Amurka Ta Saki Sunayen Ƴan Najeriya 19 da Za Ta Koro Gida, An Fadi Laifuffukansu
- Gwamnatin Amurka ta kara sunayen 'yan Najeriya 19 a cikin jerin wadanda za a koro gida saboda aikata manyan laifuffuka
- Ma'aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ta bayyana cewa wadanda aka kama sun hada da masu damfara da masu safarar kwayoyi
- Jimillar 'yan Najeriya da sunayensu ke cikin jerin ya kai 113, lamarin da ke kara nuna girman dokokin gwamnatin Donald Trump
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Amurka - Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Amurka ta kara sunayen wasu 'yan Najeriya 19 a cikin jerin sunayen masu aikata laifuffuka mafi muni a kasar.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Donald Trump ta riga ta sanar da shirin korar 'yan Najeriya 79 da sunayensu ke cikin wannan jerin a baya.

Source: Getty Images
Za a koro 'yan Najeriya 113 gida
Tare da wadannan sababbin mutane 19 da ma'aikatar tsaron cikin gida ta Amurka (DHS) ta wallafa a ranar Lahadi, jimillar 'yan Najeriya da ake shirin kora ya kai mutane 113 yanzu, in ji rahoton Punch.
Bincike ya nuna cewa mutanen da aka saka a sabon jerin an kama su ne da laifuffuka daban-daban wadanda suka hada da fyade ga kananan yara, damfara, cin zarafi, safarar miyagun kwayoyi, da kuma halatta kudaden haram.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa jami'an hukumar ICE ne suka cafke wadannan mutane kuma za a mayar da su kasarsu da zarar an kammala cike ka'idojin shige da fice.
Sanarwar DHS ta bayyana:
"Karkashin jagorancin sakatariya Kristi Noem, muna cika alkawarin Donald Trump na gudanar da korar bakin da ba su da takardu — tare da farawa daga manyan masu aikata laifuffuka."
Kasashen Afirka da ke cikin jerin
Rahoton BBC ya nuna Najeriya ce ke kan gaba a jerin kasashen Afirka da mutanensu ke fuskantar kora, inda take biye da wasu kasashe kamar haka:
- Najeriya: Mutane 79 (kafin karin na yau) dake fuskantar kora kan damfara, sata, fyade, da safarar kwayoyi.
- Kenya: Mutane 28 kan laifuffukan kwayoyi, cin zarafi, da sata.
- Ghana: Mutane 18 kan kisan kai, cin zarafi, damfara, da halatta kudaden haram.
- Afirka Ta Kudu: Mutane 6 kan laifuffukan cin zarafi da fashi.
- Burkina Faso: Mutane 5 kan damfarar wasiku da lalata da kananan yara.

Source: Getty Images
Sunayen 'yan Najeriya 19 da aka kara
Daga cikin sunayen 'yan Najeriya 19 da aka kara yanzu akwai Adeolu Solabu, Oladayo Agboola, Chinonso Ochie, Oluchi Jennifer Chimdimma Chime, Samuel Omorodion, Sunday Adediora, Sunday Kunkushi da Mkpouto Etukudoh.
Sauran su ne; Marcus Unigwe, Kehinde James, Blessing Uchanma, Victor Adebisi, Richard Ugbah, Olaniyi Ojikutu, Oluwamuyiwa Olawoye, Okechukwu Amadi, Femi Jolayemi, Anthony Asanya, Izuchukwu Okoye da Ebele Agbasiele.
Wannan matakin na daya daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Trump na kora baki masu yawa wadanda suke aikata laifuffka a kasar Amurka, in ji rahoton The Sun.
Amurka ta koro 'yan Najeriya 2,330
A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar ICE ta kori ‘yan Najeriya 2,330 daga kasar Amurka a tsakanin shekarar 2014 zuwa farkon 2025.
Kididdigar ICE ta nuna cewa an samu raguwar adadin 'yan Najeriya da aka kora daga Amurka daga 281 zuwa 138 a shekaru 11.
Najeriya ce ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka yawan mutanen da aka kora daga Amurka a cikin shekarun nan da suka gabata.
Asali: Legit.ng

