Attajiri Lamba 1 a Duniya, Elon Musk Ya Bayyana Abin da Kudi ba Za Su Iya Saye ba
- Elon Musk, attajirin da ya fi kowa kudi a duniya ya haddasa muharawa a kafafen sada zumunta kan farin cikin 'dan adam a rayuwa
- Hamshakin attajirin ya gamsu da hikimar masu zance da ke cewa kudi ba su iya sayen farin ciki, inda ya ce masu wannan magana sun fahimci rayuwa
- Wannan kalamai sun haddasa shakku daga mabiyan attajirin, wasu na ganin maganar haka take, wasu kuma na cewa kudi na samar da damarmaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Attajirin da ya fi kowa kudi a duniya, Elon Musk ya haddasa muhawara mai zafi a yanar gizo bayan ya bayyana cewa dukiya ba ta tabbatar da samun farin ciki.
Duk kuwa da cewa shi ne mutumin da ya fi kowa kudi a fadin duniya, Elon Musk ya ce wadanda ke cewa kudi ba su iya sayen farin ciki sun iya zancen hikima.

Kara karanta wannan
Masu ibada da aka sace a Kaduna, sun fadi yadda rayuwa ta kasance a hannun 'yan bindiga

Source: Getty Images
Musk, wanda shi ne shugaban kamfanin Tesla, ya wallafa hakan ne a ranar Alhamis ta shafinsa na X wanda aka fi sani da Tuwita.
Elon Musk ya rubuta cewa:
"Duk wanda ya ce 'kudi ba sa sayen farin ciki', tabbas ya san abin da yake fada."
Mutane sun fara martani kan kalaman Musk
Zuwa lokacin hada wannan rahoto, wadanda suka duba rubutun nasa sun haura miliyan 51, sannan wadanda suka sake wallafa shi a shafukansu sun kai kusan 56,000.
Haka zalika, dubban mutane sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan kalamai na attajirin, sai dai sun kasu kashi biyu, kamar yadda The Cable ta tattaro.
Yayin da wasu suka amince da cewa dukiya ba ta kare mutum daga kalubale na rayuwa ko na bacin rai, wasu kuma sun bayyana cewa kudi suna inganta rayuwa da kuma samar da damammaki cikin sauki.
Musk bai yi wani karin bayani ko dalilin yin wannan furuci ba. Sai dai a baya, hamshakin attajirin ya taba yin magana kan matsin lamba da yake fuskanta wajen jagoranci, sa idon jama'a, da wahalar tafiyar da manyan kamfanoni lokaci guda.
Nawa Elon Musk ya mallaka a duniya?
A cewar Bloomberg Billionaires Index, mai auna attajiran duniya, Musk ya zama mutum na farko a duniya da arzikinsa ya kai Dala biliyan 638 a ranar 16 ga watan Disamba, 2025.
Rahoton Bloomberg ya nuna cewa arzikinsa ya karu da kashi 42.7 cikin 100 cikin shekara daya kacal (daga Disamba 2024).

Source: Getty Images
Wannan kalamai na Musk sun sake jefa shi cikin abubuwan da aka fi tattaunawa a kafafen sada zumunta game da ma'anar dukiya, gamsuwa da rayuwa, da kuma iyakacin abin da kudi za su iya yi wa dan Adam.
Dangote ya bar wasiyya kan kudinsa
A wani labarin, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa ya bar wa iyalansa wasiyyar cewa za a cire 25% na dukiyarsa a ba gidauniyarsa don ci gaba aikin taimako.
Dangote, 'dan asalin jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ya tsara kashe Naira biliyan 100 a kowace shekara a shirin tallafin ilimi mafi girma a tarihi.
Mai kudin ya bayyana cewa ya rattaba hannu kan wasiyyar cewa ya keɓe 25% na dukiyarsa zuwa Aliko Dangote Foundation (ADF) domin tabbatar da dorewar sabon Shirin Tallafin Ilimi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
