Amurka Ta Saki Sunayen Ƙasashen Afrika da ba Ta So Ƴan Ƙasarta Su Ziyarta a 2026
- Amurka ta saka Nijar cikin jerin kasashen da ta gargadi ’yan kasarta kada su ziyarta a 2026, saboda tabarbarewar tsaro
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce ba za ta iya ba da cikakken tallafin jakadanci ga ’yan Amurka a Nijar ba, sai birni daya kawai
- Shigar Nijar ya kara yawan kasashen Afirka da ke karkashin matakin gargadi na mataki na hudu zuwa takwas, ciki har da Mali, Libya da Sudan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Washington DC, US - Gwamnatin Amurka ta sabunta jerin kasashen Afirka da ta gargadi ’yan kasarta kada su yi balaguro zuwa gare su a shekarar 2026.
Amurka ta sabunta jerin sunayen ne inda ta kara saka Jamhuriyar Nijar cikin kasashen da ke karkashin matakin gargadi mafi tsanani.

Source: Getty Images
An saka Nijar cikin kasashe masu hatsari
A cikin sanarwar da aka fitar a ranar 30 ga Janairu, 2026, gwamnatin Amurka ta gargadi ’yan kasarta da su kaurace wa duk wani balaguro zuwa Nijar baki daya, cewar Vanguard.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanya Nijar a matakin gargadi tana danganta hakan da tabarbarewar tsaro da ke cike da ta’addanci, garkuwa da mutane, laifuffukan tashin hankali da rikice-rikicen cikin gida.
Ta ce hukumomin Amurka ba za su iya ba da tallafin jakadanci na yau da kullum ko na gaggawa ga ’yan kasarsu a wajen birnin Niamey ba.
Sanarwar ta kara da cewa har yanzu ana ci gaba da aiwatar da dokar ta-baci da takaita zirga-zirga a sassa da dama na kasar Nijar.

Source: Twitter
Musabbabin kara saurara tsaro da Amurka ta yi
Jami’an Amurka sun nuna wasu sababbin hare-haren ’yan ta’adda a matsayin hujjar tabarbarewar tsaro, ciki har da musayar wuta da aka yi da ’yan kungiyar IS a filin jirgin saman Diori Hamani da ke Niamey.
A karkashin ka’idojin tsaro da ke aiki yanzu, an wajabta wa baki da ke tafiya a wajen babban birnin Nijar yin hakan ne tare da rakiyar sojojin Nijar.
Haka kuma, an kakaba wa ma’aikatan gwamnatin Amurka da ke Nijar amfani da motocin kariya, bin dokar hana fita da kuma hana su ziyartar gidajen abinci da kasuwannin bude fili.
Gwamnatin Amurka ta shawarci ’yan kasarta da har yanzu ke Nijar da su bi irin wadannan matakan kariya domin kare kansu, cewar BBC.
Shigar Nijar cikin wannan jerin ya kara yawan kasashen Afirka da ke karkashin gargadin mataki na 4 zuwa takwas.
Sauran kasashen sun hada da Libya, Mali, Burkina Faso, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Sudan ta Kudu, Sudan, Somalia, da kuma wasu sassan yankin Sahel.
Shigar Nijar cikin jerin ya sake nuna yadda matsalolin tsaro da gazawar shugabanci ke ci gaba da addabar wasu sassan Afirka, lamarin da ke shafar yadda kasashen duniya ke kallon hadarin tafiya zuwa yankin.
Amurka ta ba yan Najeriya damar karatu
Kun ji cewa ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da fara kwasa-kwasan koyon Turanci kyauta domin ƙara ƙwarewar sana’a da faɗaɗa damar samun aiki.
An tsara kwasa-kwasan ne ta shirin OPEN na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, inda mahalarta za su koyi darussa tare da hulɗa da masu koyo daga ƙasashe.
Rahotanni sun nuna cewa za a fara gudanar da darusan daga ranar 5, Janairu, 2026 zuwa 30, Maris, 2026, tare da buɗe rajista har zuwa 23, Maris, 2026.
Asali: Legit.ng

