Shugaba Trump Ya Hango Abin da zai Sanya Ya Shiga Aljanna

Shugaba Trump Ya Hango Abin da zai Sanya Ya Shiga Aljanna

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sake yin tsokaci kan batun damar samun shiga aljanna bayan an bar duniya
  • Donald Trump ya bayyana cewa yana ganin yana da damar samun shiga aljanna saboda wasu abubuwan da ya yi
  • Shugaban kasar na Amurka, ya kuma bayyana cewa shugabannin da suka gabace ba su mayar da hankali kan addini ba

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan batun shiga Aljanna.

A baya, Shugaba Trump ya taɓa nuna shakku ko zai samu shiga Aljanna, amma a 'yan kwanakin ya nuna cewa yana ganin zai iya samun dama.

Shugaba Donald Trump ya yi magana kan shiga aljanna
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald Trump
Source: Facebook

Jaridar USA Today ta ce Donald Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron addu'o'in safe na kasa karo na 74 a ranar 5 ga Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An ba Shugaba Tinubu mafita kan yadda zai yi da Kashim Shettima

Me Trump ya ce kan shiga aljanna

Shugaba Trump ya ce yana ganin zai iya samun damar shiga aljanna domin ya yi abubuwa masu kyau ga mutane nagari.

“Ina ganin da gaske zan iya shiga. Ba ina cewa ni cikakken mutumin da ya cancanta ba ne, amma na yi abubuwa masu kyau kwarai ga mutane nagari.”

- Shugaba Donald Trump

A cikin jawabi mai tsawon mintuna 77 a otal ɗin Washington Hilton, Trump ya yi ikirarin cewa ya yi wa addini hidima fiye da duk wani shugaban Amurka, yana mai cewa shugabannin da suka gabace shi sun yi watsi da addini.

Trump ya yi magana kan addini

Hakazalika, a yayin taron wanda ya kasance ba na siyasa ba, Trump ya ce ganin wani mutum mai addini zai zabi dan jam'iyyar Democrat ba, tashar NDTV ta kawo labarin.

"Ban san yadda mai addini zai zaɓi ɗan jam’iyyar Democrat ba."

- Shugaba Donald Trump

Trump ya ce ya dawo da addini da Kiristanci tsakiyar siyasa da al’adun Amurka, yana ambaton kokarinsa na goyon bayan addu’a a makarantu, manufofi da suka shafi masu sauya jinsi, da kuma kafa ofishin addini a Fadar White House, da sauransu.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yadda 'yan ta'adda suka kira Sallah, suka kashe duk wanda ya zo Masallaci

Ya kuma sanar da shirin shirya wani babban taro a National Mall a ranar 17 ga Mayu domin “sake mika lamuran Amurka ga Allah a matsayin kasa ɗaya karkashin Allah.”

Shugaba Trump ya yi magana kan shiga aljanna
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: Donald Trump
Source: Facebook

Trump ya ce addini na farfadowa a Amurka

Shugaba Trump ya kara da cewa akwai alamun da ke nuna cewa addini na dawowa da ƙarfi a kasar Amurka.

“Wasu manyan ‘yan siyasa ma sun ki faɗin kalmar ‘Allah’. Ba sa son su ambace ta. Ni kuwa ina faɗinta."
"Addini yana dawowa sosai. Cocinku suna cika. Ba haka yake ba shekaru biyu da suka wuce."

- Donald Trump

Remi Tinubu ta yi mamakin girmamawar Trump

A wani labarin kuma, kun ji cewa uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu, ta yi mamakin girmamawar da Shugaba Donald Trump ya yi mata.

Oluremi Tinubu ta bayyana cewa ta yi matukar mamaki da irin karramawar da shugaban n kasar Amurka, ya yi mata.

Uwargidan ta shugaban kasar Najeriya ta ce ba ta yi tsammanin samun irin karramawar da Shugaba Donald Trump ya yi mata ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng