'Sojojin Amurka na Luguden Wuta a Najeriya Suna Kashe 'Yan Ta'adda,' Trump

'Sojojin Amurka na Luguden Wuta a Najeriya Suna Kashe 'Yan Ta'adda,' Trump

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa na daukar tsauraran matakai kan ‘yan ta’addan da ake zargi da kashe dubban Kiristoci a Najeriya
  • Trump ya yi wannan furuci ne yayin kaddamar da wani sabon tsari da ya kira “Board of Peace”, wanda ke da burin magance rikice-rikicen kasa da kasa a fadin duniya
  • Furucin na zuwa ne bayan wasu hare-haren sama da sojojin Amurka suka kai tare da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya kan ‘yan ta’addan kungiyar IS a 2025

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Shugaba Donald Trump ya ce kasar Amurka na yin nasara mai yawa wajen murkushe ‘yan ta’addan da ake zargi da kashe dubban Kiristoci a Najeriya, yana mai cewa an kai musu mummunan farmaki.

Kara karanta wannan

An fallasa yadda Trump ke tura makaman Amurka kusa da Iran a shirin yaki

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da wani sabon tsari da gwamnatinsa ta kafa mai suna “Board of Peace”, wanda aka tsara domin magance rikice-rikicen kasa da kasa.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Donald Trump yana jawabi a taron duniya a Switzerland. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar Tribune ta wallafa bidiyon da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi bayani a kasar Switzerland kan hare-haren a shafinta na X.

Furucin Donald Trump kan hari a Najeriya

A cewar Trump, ‘yan ta’addan da ke kai hare-hare a Najeriya, musamman wadanda ke kashe Kiristoci, sun fuskanci matsanancin martani daga Amurka.

Ya ce:

“A Najeriya, muna murkushe ‘yan ta’addan da ke kashe Kiristoci. Mun kai musu farmaki mai tsanani. Sun kashe dubban Kiristoci.”

Trump ya kara da cewa hare-haren sun biyo bayan umarninsa ga ma’aikatar Yaki ta Amurka, domin daukar mataki kan wadanda ya bayyana a matsayin ‘yan ta’adda masu kai farmaki kan fararen hula marasa laifi.

Kwamitin da Trump ya kafa a duniya

A wajen taron, Trump ya yi bayani kan sabon tsari na “Board of Peace” da ya kafa, wanda ya ce zai yi aiki tare da Majalisar Dinkin Duniya wajen magance rikice-rikice a duniya.

Kara karanta wannan

Sojoji sun shiga har dajin Sambisa sun yi wa 'Yan Boko Haram jina jina

Ya bayyana cewa idan aka kammala kafa wannan kwamiti gaba daya, zai samu damar shiga manyan lamurran tsaro a duniya tare da hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya.

Rahoton Reuters ya nuna cewa wasu kasashen duniya sun nuna shakku kan sabon tsarin, suna ganin yana iya rage rawar Majalisar Dinkin Duniya a matsayin babbar cibiyar diflomasiyya da warware rikice-rikice.

Yadda aka kaddamar da kwamitin Donald Trump
Taron kaddamar da kwamitin Donald Trump a Davos. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kasashen yankin Gabas ta Tsakiya kamar Turkiyya, Masar, Saudiyya da Qatar, da kuma wasu kasashe masu tasowa irin su Indonesia, sun shiga cikin tsarin, yayin da wasu manyan kasashe da abokan Amurka ke taka-tsantsan.

Harin da Amurka ta kawo Najeriya

A wani labarin, mun kawo muku cewa sojojin Amurka tare da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya sun kaddamar da hare-haren sama kan ‘yan ta’addan kungiyar ISIS a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Shugaba Donald Trump ya ce hare-haren sun kasance yadda ya kamata, yana mai cewa sojojin Amurka sun yi aiki cikin tsari da kwarewa.

Rundunar sojin Amurka a Afirka, Africom, ta tabbatar da cewa an gudanar da harin ne tare da hadin gwiwar Najeriya a Jihar Sokoto.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng