Trump Ya Saki Sunayen 'Yan Najeriya 79 da za Su Fuskanci Fushinsa

Trump Ya Saki Sunayen 'Yan Najeriya 79 da za Su Fuskanci Fushinsa

  • Gwamnatin Amurka ta bayyana shirin korar ’yan Najeriya 79 da ke cikin jerin “manya-manyan masu laifi” da hukumomin tsaro suka fitar
  • Hukumar DHS ta ce mutanen sun aikata laifuffuka daban-daban da suka hada da fataucin miyagun kwayoyi, fyade, damfara da kisan kai
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin shugaba Donald Trump ke kara tsaurara matakan korar baki masu laifuffuka daga kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa tana shirin korar ’yan Najeriya akalla 79 da ke cikin jerin mutanen da ta bayyana a matsayin “mafi muni cikin masu laifi.”

Wannan mataki na daga cikin tsauraran matakan shige da fice da ake aiwatarwa a karkashin gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump.

Kara karanta wannan

Binciken yunkurin juyin mulki ya sa an kama tsohon Janar mai rike da sarauta

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump
Donald Trump yana magana a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hukumar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) ta ce an kama mutanen ne ta hannun Hukumar Kula da Shige da Fice (ICE), inda yawancinsu tsofaffin fursunoni ne da aka riga aka yanke musu hukunci kan manyan laifuffuka.

Donald Trump zai fatattaki 'yan Najeriya

Rahoton Radio Nigeria ya ce hukumar DHS ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin alkawarin da Donald Trump ya dauka na korar bakin haure masu aikata manyan laifuka daga Amurka.

Sanarwar ta ce, a karkashin jagorancin Ministar tsaron cikin gida, Noem, Ma’aikatan DHS da ICE na cika alkawarin Trump ta hanyar fara korar masu laifi mafi hadari.

Sunayen ’yan Najeriya da za a kora

Daga cikin ’yan Najeriya da ke cikin jerin akwai Boluwaji Akingunsoye, Ejike Asiegbunam, Emmanuel Mayegun Adeola, Bamidele Bolatiwa.

Haka zalika akwai Ifeanyi Nwaozomudoh, Aderemi Akefe, Solomon Wilfred, Chibundu Anuebunwa, Joshua Ineh, Usman Momoh, Oluwole Odunowo, Bolarinwa Salau da Oriyomi Aloba.

Kara karanta wannan

Tofa: Gwamna ya rufe dukkan makarantu, ya sanya dokar zaman gida ta awanni 20

Haka kuma akwai Olusegun Martins, Kingsley Ariegwe, Olugbenga Abass, Oyewole Balogun, Adeyinka Ademokunla, Christian Ogunghide, Christopher Ojuma, Olamide Adedipe, Patrick Onogwu, Olajide Olateru-Olagbegi da Omotayo Akinto.

Sauran sun hada da Oludayo Adeagbo, Olaniyi Akintuyi, Talatu Dada, Olatunde Oladinni, Jelili Qudus, Abayomi Daramola, Toluwani Adebakin, Olamide Jolayemi, Isaiah Okere, Benji Macaulay da Joseph Ogbara.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu na bayani a taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A jerin sunayen akwai Kenneth Unanka, Jeremiah Ehis, Oluwafemi Orimolade, Ayibatonyе Bienzigha, Uche Diuno, Akinwale Adaramaja, Boluwatife Afolabi, Chinonso Ochie, Olayinka A. Jones, Theophilus Anwana, Aishatu Umaru da Henry Idiagbonya.

Sauran sun hada da Okechukwu Okoronkwo, Daro Kosin, Sakiru Ambali, Kamaludeen Giwa, Abimbola Esan, Elizabeth Miller, Chima Orji, Adetunji Olofinlade, Abdul Akinsanya, Elizabeth Adeshewo, Dennis Ofuoma da Boluwaji Akingunsoye.

Kara karanta wannan

Amurka ta saki sunayen ƙasashen Afrika da ba ta so ƴan ƙasarta su ziyarta a 2026

Bernard Ogie Oretekor, Abiemwense Obanor, Olufemi Olufisayo Olutiola, Chukwuemeka Okorie, Cyril Odogwu, Ifeanyi Echigeme, Kingsley Ibhadore, Suraj Tairu, Peter Equere, Dasola Abdulraheem, Adewale Aladekoba da Akeem Adeleke na cikinsu.

Ragowar sunayen sun hada da Abraham Ola Osoko, Oluchi Jennifer da Chibuzo Nwaonu, Quazeem Adeyinka, Ifeanyi Okoro, Oluwaseun Kassim da Olumide Bankole Morakinyo.

Amurka ta ba 'yan Najeriya dama

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Amurka ta bude kofar karatu ta yanar gizo ga 'yan kasashen duniya da dama ciki har da Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa an ware kwasa-kwasai da dama da ke da alaka da yaren Turanci da za a koya wa wadanda ke da sha'awar shiga shirin.

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da yadda jama'ar da suke son shiga shirin za su samu damar shiga cikinsa da sharudan da ke so su cika.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng