Bayan Turo Sojoji Abuja, Amurka Ta Yi Maganar Yakar 'Yan Ta'adda a Najeriya
- Rundunar AFRICOM ta Amurka ta bayyana Najeriya a matsayin muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa wajen dakile barazanar ISIS da Al-Qaeda a Afirka ta Yamma
- Kwamandan AFRICOM ya ce karuwar hare-haren kungiyoyin ta’addanci na barazana ga tsaron manyan biranen yankin, lamarin da ke bukatar hadin gwiwa
- Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Amurka ta tabbatar da isowar wasu sojojinta Najeriya domin yaki da 'yan ta'adda da ta ce za ta cigaba da yi a kasar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Rundunar sojin Amurka da ke kula da Afirka, AFRICOM, ta ayyana Najeriya a matsayin daya daga cikin manyan kasashen da take dogaro da su wajen yaki da kungiyoyin ta’addanci na ISIS da Al-Qaeda.
Wannan bayani ya fito ne a daidai lokacin da ake fuskantar karuwar hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai a yankin Sahel.

Source: Getty Images
Gwamnatin Amurka ta wallafa cewa kalaman sun fito ne daga bakin Kwamandan AFRICOM, Janar Dagvin Anderson, yayin wani taron manema labarai ta yanar gizo da aka gudanar.
Maganar Amurka kan 'yan ta'adda
Janar Anderson ya bayyana cewa rundunarsa na sa ido kan yadda kungiyoyin ISIS da Al-Qaeda ke kara fadada ayyukansu a yankin Sahel, musamman ta hannun kungiyar JNIM da ke da alaka da Al-Qaeda.
Ya ce wadannan kungiyoyi na kara matsa lamba a yankuna daban-daban, tare da barazanar kutsawa manyan biranen kasashen yankin, da kuma yada tashin hankali zuwa wasu kasashe na gabar Tekun Guinea.
Punch ta rahoto ya ce lamari ya nuna bukatar kasashen duniya su kara karfafa hadin gwiwa, musamman ta fuskar tsaro, musayar bayanan sirri da dabarun yaki da ta’addanci.
Alakar Amurka da Najeriya kan tsaro
Kwamandan AFRICOM ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai cikakken shiri da jajircewa wajen yaki da ta’addanci, yana mai cewa hadin gwiwar da ke tsakaninta da Amurka ya zama abin koyi a yankin Afirka ta Yamma.
Ya ce Najeriya ta nemi tallafin Amurka a wasu fannoni na musamman da suka hada da tattara bayanan sirri, sa ido da bincike, tare da hada wadannan bayanai domin inganta ayyukan tsaro.
A cewarsa, wannan hadin gwiwa ta sa bangarorin biyu sun fi samun nasara wajen dakile barazanar ISIS da Al-Qaeda, yana mai jaddada cewa aiki tare na da matukar muhimmanci ga makomar tsaron yankin.
Maganar Sojan Amurka da Tinubu
Janar Anderson ya kuma tuno da taron Aqaba Process da aka gudanar a birnin Rome na kasar Italiya a 2025, wanda ya mayar da hankali kan barazanar ta’addanci a Afirka ta Yamma.
Ya bayyana cewa a taron ya gana da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, inda suka tattauna hanyoyin karfafa hadin gwiwa da dabarun tinkarar barazanar tsaro a yankin.

Source: Twitter
Gwamnatin Amurka ta turo sojoji Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta turo wata tawagar sojoji Najeriya a abin da ta kira shirin yaki da ta'addanci a kasar.
Hakan na zuwa ne bayan doguwar tattaunawa da aka yi da jagororin Najeriya da na Amurka kan zargin kisan Kiristoci a wasu yankuna.
Rahotanni sun nuna cewa tawagar sojojin ba ta da yawa, kuma wannan ne karon farko da aka turo su bayan harin da Amurka ta kai Sokoto a 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

