‘Yana Neman Ruguza Kasa’: Gwamnati Ta Haramta Amfani da Dukan Kafofin Sadarwa

‘Yana Neman Ruguza Kasa’: Gwamnati Ta Haramta Amfani da Dukan Kafofin Sadarwa

  • Alamu suna kara tabbatar da cewa yadda ake amfani da kafafen sadarwa a kasashe da dama na duniya ya fara zama barazana
  • Hukumar sadarwa ta kasar Gabon ta dauki gagarumin mataki kan shafukan sada zumunta domin tabbatar da tsaron kasar baki daya
  • Duk da haka, ta jaddada cewa ‘yancin fadin albarkacin baki har yanzu hakki ne a Gabon wanda ba za a yi wasa da shi ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Libreville, Gabon - Hukumar Kula da Sadarwa ta Gabon ta dauki gagarumin mataki da ya shafi amfani da shafukan sadarwa a kasar karkashin Shugaba Brice Olugui Nguema.

Hukumar ta sanar da dakatar da dukkan shafukan sada zumunta “har sai baba-ta-gani”, tana mai zargin cewa wasu sakonni na haddasa rikici da rarrabuwar kawuna a cikin al’umma.

Gabon ta haramta amfani da kafofin sadarwa
Shugaban kasar Gabon, Brice Oligui Nguema da ya hana amfani da kafofin sadarwa. Hoto: Ludovic MARIN / AFP via Getty Images.
Source: Getty Images

Dalilin haramta kafofin sadarwa a Gabon

Kara karanta wannan

Babban albishirin Dangote ga 'yan Najeriya kan farashin Naira a 2026

Mai magana da yawun hukumar, Jean-Claude Mendome, ya bayyana haka a wata sanarwa ta talabijin a jiya Talata 17 ga watan Fabrairun 2026, cewar BBC.

Mendome ya tabbatar da cewa an kafa dokar dakatarwar nan take domin kare zaman lafiya da martabar kasa.

Hukumar ta ce wasu sakonni marasa dacewa, na batanci, kiyayya da zagi suna tauye mutuncin dan Adam, lalata tarbiyyar jama’a da kuma barazana ga tsaron kasa.

Ta kuma ambaci yada labaran karya, cin zarafi ta yanar gizo da fitar da bayanan sirri ba tare da izini ba a matsayin manyan dalilan daukar wannan mataki.

Gabon ta fadi dalilin haramta amfani da kafofin sadarwa
Shugaban kasar Gabon mai mulki a karkashin jam'iyyar Democratic Union of Builders. Hoto: @VaticanNews.
Source: Twitter

Gabon: Matsalolin da kafofin sadarwa ke jawowa

A cewar hukumar, irin wadannan ayyuka na iya haddasa rikici a cikin al’umma, su raunana cibiyoyin gwamnati tare da jefa hadin kan kasa cikin hadari.

Sai dai hukumar ba ta fayyace sunayen shafukan sada zumuntar da dakatarwar ta shafa ba, amma ta ce matakin ya shafi dandalin sada zumunta gaba daya.

Duk da haka, ta jaddada cewa ‘yancin fadin albarkacin baki, ciki har da yin sharhi da suka, hakki ne na asali da kundin tsarin mulkin kasar Gabon ya tanada.

Kara karanta wannan

'Ina EFCC?': Watsa wa Rarara kudi a gaban Tinubu ya tayar da kura, an gargadi 'yar APC

Matakin ya zo ne kasa da shekara guda bayan zaben Shugaban kasa Brice Oligui Nguema, wanda yanzu ke fuskantar tashin hankali daga ma’aikata da malamai.

Tun daga watan Disambar 2025, malamai sun fara yajin aiki kan albashi da yanayin aiki, lamarin da ya bazu zuwa bangarorin lafiya, manyan makarantu da kafafen yada labarai na gwamnati.

WhatsApp da Facebook da Tiktok ne manhajojin da aka fi amfani dasu a Gabon, to sai dai gwamnatin ta ce babu ranar da za a dawo amfani da shi, cewar Channels TV.

Pantami ya fadi illar kafofin sadarwa

Kun ji cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya yi magana kan hana wa’azi kai tsaye da wasu ke ganin hakan zai kawo daidaito a cikin al'umma.

Malamin ya ce kungiyoyi kamar JNI, Izalah, Tijjaniyya da Kadiriyya ya dace su jagoranci tsara dokoki da kula da masu wa’azi.

Pantami ya kuma gargadi malamai su guji sukar junansu a bainar jama’a, yana cewa kafofin sadarwa sun haifar da yawaitar jayayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.