Jirgin Sama Dauke da Fasinjoji Ya Gamu da Tsautsayi, 'Dan Majalisa da Mutane 14 Sun Mutu
- Hukumomi a kasar Colombia sun gano tarkacen jirgin saman da ya bata a hanyarsa ta zuwa birnin Ocana ranar Laraba
- Kamfanin sufurin jirgin saman Satena ya tabbatar da cewa duka mutane 15 da ke cikin jirgin sun rasa rayukansu ciki har da 'dan Majalisa
- Shugaban kasar Colombia, Gustavo Petro ya bayyana alhininsa tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Colombia - Hukumomi a kasar Colombia sun samu nasarar gano jirgin saman da ya bata a hanyarsa ta zuwa birnin Ocana jiya Laraba.
Dukkan mutane 15 da ke cikin jirgin saman mai daukar fasinjoji sun riga mu gidan gaskiya biyo bayan hadarin da jirgin ya yi a Arewacin kasar Colombia.

Source: Getty Images
Kamfanin jiragen sama na kasar, Satena ya tabbatar da aukuwar wannan lamari a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.
Jirgin kamfanin Satena ya yi hatsari
Kamfanin Satena ya bayyana cewa jirginsa samfurin Beechcraft 1900 ya gamu da wannan tsautsayi ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Ocaña, wani birni da ke kusa da iyakar Venezuela.
Kamfanin bai bayyana musabbabin hadarin ba kawo yanzu, amma ya ce an gano tarkacen jirgin a wani yanki mai duwatsu da ke da wuyar isa.
Jirgin, mai lamba NSE 8849, ya tashi ne daga birnin Cúcuta, mai tazarar kusan kilomita 100 daga Arewa maso Gabashin Ocaña, dauke da fasinjoji 13 da ma'aikata biyu.
An rasa hanyar sadarwa da jirgin na kusan mintuna 11 kafin lokacin da ake ranar zai sauka da misalin karfe 12:05 na rana (agogon kasar Colombia) a ranar Laraba.
'Dan Majalisa ya rasu a hatsarin jirgi
Manyan mutanen da suka rasu a hatsarin jirgin sun hada da 'dan majalisar dokokin Colombia, Diógenes Quintero Amaya, da 'dan takarar kujerar Majalisa a zabe mai zuwa, Carlos Salcedo
An bayyana 'dan Majalisar da hatsarin ya rutsa da shi a matsayin mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen taimakon marasa galihu.
Quintero yana daya daga cikin mutane 16 da ke rike da kujerun majalisa na musamman da aka ware wa wadanda rikicin cikin gida na Colombia ya shafa.
An fara bincike don gano gawarwakinsu
Hukumomin Colombia sun kaddamar da aikin neman gawarwaki a wurin da hadarin ya faru, tare da tallafin dakarun soji saboda wahalar yankin da kuma matsalolin tsaro.
Gwamnan jihar Norte de Santander, William Villamizar, ya shaida wa manema labarai cewa zuwa yanzu an zakulo gawarwaki bakwai, in ji rahoton BBC News.

Source: Getty Images
Shugaban kasar Colombia, Gustavo Petro, ya mika sakon ta'aziyyarsa, inda ya bayyana matukar bakin cikinsa bisa asarar rayukan da aka yi, yayin da masu bincike ke kokarin gano dalilin faruwar hadarin.
Jirgin Emirates ya yi hatsari a China
A wani rahoton, kun ji cewa jirgin sama na dakon kaya ya sauka daga kan titinsa, ya fada cikin SSSSSStekun da ke bayan filin jirgi a birnin Hong Kong na kasar China.
An ruwaito cewa cewa jirgin na kamfanin Emirates ya bugi wata motar sintiri kafin daga bisani ya afka cikin teku, lamarin da ya zama ajalin mutane biyu da ke cikin motar.
Jami’an ceto sun isa wurin a kan lokaci kuma sun yi nasarar kubutar da matuka da ma'aikatan jirgin guda hudu, wadanda duk sun tsira da raunuka kadan.
Asali: Legit.ng


