An Tura Limami Gidan Kaso bayan Daurawa Masoya Masu Shekaru 16 Aure a Masallaci
- Kotun Crown da ke Northampton ta yanke wa wani limami hukuncin zama a gidan yari, bayan ya aurar da ’yan shekara 16
- Limamin, Ashraf Osmani, ya ce bai san an sauya dokar aure a Ingila ba kafin ya jagoranci daurin auren a cikin masallaci
- Alkalin kotu ya ce babu tilas a auren amma ya soki limamin bisa sakaci, yana mai cewa ya kamata ya san dokar ta sauya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Northampton, England - Wata kotu a kasar Ingila ta yanke wa wani limami hukuncin zaman gidan yari na makonni 15.
Hakan ya biyo bayan samun shi da laifin aurar da yara ’yan shekara 16 a masallaci ba tare da bin ka’ida ba.

Source: Getty Images
Rahoton BBC ya ce Kotun Crown da ke Northampton ta bayyana cewa limamin, Ashraf Osmani mai shekara 52, ya gudanar aure ga matasa biyu a Masallacin Northampton a watan Nuwamban 2023.
Limami ya kare kansa bisa rashin sani
A gaban kotu, Osmani ya bayyana cewa bai san dokar kasar ta sauya ba, wadda ta daga mafi karancin shekarun aure a kasar Ingila zuwa shekara 18, watanni tara kafin faruwar lamarin.
Limamin ya amsa laifinsa a wani zaman kotu da ya gabata, inda aka tuhume shi da laifuka biyu na haddasa auren yara, lamarin da ya sabawa doka.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Choudhury, ya ce bincike ya nuna babu wani tilastawa game da aure, kuma matasan sun je wurin limamin ne da kansu ba tare da matsin lamba ba.
Duk da haka, alkalin ya yanke masa hukuncin zaman gidan yari na makonni 15, amma aka dakatar da hukuncin na tsawon shekara guda.
Kotun ta ji cewa matasan sun nemi Osmani ne bayan wani masallaci ya ki aurar da su, inda daga bisani ya amince ya daura musu aure.

Source: Getty Images
Ka'idar da limamin ya bi kafin auren
Rahoton kotu ya ce limamin ya karbi kudin fam 50 domin bayar da takardar shaidar aure, sannan bayan bikin, matasan sun yi shagali tare da abokansu, cewar Telegraph.
Lauyan kare Osmani, James Gray, ya bayyana cewa wannan kuskure daya ne tilo da limamin ya taba yi a cikin shekaru 20 da yake gudanar da nikah.
Ya ce Osmani ya nemi fasfo domin duba ranar haihuwa, ya cike takardun neman aure, kuma ya rubuta bayanan a rajistar masallaci yadda ya dace.
Lauyan ya jaddada cewa duk wadannan matakai na nuna cewa limamin ya aikata kuskuren ne sakamakon rashin sanin sauyin doka, ba da gangan ba.
Sai dai alkalin kotu ya fada masa cewa sakacinsa ne ya jawo matsalar, inda ya ce ya kamata ya san cewa dokar aure ta sauya.
Bayan kammala shari’ar, Ashraf Osmani ya fice daga kotu ba tare da yin wani bayani ba, yana rufe fuskarsa da hannaye da kyalle.
Limami ya rasu yana sallar dare a masallaci
An ji cewa wani Bawan Allah mai suna Sani Lawal ya yi sallama da Duniya a lokacin da yake yin sallar dare domin neman yardar Ubangiji.
Malam Sani Lawal ya rasu ne yayin da yake limancin sallar daren a wani masallaci da ke garin Zaria a jihar Kaduna.
Musulmai su na ta yi wa wannan Alaranman kyakkyawan zato bayan ganin irin karshen da ya yi wanda a Musulunci ake kyautata masa zato.
Asali: Legit.ng

