An Fallasa Yadda Trump ke Tura Makaman Amurka Kusa da Iran a Shirin Yaki

An Fallasa Yadda Trump ke Tura Makaman Amurka Kusa da Iran a Shirin Yaki

  • An gano yadda Shugaban Amurka Donald Trump ke tura manyan jiragen ruwan yaki zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, a daidai lokacin da yake takun saka da Iran
  • Jiragen ruwan yaki da na makamai masu linzami na Amurka na kan hanyarsu zuwa yankin, lamarin da ke kara nuna za a iya shan kallo a kwanaki masu zuwa
  • Trump ya gargadi Iran kan kisan masu zanga-zanga da kuma yiwuwar sake farfado da shirin nukiliyarta, yana mai cewa Amurka a shirye take ta dauki mataki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Shugaba Donald Trump da kansa ya bayyana cewa kasar Amurka na tura abin da ya kira da “armada” wato manyan jiragen ruwan yaki zuwa kusa da Iran, duk da cewa ya ce yana fatan ba za a kai ga amfani da karfin sojan ba.

Kara karanta wannan

Trump ya tsorata da barazanar kashe shi, ya yi alwashin shafe Iran a duniya

Trump ya yi wannan bayani ne yayin da yake magana da manema labarai a cikin jirgin soji, bayan halartar wani taro da shugabannin kasashen duniya a Davos na kasar Switzerland.

Donald Trump da jirgin yakin Amurka
Jirgin sojan Amurka da Shugaba Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Rahoton Reuters ya ce bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Amurka da Iran ke kara tabarbarewa, musamman biyo bayan murkushe zanga-zanga da aka ce an yi a Iran da kuma takaddama kan shirin nukiliyarta.

An fallasa shirin Donald Trump kan Iran

A cewar wasu jami’an gwamnatin Amurka da suka nemi a sakaya sunansu, jirgin ruwan yaki na USS Abraham Lincoln tare da wasu jiragen ruwan yaki masu dauke da makamai masu linzami na kan hanyarsu zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.

Jami’an sun ce ana kuma duba yiwuwar tura karin na’urorin kare sararin samaniya, domin kare sansanonin sojan Amurka da ke yankin daga yiwuwar kai hari daga Iran.

Sun bayyana cewa wadannan shirye-shirye na fadada zabin da Shugaba Trump ke da shi, ko dai wajen kare dakarun Amurka da ke yankin ko kuma daukar karin matakan soja idan bukatar hakan ta taso.

Trump ya kara yin gargadi ga kasar Iran

Kara karanta wannan

Trump ya fallasa abin da shugaban Faransa ya fada masa kan Iran da Syria

Shugaba Trump ya ce Amurka na sanya ido sosai kan Iran, yana mai jaddada cewa yana fatan ba za a samu wani sabon rikici ba, amma Amurka a shirye take idan aka tilasta mata daukar mataki.

Al-Jazeera ta rahoto cewa ya sake gargadin Iran kan kisan masu zanga-zanga da ake zargin an yi a cikin kasar, yana mai cewa ya taba barazanar daukar matakin soja idan aka ci gaba da rataye fursunoni.

Shugaba Donald Trump da Ayatollah Khamenei
Ayatollah Ali Khamenei da Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya yi ikirarin cewa Iran ta janye shirin rataye kusan mutane 840 ne bayan barazanar da ya yi, yana mai bayyana hakan a matsayin alama mai kyau.

Shugaba Trump ya sake jaddada matsayinsa na cewa Amurka ba za ta amince Iran ta farfado da shirin nukiliyarta ba bayan hare-haren da aka kai a watan Yunin 2025.

Trump ya gargadi Iran kan kashe shi

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya amsa tambaya game da abin da zai faru ga Iran idan ta kashe shi.

A amsar da ya bayar, Trump ya ce idan Iran ta kuskura ta kai masa hari to ta kashe shi, Amurka za ta shafe Tehran a doron duniya.

Shugaba Trump ya yi gargadin ne bayan hukumomin Iran sun tabbatar masa da cewa za su yi martani mai zafi idan ya kai musu hari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng