Mamdani: An Karanto Tarihin Annabi SAW a tsakiyar Amurka, An Nemi Koyi da Shi

Mamdani: An Karanto Tarihin Annabi SAW a tsakiyar Amurka, An Nemi Koyi da Shi

  • Magajin garin New York, Zohran Mamdani, ya jaddada birnin a matsayin mafakar baki ta hanyar ambaton nassosi daga Alƙur’ani da sauransu
  • Ya zargi jami’an shige da ficen Amurka da haddasa tsoro da wulakanci ga bakin haure, yana cewa addinai daban-daban suna koyar da kare baƙo
  • A taron, Mamdani ya sanya hannu kan umarni da ya ƙarfafa dokokin birnin na kare baki tare da kaddamar da shirin wayar da kai ga bakin haure

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

New York – Magajin birnin New York, Zohran Mamdani, ya bayyana cewa matsayin birnin na zama mafakar baki yana na daram.

Mamdani ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko a taron hada kan addinai daban-daban da ya gudana a New York, inda shugabannin addini da na al’umma kusan 400 suka halarta.

Kara karanta wannan

An fadi wadanda suka taimaka aka zubar da jinin Musulmai kusan 200 a Kwara

Zohran Mamdani a wajen taro
Magajin garin New York, Zohran Mamdani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

FOX News ta wallafa cewa Mamdani ya jaddada cewa koyarwar addinai daban-daban, ciki har da Musulunci da Kiristanci, suna umartar mabiya da su marawa “baƙo” baya, ba tare da la’akari da asalinsa ba.

Zargin Zohran Mamdani a Amurka

A jawabinsa, Mamdani ya zargi jami’an shige da ficen gwamnatin Amurka da jefa tsoro a zukatan mazauna birnin, yana cewa hanyoyinsu na aiki na rusa rayuwar jama'a.

Ya ce ana kwashe mutane daga motocinsu, ana nuna musu bindiga ba tare da suna da makami ba, lamarin da ya bayyana a matsayin zalunci.

Bukatar koyi da Annabi SAW a Amurka

Mamdani ya ce addinin Musulunci ya ginu ne bisa hijira, inda tarihi ya nuna Annabi Muhammadu ya bar gidansa a Makka zuwa Madina domin kubuta daga tsangwama.

Ya kawo hadisin Annabi SAW da ya ke nuna cewa Musulunci ya fara a matsayin bako, kuma zai kare a matsayin bako, sannan ya yi fatan alheri ga baki.

Kara karanta wannan

Malami da fararen hula 4 da aka kama da zargin hannu a yunkurin juyin mulki a Najeriya

Yayin da ya ke kira da a yi koyi da Annabi SAW, Mamdani ya ambaci aya ta 42 a Suratun An-Nahl da ke magana a kan masu hijira.

Masallacin Annabi SAW a Madina
Masallacin Annabi Muhammadu SAW a Madina. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Maganar Zohran Mamdani kan wasu addinai

Mamdani ya ambato nassosi daga Attaura da ke magana kan kaunar baƙi tare da kawo ayoyi da ke koyar da tausaya wa 'yan gudun hijira.

Magajin garin ya kuma karanto ayoyi daga Bible da ke nuna girmama baki, inda ya ce hakan abin koyi ne ga kasar Amurka a yanzu.

Mamdani ya dauki mataki a Amurka

A yayin taron, Mamdani ya sanya hannu kan wani umarni da ya sake tabbatar da dokokin birnin na zama mafakar baki tare da hana jami’an shige da fice shiga wurare ba tare da umarnin kotu ba.

Ya kuma sanar da kaddamar da shirin “ku san haƙƙoƙinku,” wanda zai raba takardu da littattafai 32,000 cikin harsuna 10 domin wayar da bakin haure kan haƙƙoƙinsu.

A ƙarshe, magajin birnin ya karrama wasu masu fafutukar kare bakin haure da suka rasa rayukansu a Minnesota, yana cewa sun zama abin koyi wajen kare baƙo har zuwa sadaukar da rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi gargadi ga maza masu dukan mata da auren wuri a Najeriya

Ga bidiyon Mamdani da Mario Nawfal ya wallafa a X:

An yabi Remi Tinubu a Amurka

A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi magana kan matar shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Donald Trump ya bayyana Sanata Remi Tinubu a matsayin mace mai daraja da ta tsaya wajen yada addinin Kirista a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan samun sabani tsakanin Trump da Najeriya game da zargin kisan Kiristoci da gwamnatin Tinubu ta karyata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng