Amurka Ta Yi Barazana, Za a Lafta Haraji a kan Kasashen da ke Mu'amala da Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar kakaba harajin kashi 25 a cikin 100 a kan duk ƙasashen da ke hulɗar kasuwanci da Iran
- Barazanar haraji ta zo ne a daidai lokacin da Iran ke fuskantar gagarumar zanga-zanga ta adawa da gwamnati, kuma ta zargi Amurka da Isra'ila da hannu a matsalar
- Tuni kasar China, abokiyar hulda da Iran ta bayyana cewa ba za ta amince da karfa-karfa fa, kuma akwai yiwuwar ta dauki matakin ramuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States of America – Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargaɗi cewa duk ƙasar da ke yin kasuwanci da Iran za ta fuskanci harajin 25%.
Trump ya bayyana cewa wannan haraji zai fara aiki ne nan take da bare da bata lokaci ba, kuma lamarin ya shafi dukkanin kasashen da ke mu'amala da Iran.

Source: Getty Images
Bloomberg ta wallafa cewa Trump ya nanata cewa duk kasar da ke kasuwanci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta biya harajin 25% kan duk wata kasuwanci da take yi da Amurka.
Amurka ta dora haraji kan kawayen kasar Iran
Arise News ta ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya kara da cewa babu gudu ko ja da baya a wannan umarni, sai dai bai yi karin bayani ba.
Rahoton ya ce yawanci kamfanonin Amurka masu shigo da kaya daga ƙasashen waje ne ke biyan irin wannan haraji, amma ba kasashen kai tsaye ba.
Iran, wadda ke cikin ƙungiyar ƙasashen OPEC masu samar da man fetur, ta dade tana fuskantar tsauraran takunkumin Amurka, kuma tana fitar da mafi yawan man feturinta zuwa China.

Source: Twitter
Sauran manyan abokan kasuwancin kasar Iran sun haɗa da Turkiyya, Iraki, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Indiya.
Duk da sanarwar Trump, babu wata takardar hukuma da aka wallafa a shafin White House da ke fayyace tsarin harajin, ko kuma ko harajin zai shafi dukkan ƙasashen da ke hulɗa da Iran.
Martanin China ga barazanar Amurka
China ta bayyana takaicinta matuka, inda ofishin jakadancinta a Washington ya soki matakin Trump tare da gargaɗin ɗaukar matakan kare muradunta.
Ofishin jakandancin ya ce China za ta ɗauki duk matakan da suka dace kuma ta yi Allah wadai da takunkumin kai-tsaye ba bisa ƙa’ida ba da kuma amfani da danniya.
Barazanar harajin na zuwa ne a lokacin da Iran ke fuskantar mafi girman zanga-zangar adawa da gwamnati cikin shekaru, bayan yaƙin kwanaki 12 da aka yi da Isra’ila a bara.
Trump ya ce Amurka na iya ganawa da jami’an Iran, kuma yana hulɗa da ‘yan adawar kasar, yayin da yake ƙara matsin lamba kan shugabancin Tehran tare da yin barazanar ɗaukar matakin soja.
Iran ta rataye dan leken asirin Amurka
A baya, mun wallafa cewa kasar Iran ta tabbatar da aiwatar da hukuncin kisa kan wani mutum da aka bayyana sunan mutumin a matsayin Ali Ardestani bisa zargin yi wa Isra'ila leken asiri.
An zargi Ali Ardestani da laifin tattara muhimman bayanai na kasa sannan ya mika su ga hukumar leƙen asirin Isra’ila, wato Mossad, lamarin da Iran ke hukuntawa da hukuncin kisa.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Iran ke ci gaba da fafatawa da Isra’ila a boye, musamman a harkokin leƙen asiri da ayyukan sirri a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

