Trump Ya Tsorata da Barazanar Kashe Shi, Ya Yi Alwashin Shafe Iran a Duniya
- Shugaban Amurka Donald Trump ya sake barazanar cewa kasar Iran za ta shuɗe daga doron ƙasa idan aka yi yunƙurin kai masa hari
- Iran ta mayar da martani da cewa za ta yi amfani da dukkan ƙarfin sojojinta domin ramako idan wata kasa a duniya ta sake kai mata hari
- Rahotanni sun nuna cewa maganganun bangarorin biyu sun ƙara tayar da hankulan jama'a kan yiwuwar faɗaɗa yaƙi a Gabas ta Tsakiya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Sabuwar barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi ga Iran ta sake tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin ƙasashen biyu, lamarin da ke nuna cewa rikicin da ke tsakaninsu bai nuna alamun ya gama lafawa ba.
Maganganun Trump sun zo ne a daidai lokacin da manyan jami’an Iran ke bayyana cewa ƙasar ba za ta zauna shiru ba idan aka sake kai mata hari, musamman bayan yaƙin kwanaki 12 da Isra’ila ta ƙaddamar a kanta a 2025.

Source: Getty Images
Al-Jazeeera ta wallafa cewa masu sharhi kan harkokin siyasa da tsaro na ganin irin wannan musayar kalamai na iya ƙara tsananta rikicin yankin, tare da barazana ga zaman lafiya a duniya baki ɗaya.
Gargadin da Iran ta yi wa kasar Amurka
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa Tehran zai mayar da martani da dukkan ƙarfin da yake da shi idan aka sake kai masa hari daga Amurka ko ƙawayenta.
Rahotanni sun bayyana cewa Abbas Araghchi ya ce sojojin Iran a shirye suke su kare ƙasar ba tare da ja da baya ba a ko da yaushe.
Araghchi ya ce maganar da ya ke ba barazana ba ce, sun bayyana gaskiyar da ya dace duniya ta sani ne kawai a halin da ake ciki.
Ya bayyana kansa a matsayin jami’in diflomasiyya da tsohon soja da bai son yaƙi, amma ya jaddada cewa wajibi ne ya kare ƙasarsa idan aka tilasta masa.

Source: AFP
Ya kuma gargaɗi cewa duk wani rikici da aka tayar zai kasance mai tsanani ƙwarai, tare da ɗaukar lokaci mai tsawo fiye da yadda wasu ke zato.
Gargadin Trump game da kashe shi
Kalaman Araghchi sun zo ne kwana guda bayan Trump ya sake jaddada barazanar da ya taɓa yi a baya, inda ya ce Iran za ta shuɗe gaba ɗaya idan ta yi nasarar kashe shi.
Shugaban Amurkan ya ce ya bayar da umarni a bayyane, kuma duk wani yunƙurin kai hari a kansa zai haifar da mummunan sakamako ga Iran.
Rahoton News Nation ya ce Trump ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya ce idan wani abu ya same shi, za a kawar da Iran daga doron ƙasa.
Trump ya tona asirin Shugaban Faransa
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fitar da wani sako na musamman da shugaban Faransa ya tura masa.
Donald Trump ya bayyana cewa Emmanuel Macron ya tura masa sakon ne a kan kudirin kasar Amurka na mallakar tsibirin Greenland.
A sakon Macron, an ga maganganu da ya yi a kan kasashen Iran da Syria tare da bukatar taro na musamman da Trump a Paris.
Asali: Legit.ng


