Mamaye Falasdinu: Trump Ya Juyawa Isra'ila Baya, Ya Bi Ra'ayin Kasashen Musulmi
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana adawarsa ga shirin Isra’ila na kara mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan da Falasdinawa ke zaune a ciki
- Wani jami’in Fadar White House ya ce zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yammacin Kogin Jordan na da muhimmanci wajen kawo zaman lafiya
- Kasashen Musulmi da dama, majalisar dinkin duniya da wasu kasashen Turai sun yi kakkausar suka kan matakan mamaya da Isra'ila ke dauka a yankin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Shugaban Amurka, Donald Trump ya nuna rashin amincewa da shirin Isra’ila na kara mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan da Falasdinawa ke rayuwa.
Bayanin ya fito ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke nuna fushi kan lamarin, bayan ministocin kudi da tsaron Isra’ila sun sanar da sababbin matakai da ke kara tsawaita mamayar Isra’ila a yankunan Falasdinu.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta rahoto cewa matakan dai sun hada da saukaka wa ‘yan Isra’ila hanyoyin mallakar filaye domin gina sababbin wuraren zama.
Donald Trump ya takawa Isra'ila burki
Yayin nuna adawa da matakan da Netanyahu ke dauka na mamaye yankunan Falasdinawa, wani jami’in White House ya ce Trump na ganin cewa kwanciyar hankali a Yammacin Kogin Jordan na taimakawa wajen kare Isra’ila.
A cewarsa, duk wani mataki da zai kara tayar da hankali ko dagula al’amura a yankin na iya jefa shirin samar zaman lafiya cikin barazana.
Reuters ta wallafa cewa furucin White House ya nuna bambanci tsakanin matsayin Amurka da matakan da Isra’ila ke dauka a halin yanzu.
Martanin wasu manyan kasashen Musulmi
Kasashe takwas da yawancinsu Musulmi sun fitar da sanarwa guda, suna sukar abin da suka kira “haramtattun matakan Isra’ila” da nufin kakaba ikon Isra’ila ba bisa ka’ida ba a yankunan Falasdinu.
Kasashen da suka hada da Masar, Indonesiya, Jordan, Pakistan, Qatar, Saudiyya, Turkiyya da UAE sun ce matakan na kara tabbatar da gina wuraren zama.
Sun kara da cewa hakan na hanzarta kokarin mamaye yankin ba bisa ka’ida ba, tare da tilasta wa Falasdinawa barin muhallansu.
Mece ce matsayar Majalisar dinkin duniya?
Shugaban majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, ya bayyana cewa matakan Isra’ila na matukar tayar da hankali kuma suna lalata yiwuwar samar da kasar Falasdinu.
Mai magana da yawunsa, Stephane Dujarric, ya ce wadannan matakai ba za su kai ga mafita a duniya ba kuma suna kara toshe hanyar burin Falasdinawa na mallakar kasa.

Source: Getty Images
Kasashen Birtaniya da Sifaniya ma sun yi Allah-wadai da matakan, inda gwamnatin Birtaniya ta bukaci Isra’ila da ta janye shawarar nan take.
Sojojin kasar Amurka sun dura Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa wata tawagar sojojin Amurka ta musamman ta gana da shugaban Najeriya, Bola Tinubu a fadar Aso Rock Villa.
Duk da cewa ba a bayyana muhimman abubuwan da suka tattauna ba, masu sharhi na ganin hakan na da alaka da lamuran tsaron kasar.
Manyan jami'an Najeriya da suka hada da Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu sun halarci zaman da aka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

