Wani kwamitin Majalisar Dokokin Amurka ya ba da shawarar kakaba takunkumin tattalin arziki da wasu matakan ladabtarwa kan Najeriya.

Hakan na kunshe ne a rahoton da kwamitin ya mika wa shugaban Amurka, Donald Trump ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairu, 2026.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

An mika rahoton bincike ga Shugaba Trump

'Dan majalisa Riley Moore, wanda ya jagoranci binciken, ya tabbatar da mika rahoton abubuwan da suka gano ga Shugaba Donald Trump a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Amurka ta kawo shawara kan hukuncin wanda ya taba mutuncin Manzon Allah SAW a Najeriya

Rahoton ya ba da shawarar kakaba takunkumin tattalin arziki da wasu matakan ladabtarwa kan Najeriya bisa abin da ya bayyana a matsayin ci gaba muzgunawa kiristoci a Najeriya.

A cewar rahoton, kwamitin ya bukaci gwamnatin Amurka ta dakatar da tallafin kuɗi ga Najeriya har sai an ga gwamnati ta dauki matakai a aikace na dakile hare-haren da yan ta'adda ke kai wa kiristoci.

Matakan da aka nemi Amurka ta dauka

Sauran shawarwarin da kwamitin ya ba gwamnatin Amurka sun hada da:

1. Kakaba takunkumin tattalin arziki da hana biza ga mutanen da ake zargi da hannu ko goyon baya a tauye hakkin addini.

2. Kafa yarjejeniyar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya domin kare al’ummomin da ke cikin haɗari da kuma rusa hanyoyin ’yan ta’adda.

3. Ba da tallafin fasaha wajen magance tashin hankalin da ake dangantawa da wasu makiyaya Fulani masu ɗauke da makamai.

4. Soke dokokin Shari’a da na ɓatanci

Rahoton ya kuma ba da shawarar Amurka ta haɗa kai da ƙasashe kamar Faransa, Hungary da Birtaniya wajen tsarawa da daukar matakai kan Najeriya.

Kara karanta wannan

Babu wasa: Tinubu ya tara gwamnoni, ya gaya masu shirinsa don magance rashin tsaro

Yadda kwamitin Amurka ya yi bincike a Najeriya

Tawagar ’yan majalisar ta gudanar da taron sauraron ƙwararru, tattaunawa da shugabannin addini, da kuma ziyarce-ziyarce biyu zuwa Najeriya domin tattara bayanai.

A yayin ziyarar, sun kai ziyara sansanonin ’yan gudun hijira a Jihar Benue tare da ganawa da manyan jami’an gwamnati, ciki har da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu.

Moore ya ce yanzu kwamitin na da cikakken fahimta kan barazanar da Kiristoci ke fuskanta, yana mai cewa dole ne a ɗauki matakan hukunta masu laifi domin dakile ta'addancin masu tsattsauran ra’ayi.

Shugaba Trump da Tinubu
Shugaban Amurka, Donald Trump da takwaransa na Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Amurka za ta koro wasu 'yan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Amurka ta kara sunayen 'yan Najeriya 19 a cikin jerin wadanda za a koro gida saboda aikata wasu manyan laifuffuka da suka aikata.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Donald Trump ta riga ta sanar da shirin korar 'yan Najeriya 79 da sunayensu ke cikin wannan jerin a baya.

Bincike ya nuna cewa mutanen da aka saka a sabon jerin an kama su ne da laifuffuka daban-daban wadanda suka hada da fyade ga kananan yara, damfara, cin zarafi da sauransu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262