Khamenei Ya Harzuka kan Trump, Ya Hango Makomar Shugaban Amurka
- Jagoran juyin juya hali na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya aika da sakon gargadi ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump
- Ali Khamenei ya soki Trump kan yadda yake mulki da zalunci da nuna girman kai ga sauran kasashen duniya
- Ayatollah Sayyid Ali Khamenei mai shekaru 86 ya tunatar da Trump abin da ya faru da shugabanni masu irin halinsa a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Jagoran juyin juya halin Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya soki shugaban kasar Amurka, Donald Trump.
Ali Khamenei ya zargi Trump da shugabanci na zalunci, tare da yi masa gargaɗin cewa, kamar yadda ya faru da masu mulkin kama-karya a baya, shi ma zai iya faɗuwa.

Source: Getty Images
Jagoran juyin juya halin ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Juma'a, 9 ga watan Janairun 2026.
Ayatollah Ali Khamenei ya ragargaji Donald Trump
Khamenei ya ambaci sarakuna da shugabanni na tarihi kamar Fir’auna, Nimrod, da tsohon shugaban Iran, Mohammad Reza Pahlavi, yana cewa duk sun faɗi ne a lokacin da girman kai da izza suka yi musu yawa.
Ali Khamenei ya la’anci abin da ya bayyana a matsayin dabi’ar Shugaban Amurka na kallon duniya da girman kai da raini.
Ya yi kwatance kan shugabancin zamani da na shugabannin tarihi da aka sani da zalunci.
“Shugaban Amurka da ke yin hukunci a kan duk duniya da girman kai ya sani cewa azzalumai da masu mulki da izza da girman kai kamar Fir’auna, Nimrod, Mohammad Reza [Pahlavi] da irinsu sun faɗi ne a lokacin da suke kan kololuwar girman kansu. Shi ma zai faɗi."
- Sayyid Ali Khamenei
Ana zaman doya da manja tsakanin Amurka da Iran
Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da tsananta, wanda ya haɗa da rashin jituwa ta diflomasiyya, takunkumi, da musayar kalamai masu zafi tsakanin manyan jami’an kasashen biyu.
Khamenei, wanda shi ne babban jagora na siyasa da addini a Iran, ya saba yin suka ga manufofin ketare na Amurka da shugabancinta, inda yakan yi amfani da misalan tarihi da akidu wajen bayyana ra’ayinsa.
Trump ya ji dadin harin Israila kan Iran
A watan Yuni 2025, an ruwaito cewa Trump ya yaba da wani harin soja da Isra’ila ta kai wa Iran, inda ya bayyana harin a matsayin “abin burgewa ƙwarai”, tare da yin gargaɗin cewa akwai yiwuwar karin matakai nan gaba.
Jaridar The Punch ta ce wannan bayani ya fito ne daga Jonathan Karl, babban wakilin ABC News a Washington, yayin wata hira da Trump.

Source: Getty Images
A cewar Karl, Trump ya ce:
“Ina ganin abin ya yi kyau kwarai… sun sha mummunan hari, kwarai da gaske… kuma akwai ƙarin abubuwa masu zuwa da yawa.”
Kalaman Trump sun zo ne a lokacin da rikici a Gabas ta Tsakiya ke kara tsananta, sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin Iran da Isra’ila.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta la’anci abin da ta kira “bayyanannen aikin ta’addanci” daga Isra’ila, bayan hare-haren sojoji da aka kai a kan yankunan Iran, ciki har da birnin Tehran.
Khamenei ya kafawa Trump sharudda
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ayatollah Ali Khamenei ya kafawa Donald Trump sharudda kan tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.
Jagoran juyin juya halin ya fitar da wasu sharuda da ya ce idan Amurka ta cika su za a daina zaman doya da manja tsakanin Tehran da Washington.
Khamenei ya bayyana cewa kalaman da wasu jami’an Amurka ke yi na son yin haɗin gwiwa da Iran ba su da ma’ana muddin suna ci gaba da goyon bayan mummunan tsarin Yahudawa.
Asali: Legit.ng


