Rikici Ya Barke a Zauren Majalisa, An Yi Yunkurin Hana Rantsar da Sabon Minista

Rikici Ya Barke a Zauren Majalisa, An Yi Yunkurin Hana Rantsar da Sabon Minista

  • Shugaba Tayyip Erdogan ya nada Akin Gurlek a matsayin ministan shari'a na Turkiyya duk da kakkausan sukan da jam'iyyar adawa take yi
  • Rikici ya barke a majalisar dokokin Turkiyya yayin rantsar da sabon ministan inda aka ga sanatoci suna dambe a kokarin hana rantsuwar
  • Wani bidiyo ya nuna yadda ‘yan majalisar CHP suka yi yunƙurin toshe Gurlek, inda aka ga ana ture juna da kai naushi tsakanin sanatoci

Istanbul - Shugaban ƙasar Turkiyya, Tayyip Erdogan, ya naɗa babban mai shigar da ƙara na Istanbul, Akin Gurlek, a matsayin sabon ministan shari’a, wanda hakan ya haddasa kakkausan suka.

Gurlek ne mutumin da ya jagoranci kaddamar da bincike da kama mambobin babbar jam’iyyar adawa ta CHP tun bayan naɗa shi a shekarar 2024.

An ba hammata iska a majalisar Turkiyya a wajen nada sabon minista.
Shugaban Turkiyya Tayyip Erdogan yana jawabi a gaban majalisar kasa. Hoto: Ismail Aslandag/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Tabon da ke jikin sabon ministan Turkiyya

Wannan naɗi ya harzuka jam’iyyar adawa, inda suke ganin matakin a matsayin wani farmaki ne ga tsarin dimokuradiyya da kuma bin doka da oda a ƙasar, in ji rahoton Reuters.

Kara karanta wannan

Fulani Makiyaya sun fara buga wa da Amurka kan saka takunkumi

Akin Gurlek ne ya jagoranci binciken da ya kai ga kama Ekrem Imamoglu, magajin garin Istanbul kuma babban abokin hamayyar Erdogan, wanda ke garkame tun watan Maris na 2025.

A cikin wani kundin tuhuma mai shafuka 4,000 da ya gabatar a watan Nuwamban da ya gabata, Gurlek ya buƙaci a ɗaure Imamoglu na tsawon shekaru sama da 2,000.

Wannan tuhuma, wadda ta shafi zargin jagorantar gungun masu cin hanci da rashawa, ta janyo gagarumar zanga-zanga a titunan Turkiyya wadda ba a taɓa ganin irinta ba cikin shekaru 10.

Ana sa ran za a gudanar da zaman sauraron ƙarar na farko a watan gobe, inda ake tuhumar ɗaruruwan mutane da ke da alaƙa da hukumar birnin Istanbul.

Hargitsi da kokowa a majalisar Turkiyya

An samu barkewar hayaniya da dambe a majalisar dokokin Turkiyya gabanin rantsar da Gurlek, yayin da ‘yan majalisar adawa suka nuna rashin amincewarsu da nadinsa.

Kamar yadda hotunan talabijin suka nuna, ‘yan majalisar jam’iyyar CHP sun yi yunƙurin toshe Gurlek, inda aka ga ana ture juna da kai naushi tsakanin sanatoci.

‘Yan majalisar jam’iyya mai mulki ta AK sun yi kokarin kafa kariya a kusa da Gurlek domin ba shi damar karanta rantsuwar kama aiki a cikin wannan yanayi na rudani.

Kara karanta wannan

Hafsun sojoji ya fadi abin da ke jiran wadanda suka kitsa juyin mulki

"Wannan naɗi wani farmaki ne ga doka," in ji 'yan majalisar adawa yayin da suke ihu da sokar matakin da shugaba Erdogan ya ɗauka.

Sabon ministan shari'a da Shugaba Tayyip Erdogan ya nada ya jawo rikici a majalisar Turkiyya.
Shugaban Turkiyya, Tayyip Erdogan yana gaisawa da 'yan jam'iyyarsa ta AKP a majalisar kasar. Hoto: ADEM ALTAN / Getty Images
Source: Getty Images

Sauye-sauye na farko a majalisar ministoci

Wannan shi ne garambawul na farko da gwamnatin Erdogan ya yi tun bayan zaɓen tsakiyar shekarar 2023, inda Gurlek ya maye gurbin Yilmaz Tunc a matsayin Ministan Shari'a.

Haka kuma, Erdogan ya naɗa gwamnan lardin Erzurum, Mustafa Ciftci, a matsayin Ministan Cikin Gida, inda ya maye gurbin Ali Yerlikaya, in ji rahoton AP News.

Kodayake gwamnati ba ta bayar da takamaiman dalilin yin wannan garambawul ba, masu lura da al'amura suna ganin hakan a matsayin ƙarfafa iko ne ga shugaban ƙasar.

Gwamnati ta musanta zargin cewa tana amfani da shari'a wajen murƙushe adawa, inda take ikirarin cewa fannin shari'a na gudanar da ayyukansa ne ba tare da tsangama ba.

Kalli bidiyon rigimar da ta barke a majalisar, wanda @visionergeo ya wallafa a shafinsa na X:

An samu hargitsi a majalisar Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, rikici ya barke tsakanin Sanata Rufai Sani Hanga da Sanata Onyekachi Nwaebonyi yayin da ake gudanar da zaman kare kasafin kudi.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun riƙewa minista wuta a kan 'bacewar' kayan Gwamnatin Tarayya

Takaddamar ta fara ne lokacin da Sanata Hanga ya katse Nwaebonyi yayin da yake yaba wa ministan ayyuka, David Umahi tare da kira ga abokan aikinsa su yi hakan.

Wannan sabani ya dakatar da zaman na dan lokaci kafin aka samu daidaito aka ci gaba da tattaunawa kan abubuwan da aka sanya a gaba a zaman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com