Trump Ya Fasa Kwai, Ya Yi bayani kan Harin da Ya Sake Kawowa Najeriya
- Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa ta haɗa kai da Najeriya wajen kai hare-haren sama kan mayakan ISIS a Sokoto
- A bayanin da ya yi, Donald Trump ya ce an kai hare-haren ne domin murkushe mayakan ISIS da ya zarga da kashe Kiristoci da dama a Najeriya
- Tun a lokacin da aka kai harin, ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana da cewa sun yi sanadin kashe ‘yan ISIS da dama da suka addabi jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa hare-haren sama da aka kai kan mayakan ISIS a Najeriya, a ranar Kirsimetin 2025, an yi su ne cikin cikakkiyar haɗin gwiwa da gwamnatin Najeriya.
A cewarsa, manufar hare-haren ita ce murkushe mayakan ISIS da ya zarga da aikata kashe-kashe masu yawa kan Kiristoci a Najeriya.

Source: Getty Images
A bidiyon da fadar White House ta wallafa a X, Shugaba Trump ya bayyana dalilan zabar ranar Kirsimeti domin kai farmaki Najeriya.
Dalilin Donald Trump na kai hari Najeriya
Shugaba Trump ya bayyana cewa ya ba da umarnin kai hare-haren ne domin nuna ƙarfi da kuma aika saƙo kai tsaye ga ‘yan ISIS.
Ya ce tun farko an shirya kai harin a wata rana dabam, amma shi da kansa ya dage sai an yi shi a ranar Kirsimetin shekarar 2025.
A kalamansa, Trump ya ce sun yi aiki tare da gwamnatin Najeriya, amma ya jaddada cewa dole ne hukumomin tsaron ƙasar su ƙara tsaurara matakai.
Shugaban ya ce hare-haren sun yi wa ‘yan ISIS mummunan tasiri har suka rude, ba tare da sanin abin da ya faru ba.
Trump ya kara kai hari Najeriya
A cewar Trump, ya ba da takamaiman umarni ga jami’an tsaron Amurka da su tabbatar an kai harin a ranar Kirsimeti, ba kafin ranar ba kuma ba bayan ta ba.
A bidiyon da Channels TV ta wallafa a YouTube, Trump ya nuna cewa ya ce ya umarci ministan yaki, Pete Hegseth da ya tabbatar da aiwatar da harin yadda ya dace.
Trump ya ce hare-haren ba su tsaya nan ba, domin bayan farmakin ranar Kirsimeti, an sake kai wasu hare-hare daga baya domin ci gaba da raunana ƙungiyar ISIS.

Source: Facebook
Ya bayyana waɗannan hare-haren a matsayin masu ƙarfi da kuma tasiri sosai, yana mai cewa sun bar mayakan ISIS cikin firgici da rashin shiri.
An kashe Musulmai a Kwara
A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda sun kai hari jihar Kwara sun kashe Musulmai sama da 100, duk da cewa gwamnati ta ce 75 ne.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da harin da aka kai yana mai cewa ya umarci a tura bataliyar sojoji yankin da abin ya faru.
Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana cewa an kashe mutanen ne saboda sun ki karbar bakuwar akidar ta'addanci da 'yan ta'adda suka je da ita.
Asali: Legit.ng

