Koyarwar addinin Musulunci: Labarin wani Limami a garin Jos da ya boye Kiristoci a cikin Masallaci
Wani Limamin Masallaci a jihar Filato ya dabbaka koyarwar addnin Musulunci a yayin rikici tsakanin makiyaya da manoma da ya barke a jihar Filato a satin daya gabata, inda aka yi asarar sama da rayuka dari biyu, kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.
Gidan jaridar BBC Hausa ne ta ruwaito wannan labari, inda ta tattauna wa wani Limamin Masallaci mai tarin shekaru dake zama a kauyen Nghar Yelwa, wanda yace a ranar Lahadin da ta gabata, ranar da rikicin ya kara ruruwa, sai ga wasu ayarin Kiristoci sun shigo kauyensu suna neman mafaka.
KU KARANTA: Laftanar Janar Buratai ya kaddamar da madatsar ruwa da Sojoji suka gina a Yobe
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Limamin ya cigaba da cewa shigoawarsu ke da wuya bai tsaya wata wata ba, nan da nan ya tarbesu, inda ya shigar da matan dake cikinsu cikin gidansa, yayin da ya bude ma Mazan Masallacin da yake limanci, ya boyesu.
Limain yace mutanen sun fito ne daga wani kauye dake makwabtaka da karamar hukumar Barikin Ladi, kuma wasu makiyaya ne suka biyo su da nufin hallakasu, inda yace jim kadan da boyesu, sai ga maharan nan sun biyo su zuwa kauyen, inda suka fara tambyara ina Kiristocin suka shiga.
Nan fa Dattijon nan ya yi ta zama yace masa dukkanin mutanen dake cikin Masallacin nan Musulmai ne masu neman mafaka, wanda yace yawansu ya kai mutum dari biyu da sittin da biyu, bayan wani dan lokaci yan bindigan suka yarda suka yi tafiyarsu.
Limamin ya bayyana cewa: “Na fara shigar da Matan cikin gidana, yayin da na bude ma Mazajen Masallacinmu don ceton rayuwarsu” Inji shi, a haka ne kiristocin, wadanda yan kabilar Berom ne suka tsallake rijiya da baya, inda a yanzu haka suna zaune a Masallacin sakamakon sun yi asarar muhallansu.
Sai dai wani abu mai daure kai game da wannan labari shi ne, a shekarun baya da suka gabata, Musulman garin nan na neman filin da zasu gina Masallaci, suka rasa, inda daga karshe yan kabilar Berom suka basu fili kyauta, wanda anan ne suka gina wannan Masallaci.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng