Barazanar Yaki: Trump Ya Bayyana Yadda Tattaunawar Amurka da Iran ta Kasance

Barazanar Yaki: Trump Ya Bayyana Yadda Tattaunawar Amurka da Iran ta Kasance

  • An fara zaman tattaunawa tsakanin kasar Iran da Amurka domin tattake waje kan abubuwan da kasashen biyu suke takaddama a kai
  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan yadda tattaunawar ta kasance wadda aka gudanar a kasar Oman
  • Donald Trump ya bayyana cewa kasashen biyu za kuma su sake hawa kan teburin tattaunawa a mako mai zuwa

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan tattaunawar da kasarsa ta fara da Iran.

Donald Trump ya ce Washington ta yi “tattaunawa mai kyau” da Iran bayan ɓangarorin biyu sun gudanar da tattaunawa a kasar Oman, inda suka yi alƙawarin sake zama zagaye na gaba a mako mai zuwa.

Amurka da Iran sun tattauna a Oman
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da jagoran juyin juya halin Iran, Ayatollah Ali Khamenei Hoto: @RealDonaldTrump, @khamenei
Source: Twitter

Tashar Aljazeera ta ce Trump ya bayyana hakan a cikin jirgin Air Force One a kan hanyarsa zuwa Mar-a-Lago a jihar Florida.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan ta'adda suka rubuta wa Sarki wasiƙu kan shirin hari kafin hallaka Musulmai a Kwara

Iran ta tattauna da Amurka

A ɓangarenta, Iran ta ce tana sa ran ci gaba da tattaunawa da Amurka, tana mai yabawa abin da ta kira “kyakkyawan yanayi” da aka samu a ranar tattaunawar da aka yi a ƙasar Oman.

Yayin da rundunar sojojin ruwan Amurka, wadda jirgin yaƙi mai ɗaukar jiragen sama ke jagoranta, ke cikin ruwan Gabas ta Tsakiya, wakilan Amurka da Iran sun gudanar da tattaunawa a Muscat ranar Juma’a, ƙarƙashin sasancin Oman, ba tare da sun haɗu kai tsaye ido-da-ido ba.

Me Trump ya ce kan tattaunawar?

Trump ya bayyana cewa tattaunawar tsakanin kasashen biyu ta kasance mai ma'ana.

"Mu ma mun yi tattaunawa mai kyau ƙwarai kan Iran. Za mu sake haɗuwa a farkon mako mai zuwa.”

- Donald Trump

Jim kaɗan bayan kammala tattaunawar, Amurka ta sanar da sabbin takunkumi kan wasu kamfanonin jigilar kaya da jiragen ruwa, da nufin rage fitar da man fetur na Iran.

Kara karanta wannan

Tarihin yaron Shekau da ya jagoranci kashe Musulmai kusan 200 a Kwara

Trump ya kuma sanya hannu kan wani umarnin shugaban kasa a ranar Juma’a, wanda ya ba gwamnatinsa damar kakaba haraji kan kayayyakin ƙasashen da ke yin kasuwanci da Iran, tashar RFI ta dauko labarin.

Wannan na iya shafar kasuwanci da ƙasashe irinsu China, Jamus da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Duk da cewa Iran ta yi gargaɗi kan larin barazana bayan Washington ta yi ishara da yiwuwar ƙarin matakin soji, Trump ya ce:

“Idan ba su yi yarjejeniya ba, abin da zai biyo baya zai zama mai tsanani ƙwarai.”

Me aka tattauna a kai?

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, wanda ya jagoranci tawagar Iran a Muscat, ya ce tattaunawar ta taƙaita ne kawai kan shirin nukiliyar Iran, wanda ƙasashen Yamma ke zargin yana da nufin ƙera bam ɗin nukiliya, yayin da Tehran ke jaddada cewa na zaman lafiya ne.

Iran na sa ran ci gaba da tattaunawa da Amurka
Jagoran juyin juya halin Iran, Ayatollah Ali Khamenei Hoto: @khamenei
Source: Twitter

Tawagar Amurka, ƙarƙashin jagorancin wakilin Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff da surukin Trump mai tasiri, Jared Kushner, sun kuma so a tattauna batun goyon bayan Iran ga kungiyoyin mayaƙa, shirinta na makamai masu linzami da kuma yadda take mu’amala da masu zanga-zanga.

Trump ya gargadi Iran

Kara karanta wannan

Bayan kyautar N100m, gwamna Abba ya dauki matakai a kan gobara a kasuwar Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya aika da sakon gargadi ga kasar Iran.

Donald Trump ya yi gargadin cewa lokaci na ƙurewa ga Iran ta zauna kan teburin tattaunawa domin kauce wa ɗaukar matakin soji daga Amurka.

Shugaban na Amurka ya ce Iran na bukatar shiga tattaunawa domin cimma yarjejeniya kan shirinta na nukiliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng