'Rasha Ta Kaddamar da Yakin Duniya na 3,' Shugaban Ukraine Zelensky
- Yakin Ukraine da Rasha na cigaba da daukar sabon salo bayan shugaba Vladimir Putun ya cigaba da luguden wuta da mamaye yankuna
- Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya yi zargin cewa shugaba Putin ya riga ya kaddamar da yakin duniya na 3 a kan kasarsa
- Volodymyr Zelensky ya bayyana matakan da ya kamata kasashen duniya su dauka wajen hana Putin cigaba da mamaye yankunan Ukraine
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ukraine - Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, na ci gaba da aika saƙo ga gwamnatin Rasha, karkashin Vladimir Putin game da yaki da suke yi.
A sabon sakon da Volodymyr Zelensky ya aika wa duniya da kasar Rasha, ya bayyana cewa ba zai mika wuya ba duk da matsin lambar Putin.

Source: Getty Images
Lokacin da Volodymyr Zelensky ya tattauna da BBC a hedikwatar gwamnati da ke Kyiv, ya ce maimakon mika wuya, Ukraine za ta kawo ƙarshen yaƙin cikin nasara.
Ya nuna rashin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaba Vladimir Putin ke nema, wadda ta haɗa da janyewa daga muhimman yankuna da Rasha ta kasa ƙwacewa duk da sadaukar da dubban sojojinta.
Batun fara yakin duniya na 3
Zelensky ya ce shugaba Putin ya riga ya fara yaƙin duniya na uku, inda ya ce mafita guda ita ce matsin lambar soja da tattalin arziki mai tsanani domin tilasta masa ja da baya.
Moscow Times ta rahoto ya ce:
“Na yi imanin cewa Putin ya riga ya fara shi (Yakin duniya na uku).
"Tambayar ita ce yankuna nawa zai iya kwace wa da kuma yadda za a dakatar da shi... Rasha na son tilasta wa duniya wata sabuwar hanyar rayuwa tare da canza rayuwar da mutane suka zaɓa wa kansu.”

Kara karanta wannan
Trump ya durawa alkalai ashar bayan hana shi daukar mataki kan Najeriya da kasashe
Bukatar Shugaba Putin a Ukraine
Da aka tambaye Volodymyr Zelensky kan me zai hana ya amince da buƙatar Rasha ta miƙa kashi 20 na yankin gabashin Donetsk da har yanzu take riƙe da shi, ya ce hakan ba zai yi wu ba.
Gabashin Donetsk ya kunshi jerin garuruwa da Ukraine ke kira ‘garuruwan kariya’ inda Putin ke bukata tare da ƙarin yankuna a kudancin Kherson da Zaporizhzhia.

Source: Getty Images
Volodymyr Zelensky ya ce:
“Ina kallon lamarin ta wata fuska dabam. Ina ganin hakan a matsayin raunana matsayarmu da rashin girmama dubban mutane da ɗaruruwan al’ummarmu da ke zaune a can.
"Haka nake ganinsa. Kuma na tabbata cewa janyewa daga wajen zai raba kan al’ummarmu.”
Ukraine ta kashe 'yan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin kasar Ukraine ta saki sunayen wasu 'yan Najeriya da ta ce ta kashe a lokacin da suke taya sojojin Rasha yaki a wani yankin kasar ta.

Kara karanta wannan
Kotun Koli ta dakile yunkurin Trump, ta yi watsi da dokokin haraji da za su shafi duniya
Har ila yau, sojojin Ukraine sun yi zargin cewa ba a ba 'yan Najeriyan cikakken horon soji ba kafin a tura su fagen fama su fafata da dakarunta.
Ukraine ta fitar da wasu takardu da ke nuna daya daga cikin 'yan Najeriyan da ta ce ta kashe ya bar mata da iyalansa a gida kafin shiga soja a Rasha.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
