Trump Ya ba da Mamaki da Ya Girmama Matar Tinubu a wajen Taron Amurka

Trump Ya ba da Mamaki da Ya Girmama Matar Tinubu a wajen Taron Amurka

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya yaba wa Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, a taron addu'a da aka gudanar a Washington D.C
  • Trump ya bayyana Remi Tinubu a matsayin mace mai daraja kuma jagora a harkar addinin Kirista, yana mai nuna girmamawa ga rawar da take takawa
  • Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake samun muhawara kan batun tsaro da ‘yancin addini a Najeriya a idon duniya wanda ya dauki hankalin kasashe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta gana da Shugaban Amurka Donald Trump yayin taron addu'a karo na 74 a Amurka da aka gudanar a Capitol Hill, Washington D.C.

A yayin taron, an gayyaci Remi Tinubu ta hau dandalin taron tare da Trump, lamarin da ya ja hankalin mahalarta daga kasashe daban-daban.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura bataliyar sojoji Kwara bayan kashe Musulmai sama da 100

Remi Tinubu da shugaba Donald Trump
Sanata Oluremi Tinubu a hagu, Shugaba Donald Trump a dama. Hoto: Oluremi Tinubu|Getty Images
Source: Facebook

A bidiyon da fadar White House ta wallafa a X, Trump ya yi amfani da damar wajen yabawa uwargidan shugaban Najeriyar, yana mai bayyana ta a matsayin mace mai daraja.

Yabon Donald Trump ga Remi Tinubu

A lokacin jawabin da ya gabatar a gaban ‘yan majalisar dokokin Amurka, shugabannin addini da baki na kasashen waje, Trump ya hango Remi Tinubu a cikin taron inda ya tsayar da jawabin nasa domin nuna mata girmamawa.

Ya ce Amurka na matukar jin dadin halartar Uwargidan Shugaban Najeriya, wadda a cewarsa ke kuma zama fasto a daya daga cikin manyan majami’u a Najeriya.

Trump ya bayyana ta a matsayin mace mai mutunci da daraja, yana mai cewa ganinta a taron babban abin girmamawa ne ga Amurka da taron baki daya.

Matsayin Remi Tinubu a harkar addini

Remi Tinubu fasto ce da aka naɗa a cocin Redeemed Christian Church of God, cocin da Fasto Enoch Adeboye ya kafa, wanda ke daga cikin manyan majami’un Pentikostal a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan turo sojoji Abuja, Amurka ta yi maganar yakar 'yan ta'adda a Najeriya

Rawar da take takawa a harkar addini ta sa ta shahara ba kawai a siyasa ba, har ma a harkokin addini, inda take da tasiri a cikin al’umma.

Trump ya jaddada wannan matsayi nata ne yayin jawabin, yana mai danganta girmamawar da ake mata da jajircewarta wajen hidimar addini.

Muhawara kan batun ‘yancin addini

Jawabin Trump ya zo ne a daidai lokacin da ake samun ikirari daga gare shi da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar hare-hare masu yawa.

A watan Oktoba, 2025, Trump ya ayyana Najeriya a matsayin kasa mai matukar damuwa dangane da zargin kai hare-hare kan Kiristoci, matakin da gwamnatin Najeriya ta yi watsi da shi.

Yadda Trump ya yi bayani Amurka
Donald Trump na jawabi a taron addu'a na Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gwamnatin tarayya ta ce kalubalen tsaro da ake fuskanta a kasar na da nasaba da ta’addanci da laifuffuka, ba wai rikicin addini ba, tana mai jaddada cewa kundin tsarin mulki na kare ‘yancin Musulmi da Kiristoci.

Ga bidiyon da ya yi bayanin a kasa:

Trump ya kara kawo hari Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ko 'yan kwanaki da suka wuce ya sake kawo hari Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: Gwamna Radda ya yi karatun ta natsu, ya gano amfanin sake zaben Tinubu

Trump ya yi magana ne yayin taro a Amurka, inda ya ce suna cigaba da ragargazar 'yan ta'adda a Najeriya tun bayan harin farko da ya kawo.

Ya kara da cewa sun hada kai da hukumomin Najeriya wajen kawo farmaki kan 'yan ta'addan ISIS a ranar Kirsimetin 2025 a Sokoto.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng