Agogon Tashin Duniya Ya Kara Matsawa, Masifa Ta Tunkaro Mutane
- Masana kimiyya sun ce duniya ta ƙara matsowa gaba da mummunar barazana, bayan da agogon tashin duniya ya kara nausawa da daƙiƙa 85
- Kungiyar Bulletin of the Atomic Scientists ta danganta hakan da ƙaruwa a haɗarin makaman nukiliya, sauyin yanayi, da fasahohin zamani kamar AI
- Masana sun yi gargaɗin cewa rashin haɗin kai tsakanin ƙasashe da yaɗuwar bayanan ƙarya na ƙara tsananta haɗarin da ke fuskantar bil’adama
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Masana kimiyya sun sanar da sabon matsayin agogon tashin duniya na shekarar 2026, inda suka sa shi a daƙiƙa 85, matakin da bai taɓa kaiwa haka ba tun kafa agogon a shekarar 1947.
Agogon tashin duniya wata alama ce da ke nuna yadda bil’adama ke kusantar barazana a duniya, inda tsakar dare ke wakiltar lokacin da duniya za ta zama wuri da ba za a iya rayuwa a cikinta ba.

Source: Getty Images
CNN ta wallafa cewa kungiyar Bulletin of the Atomic Scientists ce ta sanar da sabon lokacin ne bayan nazari kan manyan barazanar da ke addabar duniya a halin yanzu.
Agogon tashin duniya ya matsa
A cewar kungiyar, babban dalilin matsawar agogon daga daƙiƙa 89 da aka sa shi a bara zuwa daƙiƙa 85 shi ne rashin isasshen ci gaba wajen rage manyan barazanar duniya.
Wadannan sun haɗa da haɗarin makaman nukiliya, rikicin sauyin yanayi, barazanar cututtuka, da kuma bunƙasar fasahohin da ke iya tayar da hankali.
Shugabar kungiyar, Alexandra Bell, ta ce bil’adama bai yi abin da ya kamata ba wajen shawo kan barazanar da ke iya lalata duniya ba.
Tasirin rikice-rikice a fadin duniya
Shugaban kwamitin kimiyya da tsaro na kungiyar, Dr Daniel Holz, ya ce maimakon ƙasashe su ɗauki gargaɗin da aka yi a baya, sai dai rikice-rikice sun ƙara tsananta.
Ya bayyana cewa a shekarar 2025 an samu ƙaruwa a hare-haren soja, ciki har da rikice-rikicen da suka shafi ƙasashen da ke da makaman nukiliya.

Kara karanta wannan
Solar: Gwamnati ta ware N7bn don samar da wuta ta hasken rana a fadar shugaban kasa
Haka kuma, yarjejeniyar ƙarshe da ke takaita yawan makaman nukiliya tsakanin Amurka da Rasha na dab da ƙarewa a 4 ga watan Faburairu, 2026.

Source: Getty Images
A cewarsa, idan hakan ta faru ba tare da sabuwar yarjejeniya ba, duniya za ta shiga wani yanayi na gasar tara makaman nukiliya ba tare da iyaka ba.
Menene agogon tashin duniya?
Agogon tashin duniya wata alama ce da masana da suka yi aiki a shirin ƙera bam ɗin nukiliya a yaƙin duniya na biyu suka kirkiro domin jan hankalin duniya kan haɗarin makaman nukiliya.
Daga baya, kungiyar Bulletin of the Atomic Scientists ta faɗaɗa lissafinsa domin haɗa sauyin yanayi da sauran manyan barazanar duniya.
Al-Jazeera ta wallafa cewa duk da agogo ba na gaske ba ne, masana sun ce ana amfani da shi ne domin jawo tattaunawa kan makomar bil’adama, tare da tunatar da duniya irin haɗarin da ke gabanta.
An kai hare-hare a kasar Nijar
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasar Nijar, Abdourahamane Tchiani ya yi bayani game da wasu hare-hare da aka kai kasarsa.
A bayanin da ya yi, shugaban kasar ya zargi kasashen Faransa, Benin da Ivory Cost da hannu a harin da aka kai cikin dare.
Ya bayyana cewa harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 ciki har da dan kasar Faransa da jikkata sojoji amma kuma an kama wasu mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

