Saudiyya Ta Yi Rangwame ga Attajirai game da Dokar Hana Sayan Barasa

Saudiyya Ta Yi Rangwame ga Attajirai game da Dokar Hana Sayan Barasa

  • Saudiyya ta fara bai wa attajiran baki marasa Musulunci damar sayen giya a Riyadh bayan haramci na tsawon shekaru 73
  • Sabon tsarin ya shafi masu 'Premium Residency' ko wadanda ke samun albashi mai tsoka, yayin da baki masu yawon bude ido ba su cikin tsarin
  • Masana na ganin matakin na daga cikin shirye-shiryen 'Vision 2030' domin jawo jari, kwararru da masu yawon bude ido

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Riyadh, Saudi Arabia - Kasar Saudiyya ta fara sassauta dokarta kan haramcin giya, inda a yanzu take bai wa wasu attajirai.

Rangwame game da dokar zai shafi attajirai baki da ba Musulmi ba domin samun damar sayen barasa a boye, mataki da ke nuna babban sauyi bayan haramci da ya dauki tsawon shekaru 73.

Saudiyya ta janye dokar hana sayar da giya ga attajirai
Yariman Saudiyya mai jiran gado, Shahzada Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud. Hoto: @insharifain.
Source: Twitter

Saudiyya: An rangwanta dokar hana sayar da giya

Kara karanta wannan

Za a mayar da shirgegen coci a Ingila zuwa masallaci bayan shekaru 11 a rufe

Rahoton BBC ya nuna cewa an bude wani shago na musamman a Riyadh, babban birnin kasar, wanda aka ware domin sayar da giya ga wasu tsirarun baki masu arziki.

Wannan yanki yana cikin wani yanki na musamman da ke cike da jakadun kasashe da manyan gidaje, kuma ba a bayyana sunansa a taswira ko alamu a fili.

Tun shekarar 1952, Saudiyya wacce ke dauke da wuraren ibada mafi tsarki biyu a Musulunci ta haramta sayar da giya.

Shagon giyar ya fara aiki ne a Janairun 2024, amma a wancan lokaci an takaita shi ga jakadun kasashen waje marasa Musulunci kawai, sai dai a karshen shekarar 2025, an fadada tsarin a boye domin bai wa baki masu arziki damar shiga.

Kafin mutum cancanta, dole ne ya mallaki 'Premium Residency', wacce ke kashe riyal na Saudiyya 100,000 a shekara, ko kuma ya nuna cewa yana samun akalla riyal 50,000 a wata.

Ana ta samun sauye-sauye a kasar Saudiyya

A ‘yan shekarun nan, kasar ta fara aiwatar da manyan sauye-sauye na zamantakewa da tattalin arziki domin sajewa da sauran kasashen duniya.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Katsina ya girgiza majalisa, ta mika bukata wajen Tinubu

A karkashin jagorancin Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman, Saudiyya ta sake bude sinima, ta shirya manyan bukukuwan waka.

Har ila yau gwamnatin Saudi ta bai wa mata damar tukin mota, sannan ta rage karfin ‘yan sandan addini.

Attajirai za su samu sauki kan sayan giya a Saudiyya
Yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud. Hoto: Brendan Smilowski.
Source: UGC

Wadanda tsarin zai shafa a Saudiyya

Wannan tsarin yawanci na manyan jami’an kamfanoni, masu zuba jari da kwararru ne da kasar ke bukata.

Rahotanni sun nuna cewa farashin giya a wani shago ya fi na kasashen yamma tsada sau biyu zuwa uku, amma ya fi arha idan aka kwatanta da kasuwar boye da ake yi a Saudiyya tsawon lokaci.

Masu sayen giyar sun ce ana rufe wayoyinsu kafin shiga shagon, kuma ana iya jinkiri fiye da awa guda a layi.

Babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Saudiyya, kuma da yawa sun ce sun samu labarin ne ta bakin abokai.

Masana sun ce wannan boyayyen salo na nufin gwamnati na kokarin kauce wa tayar da kura a cikin al’umma, duba da cewa giya har yanzu babban abin kyama ne ga yawancin ‘yan Saudiyya.

Kara karanta wannan

Sanatan da ya rasa dan'uwansa a hannun 'yan bindiga ya gano hanyar magance rashin tsaro

Duk da haramcin, giya ta dade tana yawo a boye a kasar a gidaje, bukukuwan sirri da kuma sansanonin baki yayin da wasu ke shigo da ita ta hanyoyin jakadanci ko kasuwar bayan fage.

Lokacin da aka fara wannan sabon tsari ya zo ne a daidai lokacin da Saudiyya ke fuskantar matsin tattalin arziki sakamakon raguwar kudin man fetur.

An hango hanyar samun kudin shiga

Kasar na kokarin jawo kwararru, masu zuba jari da masu yawon bude ido domin bunkasa bangarorin da ba na man fetur ba, cewar The Business Standard.

Yawon bude ido na daga cikin ginshikan Vision 2030, inda Saudiyya ta karbi kusan baƙi miliyan 30 daga kasashen waje a shekarar 2024, kuma tana fatan kai miliyan 70 nan da shekarar 2030.

Rahotanni sun kuma ce gwamnati na shirin bude wasu shagunan giya guda biyu a Jeddah da Dhahran, duk da cewa har yanzu za a takaita su ga baki masu arziki da jakadu.

Masana harkar otel sun ce suna shirin yiwuwar a nan gaba a bai wa masu yawon bude ido damar sayen giya, musamman a wuraren shakatawa kamar gabar Tekun Red Sea da tsohon birnin Al-Ula.

Kara karanta wannan

Abin da ya hana Epstein kasuwancin mai a Najeriya, ya shiya ganawa da Jonathan

Sai dai masana na ganin Saudiyya ba za ta yi sassauci kamar Dubai ba, illa dai ta bi tsari mai tsauri irin na Qatar, inda ake takaita shan giya a wurare na musamman.

Saudiyya ta magantu kan tsaron Najeriya

Mun ba ku labarin cewa Saudiyya ta bayyana cewa watsi da marayu da yara marasa galihu na daga cikin abubuwan da ke rura wutar matsalar tsaro a Najeriya.

Ta gargadi gwamnatin Najeriya kan illar barin yara suna gararamba a gari, tana mai cewa hakan barazana ce ga tsaron kasar Afrikar.

Saudiyya ta zakulo marayu sama da 1,000 daga addinin Musulunci da Kiristanci, ta ba su horo da jarin kama sana'a domin dogaro da kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.