Trump Ya Durawa Alkalai Ashar bayan Hana Shi Daukar Mataki kan Najeriya da Kasashe
- Donald Trump ya kaddamar da sabon harajin kashi 10 bayan kotun kolin Amurka ta yi watsi da harajin shigo da kaya da ya sa wa kasashe
- A martanin da ya yi a wani taro a fadar White House, Trump zagi alkalan kotun ya nuna cewa ba su da jarumtar daukar matakai masu tsauri
- Tun a shekarar 2025 Donald Trump ya kakaba wa Najeriya da wasu kasashen duniya haraji, lamarin da ya tayar da kura a fadin Amurka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Matakan da alkalan kotun Amurka suka dauka na hana shugaba Donald Trump kakabawa Najeriya da wasu kasashe haraji ya tayar da kura.
Shugaban Amurkan wanda ya dawo ofis a 2025 ya nuna rashin jin dadinsa game da matakin da alkalan suka dauka, yana cewa ba su yi abin da ya kamata ba.

Kara karanta wannan
Kotun Koli ta dakile yunkurin Trump, ta yi watsi da dokokin haraji da za su shafi duniya

Source: Getty Images
Rahoton New York Times ya nuna cewa Donald Trump ya fusata, inda ya siffanta matakin da abin kunya da kuma alkalan a matsayin wawaye.
Donald Trump ya zagi alkalan Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya sabon harajin10% a duniya domin maye gurbin waɗanda kotun kolin kasar ta soke.
BBC ta rahoto cewa Trump ya kira hukuncin da “abin takaici”, tare da sukar alƙalan da suka yi watsi da manufofinsa na kasuwanci a matsayin “wawaye”.
Shugaban ya bayyana sabon shirin ne jim kaɗan bayan da alƙalan kotun suka soke harajin da ya kakabawa kasashe a 2025.
Yadda Kotun koli ta soke harajin Trump
Rahotanni sun nuna cewa a hukuncin da aka yanke da rinjayen ƙuri’u 6-3, kotun ta ce shugaban ya wuce iyakar ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi.
Hukuncin ya zama babbar nasara ga kamfanoni da jihohin Amurka da suka kalubalanci harajin, wanda ya buɗe ƙofa ga yiwuwar mayar da biliyoyin Daloli na kuɗin haraji.
Da yake jawabi daga Fadar White House a ranar Juma’a, Trump ya nuna cewa ba za a mayar da kuɗin harajin ba tare da shari’a ba, yana cewa yana sa ran lamarin zai ɗauki shekaru a kotu.

Source: Getty Images
Ya kuma ce zai koma ga wasu dokoki domin ci gaba da aiwatar da harajinsa, wanda ya ce yana ƙarfafa zuba jari da masana’antu a Amurka.
“Muna da wasu hanyoyi – hanyoyi masu kyau, kuma hakan zai ƙara mana ƙarfi,”
- In ji Trump
Najeriya da kasashen da harajin ya shafa
Shari’ar ta mayar da hankali ne kan harajin shigo da kaya da Trump ya ƙaddamar a bara kan kayayyaki daga kusan kowace ƙasa a duniya.
Harajin ya fara ne kan kayayyaki daga Mexico, Canada da China, kafin daga bisani ya faɗaɗa sosai zuwa ga ƙasashe da dama abokan hulɗar kasuwanci ciki har da Najeriya.
Trump ya yi magana da Birtaniya
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana da Firaministan Birtaniya game da shirin kai hari Iran.
Wasu rahotanni sun nuna cewa Donald Trump ya nemi amfani da wani babban sansanin sojin Birtaniya domin kai hari Iran ta sama.
Sai dai wasu jami'an gwamnatin Birtaniya sun nuna an ki amincewa da bukatar, suna cewa hakan ya saba dokokin kasa da kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
