Amurka Ta Kawo Shawara kan Hukuncin Wanda Ya Taba Mutuncin Manzon Allah SAW a Najeriya
- Kwamitin 'yan Majalisar dokokin Amurka da ya gudanar da bincike kan zargin muzgunawa kiristoci a Najeriya ya mika rahotonsa
- 'Dan Majalisa Riley Moore ne ya jagoranci mika rahoton ga Shugaba Donald Trump a fadar While House ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairun 2026
- Daga cikin shawarwarin da kwamitin ya ba gwamnatin Amurka akwai soke amfani da dokokin shari'a da batanci a Najeriya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Kwamitin bincike na 'yan Majalisar Dokokin Amurka da aka kafa a kwanakin baya, ya ba da shawarar a soke dokokin Shari’a da na ɓatanci a Najeriya.
Kwamitin ya ayyana hakan a matsayin wani ɓangare na matakan da za su taimaka wajen magance muzgunawa Kiristoci da kuma matsalar tsaro da ke ƙara tsananta a ƙasar.

Source: Getty Images
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Riley M. Moore, ya tabbatar da mika rahoton binciken a shafinsa na manhajar X.
Kwamitin Amurka ya mika rahoto ga Trump
Moore tare da haɗin gwiwar mambobin Kwamitin Kasafin Kuɗi da na Harkokin Waje na Majalisar Wakilai, ne suka gabatar da rahoton a Fadar White House.
Rahoton ya biyo bayan matakin da Shugaba Donald Trump ya ɗauka a ranar 31 ga Oktoba, 2025, na sake sanya Najeriya a matsayin ƙasar da ke da ake da damuwa da ita kan take ’yancin addini (CPC).
A cewar Moore, Shugaba Trump ya umurce shi da Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Tom Cole, su jagoranci bincike kan muzgunawa kiristoci da kuma matsalolin tsaro a Najeriya.
Ya ce sun hada rahoton ne bayan ziyarar haɗin gwiwa ta ’yan majalisar Amurka na jam’iyyu daban-daban zuwa Najeriya, sauraron shaidu, tattaunawa da shugabannin addinai, da ganawa da ’yan gudun hijira (IDPs)
Moore ya kuma tabbatar da cewa sun zauna sun yi tattaunawa da manyan jami’an gwamnatin Najeriya.
Shawarar kwamitin Amurka kan dokar shari'a
Daga cikin shawarwarin da rahoton ya bayar akwai soke dokokin Shari’a da na ɓatanci, wanda ya kunshi hukuncin taba mutuncin Annabi Muhammad S.A.W.
Bayan ganawar a White House, Moore ya gode wa Shugaba Trump bisa sake ayyana Najeriya a matsayin CPC da kuma jajircewar gwamnatinsa wajen kare Kiristoci.
Ya ce ya jagoranci tawaga zuwa Najeriya inda suka ga irin wahalhalun da Kiristoci ke fuskanta, tare da tattaunawa da shugabannin addini da jami’an gwamnati.
“’Yan’uwanmu Kiristoci sun sha wahala na tsawon lokaci. Yanzu duniya na kallo, ina kira ga gwamnatin Najeriya ta yi amfani da wannan dama wajen ƙarfafa dangantakarta da Amurka, domin amfanin ƙasashen biyu," in ji Moore.
Ya ƙara da cewa dole ne a ɗauki matakai masu ƙarfi domin magance matsalolin tsaro da kawo ƙarshen kisan Kiristoci a Najeriya, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.

Source: Getty Images
Jami'in gwamnatin Amurka zai shigo Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa babban jami'i a gwamnatin Donald Trump , Jonathan Burke, wanda shi ne Mataimakin sakataren ma’aikatar kuɗi ta Amurka zai shigo Najeriya.
Mista Burke zai gudanar da wata ziyara daga Litinin 23 zuwa Talata 24 ga watan Fabrairu, 2026 domin ƙara haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya kan tsaro.
Wannan na zuwa ne bayan sojojin Amurka kimanin 100 sun iso Najeriya domin taimakawa dakarun soji wajen samun bayan sirri da horo da nufin kawo karshen ta'addanci.
Asali: Legit.ng


