Iran Ta Kara Rataye Mutumin da Ta Kama da Yi wa Isra'ila Leken Asiri

Iran Ta Kara Rataye Mutumin da Ta Kama da Yi wa Isra'ila Leken Asiri

  • Kasar Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa kan wani da ake zargi da leƙen asiri ga Isra’ila, inda ya ke kai mata muhimman bayanai a kanta
  • Hukumar shari’a ta Iran ta bayyana cewa kotun koli ta amince da hukuncin bayan an bi dukkanin tanade-tanaden da dokar kasa ta yi
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an karuwar aiwatar da hukuncin kisa kan masu alaƙa da leƙen asirin Isra’ila da ke kwasar bayanai daga Iran a bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran – Kasar Iran ta tabbatar da cewa ta aiwatar da hukuncin kisa kan wani mutum da aka zarge shi da yi wa Isra'ila leƙen asiri.

Kafofin yada labarai na bangaren shari’a a kasar, Mizan, sun bayyana hakan a ranar Laraba, inda suka bayyana sunan mutumin da Ali Ardestani.

Kara karanta wannan

Kotu ta ba Abubakar Malami, matarsa da dansa beli, za su biya N1.5bn

Iran ta dauki mataki a kan dan leken asirin Isra'ila
Ayatoulla Khameni, jagoran kasar Iran Hoto: Getty
Source: Twitter

BBC ta wallafa cewa a cewar rahoton, Iran ta zage shi da laifin tattara wa da mika bayanai masu muhimmanci na kasa ga hukumar leƙen asirin Isra’ila, wato Mossad.

Yadda Iran ke hukunta masu leken asiri

Reuters ta wallafa cewa kasashen Iran da Isra’ila sun shafe shekaru masu yawa suna fafatawa a boye, inda kowanne ke zargin dayan da shirya hare-haren sirri da ayyukan leƙen asiri a yankin Gabas ta Tsakiya.

A wannan lokaci, Iran ta sha aiwatar da hukunci kan mutanen da ta ce suna da alaka da ayyukan sirri na Isra’ila, musamman wadanda aka zarga da taimakawa ayyukan leƙen asiri a cikin kasar.

Mizan ta ce hukuncin kisa da aka yanke wa Ali Ardestani ya biyo bayan cikakken shari’a ne, inda aka bi dukkannin ka’idojin doka da ake bukata.

Iran ta rataye dan leken asirin Isra'ila
Firayim Ministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Facebook

Rahoton ya nuna cewa kotun koli ta Iran ta tantance shari’ar tare da amincewa da hukuncin kafin a aiwatar da shi.

Kara karanta wannan

Kano: Wasu yara sun fadi dalilin murna da rasuwar mahaifinsu bayan shekaru 20

A cikin bayanin da kafar ta wallafa, ta ce:

“An aiwatar da hukuncin kisa kan Ali Ardestani saboda laifin leƙen asiri a madadin Mossad, bayan tabbatar da cewa ya mika muhimman bayanai na kasa."
"An kammala hukuncin ne bayan amincewar kotun koli da kuma bin hanyoyin shari’a yadda doka ta tanada.”

Hukumar shari’a ta Iran ta ce tana daukar matakan tsaro da tsanani kan duk wanda aka samu da hannu a ayyukan da ke barazana ga tsaron kasa.

Ta ce irin wadannan hukunci na nufin dakile duk wani yunkuri da ka iya cutar da muradun Iran da kuma jawo wa kasar tashin hankali.

Yadda ake rikicin Iran da Isra’ila

Masu lura da al’amuran yankin sun ce karuwar hukuncin kisa kan mutanen da aka zarga da leƙen asiri ga Isra’ila na da alaka da tsanantar rikici tsakanin kasashen biyu.

A bana, rahotanni sun nuna cewa adadin irin wadannan hukunci ya karu sosai bayan wata arangama kai tsaye da ta faru a watan Yuni.

Kara karanta wannan

Kotu ta tabbatar da hukuncin kisa kan Farida, matar da ta kashe tsohon mijinta

A lokacin arangamar, sojojin Isra’ila tare da hadin gwiwar Amurka sun kai hare-hare kan wasu cibiyoyin nukiliya na Iran, lamarin da ya kara tsananta rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu.

Wannan ya sa Iran ta kara tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido kan ayyukan sirri a cikin kasar, inda aka kuma samu karin hukuncin kisa.

Iran ta daura damarar yaki

A wani labarin, mun wallafa cewa jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa ta kera sabon nau’in makamai masu linzami da suka fi ƙarfin waɗanda ta yi amfani da su a cikin rikicin da ta yi da ƙasar Isra’ila.

Ministan tsaron Iran, Aziz Nassirzadeh, ya fito da wannan jawabi a ranar Laraba, 20 ga watan Agusta, 2025, inda ya ce sabbin makaman nan suna da ƙarfi sosai, kuma a shirya suke su gwabza idan wani yakin ya taso.

A cikin jawabin, Nassirzadeh ya ce Iran ta ɗauki matakan kera makamai ne don kare martabar ta da muradun tsaro, kuma ba ta son yaƙi da kowa sai dai idan ƙalubale ya zo daga waje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng