Abu Ya Girma: Sarkin Saudiyya Ya Umarci Fita Sallar Rokon Ruwa a Masallatai 12,000

Abu Ya Girma: Sarkin Saudiyya Ya Umarci Fita Sallar Rokon Ruwa a Masallatai 12,000

  • Sarkin Saudiyya, Sarki Salman bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin gudanar da sallar roƙon ruwa a duk faɗin ƙasar
  • Sanarwar fadar Sarki ta ce za a gudanar da sallar a masallatai sama da 12,000 ciki har da Masallacin Harami da Masallacin Annabi
  • Sarki Salman ya bukaci jama’a su tuba, su yawaita istigfari, tare da dogaro ga rahamar Allah domin shi kaɗai ke saukar da ruwan sama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Riyadh, Saudi Arabia - Mai kula da Masallatai Biyu Masu Alfarma, Sarki Salman bin Abdulaziz na kasar Saudiyya, ya bayar da umarnin gudanar da Sallar rokon ruwa.

Basaraken ya ce za a yi sallar a duk faɗin masarautar ranar Alhamis 12 ga Fabrairun 2026 da muke ciki inda ya roki al'umma su tuba tare da komawa ga Allah.

Kara karanta wannan

Shekarau: Yayan tsohon gwamnan Kano ya riga mu gidan gaskiya bayan jinya

Sarkin Saudiyya ya umarci fita sallar rokon ruwa
Sarkin Saudiyya, Mai Martaba Salman bin Abdulaziz. Hoto: Mikhail Svetlov.
Source: Getty Images

Ruwan sama: Sarkin Saudiyya ya ba da umarni

Hakan na cikin wata sanarwa da Legit Hausa ta samu wanda shafin Inside The Haramain ya wallafa a X a jiya Talata 10 ga watan Fabrairun 2026.

Bisa ga umarnin da aka fitar daga fadar Sarki, an bukaci al’umma su koma ga Allah cikin ƙanƙan da kai, su nemi gafara tare da shirya tarukan addu’ar neman ruwan sama.

Sanarwar hukuma ta bayyana cewa za a gudanar da Sallar a masallatai sama da 12,000 a faɗin Saudiyya, ciki har da Masallacin Harami da Masallacin Annabi

Limamai za su jagoranci addu’o’i na musamman domin neman saukar ruwan sama, neman gafarar zunubai da kuma alherin al’ummar Musulmi gaba ɗaya.

Sanarwar ta ce:

"Mai Kula da Masallatan Harami Biyu Masu Tsarki, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, ya yi kira da a gudanar da sallar neman ruwa a fadin Masarautar Saudiyya a ranar Alhamis, 24 ga Sha’aban 1447 (12 ga Fabrairu, 2025)."

Kara karanta wannan

Sanata ya shawarci Musulmi kan yadda za su kalubalanci malamai

Za a gudanar da sallar rokon ruwa a masallatai 12,000 a Saudiyya
Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz a taro. Hoto: Inside The Haramain.
Source: Facebook

Sarki ya ja hankalin Musulmi kan tuba

Sarki Salman ya jaddada muhimmancin tuba da yawaita neman gafara a rayuwar Musulmi, yana mai cewa a dogara da rahamar Allah domin shi ne mai saukar da ruwa.

Ya ƙara da cewa Allah ne kaɗai ke ba ƙasa rai ta hanyar ruwan sama, don haka ya kamata jama’a su ƙarfafa imaninsu da fatan samun rahama.

An kammala shirye-shiryen tarukan sallar rokon ruwa a duk faɗin masarautar, inda ake sa ran miliyoyin jama’a za su halarta domin yin addu’a.

Ana tsammanin taron zai kasance cikin tsari a masallatai daban-daban, yayin da Musulmai za su roƙi Allah da zuciya ɗaya domin albarkar ruwan sama.

Giya: Saudiyya ta yi rangwame ga attajirai

Mun ba ku labari a baya cewa kasar Saudiyya ta fara bai wa attajiran baki da ba Musulmi ba damar sayen giya a Riyadh bayan haramci na tsawon shekaru 73.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Sheikh Pakistan ya fadi dalilin murabus daga shugabancin NAHCON

Sabon tsarin ya shafi masu 'Premium Residency' ko wadanda ke samun albashi mai tsoka, yayin da baki masu yawon bude ido ba su cikin tsarin.

Masana na ganin matakin na daga cikin shirye-shiryen 'Vision 2030' domin jawo jari, kwararru da masu yawon bude ido a kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.